Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Soke Zaben dan Majalisar APC Mai Wakiltar Sumaila Da Takai

Published

on

A jiya Juma’a Kotun zabe ta soke zaben Shamsuddeen Dambazau, dan tsohon ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau, mai wakiltar Sumaila daTakai a inuwar jam’iyyar APC.
Kotun ta Umarci Hukumar zabe ta ba Surajo Kanawa, dan takarar jam’iyyar PDP, shaidar lashe zaben.
Dambazau, wanda ya zo na biyu a zaben fid da gwani lokacin da wata babbar kotu ta soke damar tsayawar tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara, Kawu Sumaila.
Dambazau ya kai karar INEC da APC da Kawu Sumaila wanda yake kalubalantarsu kan takardar zaben APC.
Lauyansa, Nuraini Jimoh ya bayyana cewa, Kawu Sumaila ya tsaya takara daga mazabar Kano ta Kudu wanda Kabiru Gaya ya kayar da shi.
Kawu Sumaila ya tsaya takarar sanata daga mazabar Kano ta Arewa karkashin inuwar jam’iyyar APC inda sanata mai ci, Kabiru Gaya ya samu nasara a kansa.
Sai daga baya,jam’iyya APC a matakin jiha ta saka masa da tikitin tsayawa takara a mazabar Sumaila da Takai wadda take cikin mazabar Kano ta Kudu. Saboda haka sai jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zaben majalisar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: