Connect with us

Allah Daya Gari Bambam

Al’adun Kabilar Zulu Da Suka Sha Bamban Da Na Saura

Published

on

A makon da ya gabata, mun fara kawo muku tarihi da yanayin rayuwar al’ummar Zulu. A bayananmu, mun ba da karfi sosai kan abubuwan da suka shafi dabi’unsu na gargajiya ciki har da tarihin asalinsu da yadda suke iya gane mutumin da yake dauke da bakin ruhi da kuma wanda yake dauke da farin ruhi.A yau za mu ci gaba da bayani kan sauran harkokin rayuwarsu tun daga kan tsarin gidajensu har zuwa bukukuwan aure da kan kunshi shagulgula iri-iri ta bangaren ango da amarya. Har ila yau, a yau din za ku ji wasu al’adu na musamman da mutanen Zulu ke da su da suka sha bamban da na sauran al’umma.

Tsarin gidajensu

Bukkokin gargajiya na tarihi ana kiran sa Ikukwane. Magidanta maza ke neman karare su jera yadda zai zagayen bukka, mata kuma sukan hada tare da yin saman ginin da Dogaye hade da guntayen ciyawa suna amfani da katuwar reshen bishiya wadda ake sawa a tsakiya dan ya zama ma tashi ga ginin, kofar bukkan ana yinsa guntu saboda ko waye ya zo sai ya tsaya ya rankwafa kafun ya shiga.

Akan yamutsa kashin shanu da tabon gidan gara a yi lakan da ake shimfida shi a tsakiyar bukkan. Wannan hadi kan zama abu mai tauri kamar dutse sai a zo a bisa da dutsen guga don ya yi ta kyalli. Da wannan hadi kuma ake yin dan tudu kusa da matashin bukkan.  Abin mamaki, wannan bukka tasu tana da sanyi a lokacin zafi, sannan tana da zafi a lokacin sanyi.

Suna amfani da hannayen su da kuma tafin kafan su wurin ginin gidajen su, a cikin kabilar Zulu hakkin miji ne gina gidan sa amma mata za ta iya tayawa, duk da haka kasancewar hakkin mazan ne ginin gidaje mata kan karbi ayyukan da zarar mazajen sun yi nisan kiwo.

Kofofin gidajen dole su kalli wuri daya kamar yadda na fada daga farko sukan yi amfani da kashin shanu da kuma kasar shuri  wurin yin tsakar dakunan. Kofa daya ake yi na shiga da fita, sa’annan kofar dole ta kasance guntuwa ta yadda dole mai shiga ko fita sai ya tsuguna kafun ya wuce, gidajen kan yi kimanin shekaru goma zuwa sha biyar kafun a sake sabon gini, sukan fara ginin wani a gefen nasu kafun lokacin da wadda suke ciki zai fadi ko su rusa da kansu.

Saman suna yinsa da ciyawar da aka dinke da igiyar katako da kuma wadda aka yi da ciyawa kafun a gama saman gidan yakan kai sati ko kuma watanni har biyu, ya danganta ga yanayin ma ginin dan kuwa tun daga sama ake dinkin har kasan ciyawar domin a samu saman bukka mai inganci wadda zai tsaya komai ruwa komai iska.

Suna da gidaje kala kala. Akwai masu zagaye wato ‘roundabel houses’ da ake yin su da bulo na laka, suna amfani da wannan a matsayin dakin bacci.

‘Skuare houses’, su kuma gidaje ne masu kusurwa hudu, wadda ake amfani da su a matsayin dakin baki, sai kuma bukkokin da ake yi da ciyawa tun daga saman ginin har kasan sa, tun daga bango har rufi su suke kira gidan kakanni inda kakanni ke zama, sannan suna yin girki ne a wajen gidajen da tsakar gidan.

Tutoci.

Farar tuta na nufin ana sanannen baiko. Tuta mai ja da fari kuwa na nufin ango sai ya yi ta wahala da hawaye da kadaici kafin ya samu soyayyar matarsa wato farin jinin kenan.

Shanu

Mutumin Zulu na kaunar shanun sa a kan komai kai hatta ga iyalin sa suna bayan garken sa. Zai dauki kimanin sa’anni marasa iyaka yana kallon garken nan nasa domin ya san ko wani shanu a cikinsa, shanu na nufin kima da kuma matsayi tare da dukiya da iko a wurinsu, domin saniya daya na da ikon saya wa mutum mata ko nawa ne. Da zarar sarki ya mutu akan bizine shi ne a cikin garken shanun sa wato kraals.

Auratayya

zulu traditional weddding dresses ideas wedding decor theme Elegant zulu wedding dresses

Aurensu na gargajiya na da bukatu daga wurin gidan maza da mata gaba daya, inda ango ke bayar da kyauta da suke kira lobola zuwa ga gidan amarya, yawanci maza kan bada shanu  ne a matsayin kyautar duk da cewa ya danganta da yanayin wadatar mijin yanayin arzikin sa yanayin yawan kyautar sa.  Da zarar dangin amarya sun karbi wannan lobola to aure ya dauru a al’adar Zulu, sai mata ta bar gidan su zuwa gidan mijin ta ta ci gaba da zama a matsayin mata shi kuma mijin. A auratayyarsu mata kan koma cikin dangin mijin ta da zarar sun yi aure, ma’ana danginsa sun karu. Kyautar lobola kaman sadaki ne ake badawa ga dangin mata.

Al’adu

Mutanen Zulu na da al’adar su ta musamman da ta banbanta su da ko wace al’umma.  A ko wacce shekara sukan yi bukukuwa na farfado da al’adun su na gargajiya wadannan bukukuwa sun hada da ranar gado (heritage day), wadda ake yi dan murnar rayuwar shaka Zulu, sarki mai izza da kuma wadda ya kirkiri kasar Zulu. Abun da ya kara banbanta su da saura shi ne yanayin shigar matan su wadda yawanci ya kunshi saka abubuwan sakin wuri, su kuma mazan kan yi shiga yawanci da fatar saniya wadda ake amfani da ita wajen rufe gaba da bayan jiki kuma kaf maza da matan kan tafi ne ba takalmi in suka yi shigar.

Matayen Zulu ba sa taba gama ayyuka, kamar sauran matan kabilu suma sukan yi dan ayyuka amma abin lura shi ne ayyukan da matan Zulu na birni ke yi ya banbanta da na kauye, dan kuwa na birni yafi sauki a kan na kauyen kwaZulu-natal, saboda a birane gidaje suna samun wadataccen ruwa da kuma wutar lantarki, a kauyuka mata kan  samo itace, sai debo ruwa, girki, wanki, kula da tsofi da kuma yara.

Matan kauye basu da abubuwan girki irin su risho, butar lantarki(electric kettle),plas din ruwan zafi(bacumn flask),bacumn cleaner(abun shara), da dai sauran ababen girki sai sun niki hanya sun tafi jeji sunyi itace dan girki da sauran su, wannan kadai kan saka mata yin nisa da gidajen su tun daga safiya har yamma. Mata kan tafi ne cikin ayari saboda debewa juna kewa da kuma kariya daga muggan namun daji.

Mata kanyi dogon tafiya dan samo ruwa, sukan dauki bokaten karfe,ko tukunyan kasa ko kuma plastic yawanci sun kware a daukan ruwa a digirgire tun suna yara. Akwai kauyuka masu famfo, amma yawanci suna amfani ne da koramu masu gudana inda akan samu kwadi da sauran halittun ruwa na yawo. Suna amfani da ruwan nan ta hanyoyi mai yawa kaman sha, wanki, wanke wanke, wanka, da kuma bayin shuka.  Saboda yaduwar chutuka irin su cholera da bilharzia(cutar fitsarin jini),an koyar dasu tafasa ruwan kafun asha ko kuma su saka bleach.

    Girki

A al’adar Zulu girki aikin mata ne wasu mazan sun gwammace su zauna da yunwa da su taba tukunya da sunan girki, wannan ya samo asali ne daga koyarwar da suke samu tun suna kanana na cewa  iyayen su mata da yan uwansu mata  ne kadai suke girki. Wasu mazan da ke girki an dauke su sakarkaru matsorata. Matan karkara na amfani da tukwanen dalma da wutan murhu wajen yin girki wadda akanyi a cikin gida duk da wasu matan kanyi a waje dan gudun hayaki a cikin gidan, mutanen Zulu basa cin abinci a kwano kaman kowa duk da cewa sukanci a zamanin da, ya danganta ga yanayin abincin,wasu kuma sun gwammace suci da hannu akan su saka cokali. A birane sukan yi amfani da teburin cin abinci amma a karkara a taburma ake bajewa a ci abinci.

Tsaftace gida

Shi ma wani aiki ne na mata kadai matan kauye na amfani da hanyoyi kala kala wajen tsaftace gidajen su kaman amfani da kashin shanu wurin goge tsakar daki, amma a birane ana amfani ne da inji na zamani wajen tsaftar gida. In aka zo wanki matan karkara na tafiya rafi su yi wanki a can dan rage wa kansu debo ruwa zuwa gida tukunna su wanke.  Reno da kuma kula da tsofi a wurin matan Zulu aiki ne da ya zama wajibi, matar da bata da yaro ana daukan ta a kaskance har a wani lokutan ma ba’a daukan ta mace.  Idan mace bata haihuwa ‘yan’uwan mijin da ma matar kanta kan saka mijin ya karo wata wadda zata haifa masa yara, wani lokaci kuma in basu samu haihuwan da namiji ba, mijin nan ma kan karo wata matar ko za a dace.  Domin sun yi imani da cewa da zarar mutum ya mutu bashi da magaji namiji to fa zuri’arsa ta kare saboda matan za su yi aure su bar gida. Saboda in kana da yara mata gaba daya to da zarar ka mutu shikenan tarihin ka ya shude. Goyon yaro a baya shi ne ya raba matan Afrika da sauran matan duniya wani abun burgewa kuwa, a goye da yaro sukan dauki ice ko ruwa a lokaci daya.  A al’adar Zulu iyayen miji da kakannin sa na samun kula ne daga matan ‘ya’yansu da jikoki. Bakon al’amari ne a wurinsu daukan tsoffi a kai gidan kula da su, faruwar hakan abu ne mai wuya a wurin koda kuwa hakan ya faru; a karshe sukan je su dauko su zuwa gida.

Shagalin biki

A biki, amarya kan canza kaya sama da sau uku a ranar auren ta, domin nuna wa  surukan ta irin kyau din da take dashi a cikin kaloli iri iri.  Duk da cewa ba al’adar su ba ne saka farin rigar aure, amma a zamanin nan sun koma sakawa ana auren a coci kuma matan suna saka farar dogon riga. Bayan coci ana bikin a gidan miji inda matan kan canja zuwa shigar kayan al’ada. A lokacin bikin gargajiyar akan samu dangin amarya da ango su yi gasar rawa da kuma waka. A wannan shagalin dangin ango kan yanka saniya dan nuna yardar zuwan amaryar cikin gidan su, amaryar kuwa a gaban kowa za ta saka kudi a cikin saniyar inda  wannan shi ne yake nuna cewa yanzu ta zama ‘yar gidan. A karshe akan rufe ne a inda amarya kan bada kyautar bargo ga dangin mijin a matsayinta ta sabuwar shigowa gidansu. Wannan al’ada ana kiran ta da ukwaba, hatta wadanda suka mutu ana bada kyautar har da su inda rayayyu ke wakiltan su a gaban kowa  za su rufa bargon.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: