Connect with us

LABARAI

Zaman Lafiya Da Hadin Kai Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Su Sa A Gaba – Jangebe

Published

on

Sarki yakin miyetti Allah na Jihar lagos, Alhaji Sanda Jangibe ya nemi ‘Yan Nijeriya a duk inda suke su rungumi zaman lafiya da juna tare da hadin kai a tsakaninsu, domin ta haka ne kawai za a samu ci gaban kasar ta Nijeriya da kuma al’ummarta.

Ya yi wannan kiran ne sa’ilin da yake hira da ‘yan jaridu a Abbatuwa da ke birnin Legas, bayan wani zabe da kungiyar ta Miyetti Allah ta gudanar domin samar da shugabanta na Jihar Legas.

Sarkin yakin kungiyar, ya karada cewa duk wani abu da za a yi na ci gaba ba zai yiwu ba matukar babu hadin kan ‘yan kasa da kuma samun yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya kuma yi kira ga ‘yan arewa mazauna kurmi du karace wa fada da gaba da junansu tare da tabbatar da hadin kai a tsakaninsu don ciyar da harkokinsu na neman halaliya gaba.

Ya ce fadace-fadace da rigingimu babu abin da za su haifar illa gadar da asara da kuma barin wa ‘yan baya masu zuwa abin kunya. Ya kara da cewa, “Ina kira ga ‘yan arewa da suka zo nema a Legas da kuma duk yankin kudancin kasar nan su so juna, su taimaki juna, kowa ya zauna lafiya da dan’uwansa, ban da fada, domin mu ci gajiyar abin da ya baro da mu gida muka zo nan”.

Sarkin yakin na Miyetti Allah na Jihar Legas, Alhaji Sanda Jangibe ya kuma roki matasa da su kaucewa shaye-shaye da dukkan wani nau’i na tayar da husuma, sannan su dage da nema ilimi da kuma sana’ar da za su rike kansu, kasancewar da sana’a ce za su yi alfahari.

Alhaji Sanda Jangibe ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari buhari saboda irin kokarin da yake yi na cigaban kasa, kana ya nemi ‘Yan Nijeriya su ba shi hadin kai don ya samu nasarar gudanar da ayyukan alkhairi da ya sanya a gaba. “Bayan haka, ina kuma rokon ‘Yan Nijerya don Allah mu kauce wa aiki na ta’adanci da rashin bin doka, duk wadannan babu abin da suke yi illa bata kasa da haddas asarar rayuwa da dukiyoyin jama’a”.

Alhaji Sanda ya yaba wa shugabannin Miyetti Allah musamman na reshen Legas Abbatuwa, bisa kyakkyawan shugabancinsu. Haka nan ya yaba wa Sarkin Fulanin Abbatuwa Alhaji Bello Danbaffa, kana ya jinjina wa shugaban da aka sake zaba ya koma kuejerarsa ta Alhaji Abdullahi Lelega. Sai kuma sauran wadanda ya yaba musu bisa gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban jama’arsu da suka hada da: Alhaji Guruna, Alhaji Bello Ganbori, da Alhaji Audu Kala.

Daga karshe ya nemi ‘Yan Nijeriya su ci gaba da yi wa kasar addu’a domin samun nasararta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: