Connect with us

WASANNI

Manchester City Ta Fi Kowacce Kungiya Kashe Kudi A Duniya

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ke kasar Ingila ta hada tawagar ‘yan wasa da ta kai ta yuro bilyan daya, kungiya ta farko da ta yi haka a duniya kamar yadda wani rahoto ya tabbatar a ranar Talata.
Manchester City, wacce ta ci moriyar karbar kungiyar da kamfanin Abu Dhabi ya yi tun a shekarar 2008 ta kashe Yuro biliyan daya da miliyan 14 kan ‘yan wasanta, wato kwatankwacin fam miliyan 906 kenan, yayin da Paris Saint Germain ta Faransa ta kashe Yuro miliyan 913, a matsayi na biyu, Real Madrid ta Sipaniya, a matsayi na uku ta kashe yuro miliyan 902.
Darajar abin da aka kashe kan ‘yan wasan Manchester City ta ninka ta kungiyar kwallon kafa ta Norwich har sau 32 kamar yadda kunshin wannan rahoto ya fitar kuma akwai kungiyoyi da dama da abinda Manchester City din ta kashe ya ninka darajarsu a duniya Sannan CIES, wato kungiyar da ta yi wannan bincike, wacce ke kasar Switzerland, ta yi nazari ne kan manyan ‘yan wasa dake manyan gasannin lig-lig na Turai hudu, wato firimiyar Ingila da La liga da Siriya A da gasar Bundesliga ta kasar Jamus. Paderborn, kungiyar kasar Jamus da ta samu ci gaba zuwa babban gasa a wannan kaka, ita ce mai tawaga mafi araha, na fam miliyan 3 da dubu 57 kuma kawo yanzu duk acikin wadannan kasashe babu kungiya mai arahar kungiyar.
Ga jerin kungiyoyi 10 na farko da darajarsu a kudin Yuro:
1. Manchester City – 1.014 billion
2. Paris St-Germain – 913m
3. Real Madrid – 902m
4. Manchester United – 751m
5. Juventus – 719m
6. Barcelona – 697m
7. Liberpool – 639m
8. Chelsea – 561m
9. Atletico Madrid – 550m
10. Arsenal – 498m.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!