Isa Abdullahi Gidan Bakko" />

2020: Sabon Irin Masara Na ‘TELA MAIZE’ Zai Shiga Hannun Manoma  – Farfesa Rabi’u

Farfesa Rabi’u

Wakilinmu da ke Zariya ISA ABDULLAHI GIDAN BAKKO ya sami damar zantawa da wani fitaccen masanin ayyukan noma da ke cibiyar bunkasa dabarun noma ta Jami’ar Ahmadu Bello (IAR) mai suna FARFESA RABI’U ADAMU, wanda ke zama a matsayin shugaban binciken aikin gona na sabuwar irin masara ta ‘’TELA MAIZE NIGERIA‘’da wannan cibiya ke ci gaba da gudanar da bincike a kan sabuwar masarar da aka ambata.

Me ya bambanta wannan sabuwar masara ta TELA MAIZE da sauran irin masarar da ibiyarku ta shafe shekaru tana samarwa da manoma na ciki da wajen Nijeriya ?

Lallai akwai bambanci mai yawa, na farko, mafiya yawan masarar da aka samar aka kuma gudanar da bincike kafin a fitar da su, ba su da wasu sinadirai ko kuma wata kariya daga kamuwa daga wani Kwaro ko kuma kwari da suke damun masara ko kuma karar masara da ake kira da sunan sambora da harshen turaci, duk masarar da mu ked a su, ko kuma mu ka samar a wannan cibiya ta (IAR) ba su da wadannan kariya da na ambata, amma wannan masara ta TELA MAIZE ta na da kariya daga kwari da kuma daure rashin ruwa da kuma auki da sabuwar masarar ke da shi, amma sauran masarar ba su da wannan kariya Kuma matukar manomi ya sami wannan sabuwar irin masara, zai samu canji a noman da yake yi, wato zai sami amfanin gonar da bai saba samu bag a kuma saurin yi, game da auki kuma a kowaci kadada daya za a iya samun tan daya za a iya samun tan biyar da rabi zuwa fiye da haka wato shi har zuwa da rabi., musamman in an bi umarni da kuma shawawarwarin da aka ba wanda ya yi amfani da wannan iri na TELA MAIZE.

Kamar wadanne ire-iren sinadirai wannan sabuwar masara ke da su, da sauran masara da ku ka samar ba su da su ?

 

Lallai tana da sinadirai da yawan gaske, kamar wadanne sinadirai ke nan ?

Wannan sabuwar masara ta na da sinadiran kara lafiya da dai sauran sinadirai masu yawan gaske da wani sindiri mai kara karfin idanu musamman idanun yara.

Tsawo wane lokuta kuka dauka zuwa yau da za mu iya cewar zuwa tattaunawar da muke yi da kai, ba ku kammala binciken ba ?

A gaskiya, zuwa wannan shekarar da muke ciki, mu na cikin shekara ta shida ke nan mu na gudanar da wannan bincike na samar da sabuwar masara ta TELA MAIZE, amma mu a nan Nijeriya, shekara biyu ke nan mu na gudanar da wannan bincike.

Za mu so ka yi ma na bayanin alhairan da suke tattare da wannan sabuwar masara ta TELA MAIZE.

Gaskiya wannan masara ta TELA MAIZE ta na da alhairai ma su yawan gaske, a baya manoma su na kukan rashin samun amfanin gonar da suka noma a baya, shi ya sa aka samar da wannan iri da na ambata, amma wanda muke shukawa a yau, bai wuce a sami tan biyu ba a kadada daya, amma kamar yadda na bayyana a baya, a kadada daya, za a iya samun tan biyar zuwa shida na masara, in an shuka TELA MAIZE, musamman in sa ma tat akin zamani bisa shawarwarin da aka ba manomin day a shuka wannan sabon iri.manomi zai sami raguwar sat akin zamani, zai kuma sami amfanin gona da yawa, zai rage yawan bata gonaki a dalilin sa takin zamani, kuma yawan amfani da takin zamani yak an kawo matsala ga yanayi da ke haifar da cututtuka da yawan gaske.

Ya ya ya manomin da ke kauyen-kayau ta wasu hanyoyi wannan cibiya ta tsara ta yadda manoman za su sami wannan sabon irin masara zai kai garesu a cikin sauki ?

Wannan sabon iri na musamman ne, ba a ko wane wajen sayar da iraruwa za a sami wannan sabon iri na TELA MAIZE ba, sai dai wajen kamfano in da suke sayar da iraruwa ne wannan cibiya ta kulla alaka da su, kuma ire-iren wadannan kamfanoni da suke sayar da iraruwa, akwai su a manyan garuruwan Nijeriya baki daya, daga nan sai manoma kananan da ka ke magana zai kai garesu, amma ba cikin kasuwa za a sami wannan iri ba

 

Zuwa wane lokaci ku ke sa ran kammala binciken da ku ke yi da manomi zai samu ?

Muna sa ran za mu kammala wannan bincike in Allah ya yadda a shekara ta 2022, amma a shekara ta 2021, a badi ke nan, za mu yi gwajin wannan sabon iri na TELA MAIZE  a gonakin gwajin da mu ka mallaka a karkashin cibiyarmu ta binciken ayyaun gona ta (IAR) a nan Zariya, daga kammala binciken da mu ka yi, sai mu fara shirin rarraba shi ga wadannan kamfanoni da suke sayar da iraruwa a sassan Nijeriya, mu na sa ran, kamar yadda na bayyana a baya, a shekara ta 2022.

Kafin dai mu fiyar da wannan sabon iri, gwamnatin tarayya za ta turo kwararru wannan cibiya ta mu inda za su gwada wannan iri tare da bincike maizurfi, daga mnan sai a yanke hukumci mika sabon irin ga wannan cibiyoyin sayar da iraruwa kamar yadda na bayyana a baya.

A karshe, bayan kun saki wannan sabon iri ga wadannan kamfanoni, za ku sa ido ne ga manoma na ganin sun yi amfani da bin dokokin da ku ka tsara wajen shuka wannan sabon iri ?

Lallai akwai tsarin sa ido da kuma bibikon manoman da suka yi amfani da sabon irin ta yadda da zarar sun shuka, su amfana da noman da suka yi, wato su sami amfani fiye da yadda suka saba samu, ita gwamnatin tarayya ta amfana da wannan sabon irin na yadda za ta kara samun kudaden shiga a lalitar ta, kuma bibiyan da wannan cibiya ta mu za ta yi a tsakanin tad a manoman da suka shuka sabon irin, za a yi shekara biyu zuwa uku a na sa ido a kansu, har zuwa lokacin da za mu fahimci sun gane yadda za su yi amfani da wannan sabon iri na TELA MAIZE.

Exit mobile version