Connect with us

BIDIYO

Yadda Kotu Ta Bada Belin Naziru Sarkin Waka

Published

on

Wata da ke zamanta a Rijiyar Zaki da ke birnin Kano a karkashin jagoranci Mai Shari’a Aminu Fagge ta amince da bayar da belin Sarkin Wakar Sarkin Kano, Alhaji Naziru M. Ahmad, a yau Alhamis, 12 ga Satumba, 2019.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ce ta gurfanar da shi bisa zargin sa da Hukumar Tace Finafinai ta jihar Kano karkashin jagorancin Isma’il Afakallahu ke yi da sakin wakoki na cin zarafi ba bisa ka’ida ba.

A jiya Laraba ne ‘yan sandan su ka je gidan mawakin su ka gudanar da bincike, inda daga bisani su ka yi awon gaba da shi.

Bayan ya kwana a hedikwatar ‘yan sanda da ke Kano a Bompai ne su ka kai shi kotu neman a hukunta shi kan zargin yin wakokin batanci da sakin su a gari ba bisa ka’ida ba; zarge-zargen da Sarkin Wakar ya musanta.

Bayan sauraron bangarorin biyu ne, sai Mai Shari’a Aminu Fagge ya amince da bayar da belinsa bisa wasu sharudda da su ka hada da zai kawo ma’aikacin gwamnati mai matakin albashi na 12 da kamfanin da ya biya haraji na tsawon shekara uku baya da jingine Naira 500,000 tare da ajiye fasfonsa ga kotun. Haka nan kuma sai wani Mai Unguwa ko Dagaci ya tsaya ma sa.

Rahotanni sun tabbtarwa da wakilin LEADERSHIP A YAU cewa, kotun ta cika makil da dimbin masoyan Nazirun.

Idan dai za a iya tunawa, da ma Sarkin Wakar ya na cikin wadanda a ke zargin hukumar tace finafinan a karkashin jagorancin Afaka ta ke raragefen kamawa tun bayan kammala zaben gwamnan Kano na 2019, wanda Nazirun na cikin wadanda su ka yaki bangaren gwamnatin jihar.

Wata majiya ta nuna cewa, wasu a cikin fadar gwamnatin jihar sun yi fushi matuka da irin rawar da Sarkin Wakar ya taka a lokacin zaben, inda su ke kallon sa a matsayin wanda ya ci amanarsu ko ya butulce mu su.

Bugu da kari, a na ganin cewa, kusancin mawakin da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda ba sa ga maciji da Gwamnan Jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya taka rawa wajen huce haushi kan Sarkin Wakar.

Daga cikin wadanda a ka taba bayar da rahoton akwai yiwuwar hukumar ta kama, akwai Aminu Alan Waka, wanda ya garzaya kotu ya amso odar taka burki kan kama shi, saboda farmakin da jami’an tsaro su ka kai ma sa a ofishinsa da ke Zoo Road.

Haka nan akwai kuma Darakta Sunusi Oscar, wanda a kwanakin baya a ka kama shi har sai da ya shafe kwanaki a gidan yari kafin a bayar da belinsa.
labarai

%d bloggers like this: