Connect with us

JAKAR MAGORI

An Damke Wani Mutum Ya Na Noman Wiwi A Kebbi

Published

on

Hukumar sha da fataucin muyagun kwayoyi (NDLEA), ta samu nasarar damke wani mutum mai suna Abdullahi Sani dan shekara 40, mai yara guda shida, bisa noman tabar wiwi a gonarsa da ke kauyen Shingi cikin karamar hukumar Danko/ Wasagu ta Jihar Kebbi. Kwamandar hukumar ta jihar, Peter Odaudu, shi ya bayyana hakan lokacin da ya ke ganawa da manema labarai ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa, gonar ita ce ta biyu a girma wanda a ka gono ana noma wiwi a cikin jihar. Ya ce, “bisa bayanan sirri da mu ka samu, jami’an hukumar NDLEA sun gudanar sa sintiri na musamman a jihar ranar 5 ga watan Satumbar shekarar 2019, inda su ka gano gonar wiwi a kauyen Shingi tare da lalata gonar.”
Ya kara da cewa, sun damke wanda a ke zargin da shuka muyagun kwaya kuma za a hukunta shi a gaban kuliya. “Mun samu kilomita 46 na shukar wiwi a cikin gonar. Wannan ba karamin hatsari ba ne, a ce an samu irin wannan lamari a cikin Jihar Kebbi, a matsayin jihar da ke shan muyagun kwayoyi, ai idan irin wannan lamari ya cigaba, to sai jihar ta zama jihar mai samar da muyagun kwayoyi,” in ji shi.
Ya bayyana cewa, hukumarsa ta samu nasarar cafke wani mai siyar da maganin gargajiya mai suna Arage Rikici dan shekara 55, a ranar 24 ga watan Yulin shekarar 2018, bisa laifin noma tabar wiwi, a kauyen Kukin da ke cikin karamar hukumar Fakai ta jihar. Ya gargadi manoman jihar a kan kar su yadda su dunga noma haramtattun kwayoyi. Ya shawarce su a kan su cigaba da noma abincinsu domin su samu kudi. Ya kuma yi kira da masu gonakin jihar a kan kar su amince a dunga noma musu tabar wiwi a gonarsu, domin ya na kawo matsaloli da abincin da su ke nomawa.
Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ofishin hukumar NDLEA da ke Birnin Kebbi, wanda a ke zargi da noma wiwin, ya bayyana cewa, ya noma tabar wiwin ne domin ya sha shi daya, sannan ya taimaki abokansa wadanda su ke bukata. “Ni dai ina da mata har da yara guda shida. Ina sane cewa, doka ne shuka tabar wiwi, amma ina rokon hukumomi su yafe min. Na rantse ba zan sake shukawa ba,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!