Connect with us

RAHOTANNI

Garin Da Aka Shafe Shekaru 10 Ba A Haifi Da Namiji Ba

Published

on

A lokacin da aka gudanar da gasar aikin kashe wuta na matasa, Sarauniyar garin Miejsce Odrzanskie na kasar Poland, Krystyna Zykziak, mace mai shekaru 67 da haihuwa, ta yi nuni da wani abu mai ban mamaki a karamin garin na kasar Poland. Inda ta lura da cewa gabaki-dayan wadanda suke a cikin gasar ‘yan mata ne.

Dalilin hakan kuwa mai sauki ne kuma mai ban mamaki. Domin an shafe sama da shekaru 10 ba a haifi da namiji ba a garin na Miejsce Odrzanskie.

Karancin mazajen a garin ya kai ga Sarauniyar garin har ta sanya kyautar kudi ga duk wasu iyalan da suka yi hobbasan haihuwar da namiji.

“Wasu kwararru masana kimiyya sun yi nuni a kan dalilin haihuwar ‘ya’ya mata zalla a garin,” in ji Rajmund Frischko, Sarauniyar garin na Cisek, wanda shi ne gundumar da garin yake a cikinsa,  Na ma sami wasu Likitoci da suke kirana daga sassan kasar nan suna gaya mani yanda za a yi a sami haihuwar da namiji a cikin garin.

Ta ce, na yi Magana da wani Likita da ya yi ritaya da ke tsakiyar kasar ta Poland, wanda ya ce samun daukan cikin da namiji ya danganta ne da abincin da uwar ke ci.

Frischko ta yanke shawarar bayar da kyauta ga duk wasu iyalan da suka fara haihuwar da namiji a garin.

“Kafafen yada labarai suna ta Magana a kanmu, ina ma tunanin sanyawa wani layi sunan duk wani da namijin da aka fara haihuwa a nan,” in ji ta. Tabbas zai sami kyauta mai tsoka, za ma mu dasa wata bishiya wacce za mu mabaceta da sunan yaron.

Kamar wasu kauyakun kasar ta Poland masu yawa, tabbas wannan garin namu ya sami koma bayan habakan al’umma. A bayn yakin Duniya na II, garin yana da mutane 1,200, amma a halin yanzun kwata-kwata mutane 272 a cikin garin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: