Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Neja: Uba Da ‘Ya’yansa Sun Mutu Sakamakon Kifewar Kwalekwale

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Neja, ta tabbatar da mutuwar mutum uku, a wani hatsarin kwalekwale wanda ya afku a yankin Wuya cikin kogin Jihar Kaduna.

Daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Neja, Alhaji Ahmed Inga, shi ya tabbatar da wannan lamari sa’ilin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na Nijiriya a garin Minna ranar Asabar.

Ya bayyana cewa, wani mutum mai suna Malam Yahaya Hamza tare da ‘ya’yansa guda biyu, kwalekwale ya nutse da su lokacin da su ke dawowa daga gonarsu.

Inga ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta, a cikin kogin Jihar Kaduna a yankin Wuya kusa da hanyar Bida zuwa Mokwa. Ya cigaba da cewa, mutanen da su ka mutu ‘yan asalin karamar hukumar Edati ta Jihar Neja ne.

A cewar Inga, mutumin da ke tuka kwalekwalen ya tsallake rijiya da baya a wannan hatsari. Shugaban hukumar ya kara da cewa, an samu nasarar gano gawarwaki, kuma har an bunne su. Ya shawarci direbobin kwalekwale da su dunga kulawa duk lokacin da su ke tuka kwalekwalensu.

Ya cigaba da cewa, gwamnati za ta dauki mataki wajen samar da rigunar ruwa ga matafiya domin dakile faruwar irin wannan lamari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!