Connect with us

KASASHEN WAJE

Nijar: Bukin Karrama Dalibai Masu Kwazo Da Hazaka A Fannin Kimiyya

Published

on

Jamhuriyar Nijar shugabar gidauniyar Guri wato uwargidan shugaban kasa Hajiya Aichatou Issouhou Mahamadou, ta jagoranci bikin karrama wasu dalibai sama da 200 da suka fi nuna kwazo, da hazakar karatu a fannin ilimin kimiya.

Wannan shine karo na tara da ake shirya irin wannan buki na bayar da tukwici da lambobin yabo ga daliban da suka fi abokansu hazakar karatu, da nufin cusawa matasan Nijar kwadayin romon dake tattare da ilimin zamani.

Ousman Kadri Nouhou shine daraktan zartarwar gidauniyar Guri Bie Meilleur wace ke dauke da dawainiyar wannan tsari mai sunan Prid de l’Edcellence et du merite. Samarwa Nijar wadatattun ma’aikatan da suka kware a fannonin dake ciyar da kasa gaba, na daga cikin abubuwan da gidauniyar Guri Bie Meilleur ke hange a karkashin wannan tsari na karrama daliban makarantun boko, inji shugabar wannan gidauniya uwargidan shugaban kasar Nijar Hajiya Aichatou Issouhou Mahamadou.

‘Yaran da suka yi nasarar shiga sahun hazikan daliban wannan shekara sun samu tukwici kala kala masu tsoka, abin da ake ganin zai iya sassauta wahalhalun iyayen yaran, da abin ya shafa. Wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma, ya zanta da wasu daliban da suka je Yamai takanas daga jihohi domin karbar nasu tukwicin.

A yammacin yau Laraba shugaban kasa Issouhou Mahamadou ke karbar wadanan dalibai a fadarsa domin yi masu gargadi akan bukatar su maida hankali akan karatu, yayin da su ma malaman makarantar da aka baiwa lambar yabo saboda kwarewa da gwada kishi akan aiki zasu samu jinjina daga gareshi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: