Connect with us

KAUCIN KABA SHA NEMA

Hanyoyin Mallakar Mace

Published

on

Akwai hanyoyi da yawa da magidanci zai iya ribata don samun karbuwa a wurin matarsa. Wadanda kuma ba wasu masu wuya ba ne, domin kusan abubuwa ne da muke yi kullum. Kawai dai salon aiwatar da su din za a inganta. Da yawa daga maza sun san da abubuwan, sai dai ba sa daukar su da muhimmanci, saboda ba su san ayadda suke da matukar tasiri a wurin matan ba. watakila don suna ganin ai kananan abubuwan ba su da wani muhimmanci idan an kwatanta su da manyann abubuwan da suka saba yi yau da kullum.

Sau da yawa, maza su kan fara yin wani abu karami, wanda kuma ya ke matukar burge mata. Amma zuwa wani dan lokaci kuma sai su dena. Su musanya shi da wani abu da suke ganin ai babba ne, kuma mai muhimmanci. A ganinsu, hakan shi ne abu mafi alfano. Sai dai abin da ba su sani ba shi ne, idan har ana so a burge mace, to dole ne a yi mata wasu kananan abubuwa wadanta ita su ne za su sa ta ji lallai an damu da ita, kuma an karfafe ta, sannan ana son ta.

Sabanin maza, mata suna bukatar a yi musu abubuwa da yawa kafin su yarda cewa lallai ana son su. Amma abu daya ko biyu ba za su taba gamsar da su har su yarda ana son su ba. abin yana da wuyar fahimta a wurin namiji. Amma abin da ya kamata ya kaddara shi ne, ita mace tana da wani tankin soyayya tamkar tankin gas da yake jikin mota. Yana bukata a cika shi, ya kare a kara cika shi, lokaci zuwa lokaci. Wato kenan yin abubuwa da dama a lokuta da dama shi ne sirrin da ake bi wurin cika tankin soyayyar mace. Yayin da kuma duk aka cika wannan tankin to mace za ta samu cikakken kuzarin da za ta iya nuna wa mutum yarda da sadarkarwa da soyayya iyakar kokarinta. Kananan abubuwa da dama ake bukata domin cika tankin soyayyar mace.

Wadannan hanyoyi ne har guda 101 wadanda magidanci zai bi don cika tankin soyayyar matarsa.

Hanyoyi 101 da za ka iya mallakar zuciyar matarka:

 1. Yayin da ka dawo gida, kafin aikata kowane abu, ka fuskance ta, ka rungume ta.
 2. Ka yi mata tambayoyi da suka shafe ta. Musamman yadda ta wuni a gida ko kuma yadda ta dawo daga wata unguwa ko asibiti da ta je.
 3. Ka yi kokarin yi mata ‘yan tambayoyi, kuma ka yi juriyar saurarenta.
 4. Kar ka damu da sai ka magance matsalolin da za ta lissafa maka. Nuna mata damuwarka da abin kawai.
 5. Ka ba ta mintuna ashirin kawai. Wanda babu abin da za ka yi a ciki sai sauraren ta. Kar ka karanta jarida ko bude talbijin ko wayarka a cikin wannan mintunan.
 6. Ka rika zuwa mata da kyauta ko ta irin furen nan ce, a wasu lokuta da ba ta zata ba.
 7. Ka kirkiri wata rana da za ku gabatar da wani abu na soyayya na musamman. Ba wai sai ka jira wasu ranaku irin su ranar masoya da ake yi gama-gari ba.
 8. Watarana ka yi kundumbala ka shiga kicin, ka ce “Yau dai na hutar da ke, ki zauna zan yi mana abinci!”
 9. Ka kalle ta sosai, ka yabi kyawun surarta. Musamman ma a lokutan da ta yi kwalliya. Kallon mace a lokacin da ta yi kwalliya ba tare da an yabe ta ba, tamkar a ce mata “Ba ki da kyau ne.”
 10. Yayin da duk ka lura ta bata rai, ka saurare ta, kuma ka girmama abin da ta bayyana a matsayin dalilin bacin ranta. Sau da yawa maza suna kallon abubuwan da suke bata wa mata rai a matsayin wasu ababen da ba su taka kara sun karya ba. Amma tare da haka, nuna an fahimci dalilin bata ransu, kuma an gamsu da suna da damar su bata ran a kan hakan shi ya fi komai muhmmanci a wuinsu.
 11. Ka taya ta aiki lokacin da ka ga alamar ta gaji. Wannan shi yake nuna mata tabbas kana tausayinta.
 12. Ka rika ba ta rarar lokaci, musamman idan za ku yi wani abu tare. Saboda kar ka zo kana azalzalar ta. Misali, idan za ku yi wata tafiya tare. Idan karfe tara ya kamata ku fita daga gida, sai ka ce mata karfe takwas za ku bar gidan. Saboda ta iya shiryawa a nitse bayan takwas din kadan, ko zuwa taran saura kadan. Maimakon ka fada mata taran ta zo ba ta shirya a kan lokaci ba, ka yi ta azalzala har ranku ya baci dukkanku. Ku fita cikin yanayi mara dadi.
 13. Idan za ka yi latti; ba za ka dawo gida a kan lokacin da ka saba dawowa ba, ka kira ta ka sanar da ita. Kar ka bar ta cikin zulumi.
 14. Idan ta tambayi ko ta roke ka wani abu, ka ce “E” ko “A’a” kawai. Ba tare da ka nuna laifinta na tambayar wannan abin ba. Sau da yawa, mata sukan yi mamakin maza, har abin ya daure musu kai. Cewa, idan ta nemi wani abu a wurin miji, bayan ya hana ta, sai kuma ya dauki lokaci yana fada ko korafi game da don me ma za ta yi wannan maganar. Misali ta ce za ta je wata unguwa. Maimakon ya ce “A’a, ba za ki je ba.” sai ya yi ta fada, “Ke shikenan ba ki da aiki sai yawo. Kullum kina kan hanya, ko gajiya ba kya yi.”
 15. Yayin da ka fahimci ranta ya baci sakamakon wani aiki ko wata magana da ka yi, ka daure ka ba ta hakuri, ta hanyar da za ta fahimci ka yarda ranta ya baci. Sannan sai ka yi shiru. Ta fahimci cewa da gaske kake ba ta hakurin. Kar ka damu da yi mata wani karin bayani da zai nuna ba laifinka ba ne.
 16. Yayin da duk ka ji kana bukatar sarari. Wato ka ji kana bukatar shiga kogo, ba ka son yin magana ko a yi maka, sakamakon wani yanayi na damuwa da ka tsinci kanka. To ka sanar da ita, cewa kana bukatar lokaci. Yanzu ba ka bukatar yawan magana ko kasancewa a cikin mutane kamar da. Saboda haka, ta yi maka uzuri zuwa wani dan lokaci kadan, za ka dawo.
 17. Yayin da kuma ka dawo hayyacinka. In ka zo za ka tattauna batun abubuwan da suka same ka, ka yi cikin girmamawa, yadda ba za su cutar ko bata rai ba. Ba kuma tare da ka jingina wani sashe na laifin a kanta ba. Wannan shi zai sa ta yi saurin farfadowa daga yanayin damuwar da ta tsinci kanta a lokacin da ka janye jiki daga gare ta.

Ka dauki gabarar hura wuta domin ku ji dumi, a lokacin sanyi. Ko lullubar ta, tamkar yadda ake lullubar yara, a matsayin ba ta kariya daga sanyin. Maimakon ka tsaya ita ta samar maka da wannan yanayin. Domin yanayi ne da babba ya kamata ya nuna kulawa ga karami a cikinsa. Don haka idan kai ne ka yi, ya fi kayatarwa.

Mu hadu a mako na gaba, domin ci gaba daga na 19.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: