Connect with us

MAKALAR YAU

Lambar Yabon Kwamitin Shugaban kasa: Tabbas NIS Ta Cancanta

Published

on

Daga lokacin da gwamnati mai ci ta hau kan karagar mulki tun a wa’adin farko, a ranar 29 ga watan Mayun 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran ‘yan majalisarsa ta zartaswa suka fara zurfafa tunaninsu kan yadda za a farfado da tattalin arzikin kasa, kasancewar tattalin ya auka cikin ka-ka-ni-ka-yi bisa faduwar darajar danyen mai da kasar take tinkaho da shi wajen samun kudin shiga.

A cikin shawarwarin da shugaban kasan da kwararrunsa kan bunkasa tattalin arzikin kasa suka aminta da su domin tayar da komadar tattalin arzikin akwai batun hanyoyin da za a bi a saukaka matakan hada-hadar kasuwanci. Domin cimma hakan, an umurci dukkan hukumomin da suke da ruwa da tsaki kan hulda da ‘yan kasashen waje su sassauta matakan sahale wa ‘yan wajen shigowa cikin kasa domin zuba jari. Hukumar Kula da Shige da Ficen kasa (NIS) tana daga cikin wadannan hukumomin.
Tabbas wannan dabara ta haifar da kyakkyawan sakamako, kasancewar an samu shigowar ‘yan kasar waje da dama masu zuba jari a sassa daban-daban na bunkasa tattalin arziki irin su noma, ma’adanai, masana’antu, sufuri da dai sauransu.
Bisa la’akari da rawar ganin da Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa ta yi wajen cika umurnin shugaban kasa na saukaka matakan hada-hadar kasuwancin a cikin kasa, Kwamitin Shugaban kasa Mai Kula da Samar da Ingantaccen Yanayin Kasuwanci (PEBEC) ya ba ta lambar yabon musamman a kan tsere-wa-tsara da kuma zama Hukumar da ta fi samun kwarya-kwaryan sauye-sauye masu ma’ana a tsakanin hukumomin gwamnati rankacakaf, wadda aka ba ta a ranar 11 ga watan Maris din shekarar 2020.
Wani abin birgewa game da wannan shi ne, an kira hukumar har zuwa fadar shugaban kasa inda aka damka mata lambar yabon a wani biki na musamman da Kwamitin Shugaban kasan na PEBEC ya shirya a zauren taro na fadar.
Shugaban Hukumar Kula da Shige da Ficen ta kasa, Muhammad Babandede wanda daya daga cikin mataimakansa, DCG Graham ya wakilta wajen karbar lambar yabon, ya bayyana farin cikinsa mara misaltuwa da wannan ci gaba da NIS ta samu. Kana ya yi godiya a madadin shugabanni da sauran jami’an NIS bakidaya wanda ya ce sun yi aiki tare a matsayin tsintsiya madaurinki daya har aka samu wannan nasara da kuma sauran kwazon aiki da suka nuna a kan sauye-sauyen da suka saukaka hada-hadar kasuwanci ta hanyar tsarin Biza.
Ganin wannan nasara da hukumar ta samu, tunanina ya tafi wurin zakulo irin namijin kokarin da NIS ta yi da har ya kai ta ga samun wannan lambar yabo da ta sa ta zama zakara a fagen samar da sauye-sauye masu ma’ana.
Hukumar ta NIS a karkashin Shugabancin Muhammad Babandede ta gudanar da sauye-sauye da daman gaske da suka saukaka yanayin hada-hadar kasuwanci ta hanyar bullo da sabon tsarin Biza wanda a karkashinsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kundi na Bizar a ranar 4 ga Fabarairun 2020, a fadarsa da ke Abuja. Wadannan sauye-sauye sun kara wa Bizar kasar nan tagomashi a fagen tsare-tsaren bayar da biza na kasashen duniya. Haka nan, sauyin ya samar da kafar da ‘yan kasashen waje za su nemi Bizar Nijeriya ta shafin intanet cikin sauki.
Har ila yau, wani abu da ya kara bai wa NIS damar lashe wannan lambar yabo shi ne kaddamar da gyarar fuska a kan daukacin takardun hukuma a kan shige da fice da ake bayarwa tun a zamanin da aka kafa dokar shige da fice a 1963, inda aka samar da sabbin tanade-tanade a dokar; daidai da zamani a shekarar 2015 da 2017. Da kuma samar da kundin tsare-tsaren kula da kan-iyakokin kasa da za a yi aiki da su a tsakanin 2019 zuwa 2023. Da samar da dokokin tsarin aiki na shige da fice da sauran ayyuka a dukkan sassan NIS na 2019.
Bisa sauye-sauyen da Hukumar ta NIS ta tasa a gaba, a tsakanin shekara uku kacal an yi bita tare da kwaskwarima a kan takardun Fasfo inda hakan ta kai ga samar da Fasfo da za a yi aiki da shi na tsawon shekara 10 mai kunshe da alamomi na tsaro guda 25 daidai da ka’idar Hukumar Shige da Fice ta Duniya da ake amfani da su wajen tantance ingancin fasfo.
Wani muhimmin sauyi da NIS ta kawo kuma shi ne samar da kundin aiki da za a rika aiki da shi wajen kula da shige da fice a tsakanin shekara hudu, inda za a rika bitarsa da zarar shekarun da aka diba na aiki da shi sun cika. Kundin tsare-tsaren kula da iyakokin kasa na 2019 zuwa 2023, da hukumar ta samar a bara, shi ne ke jagorancin fagen ayyukan kula da iyakokin kasa, wanda a wani bangarensa ne aka samar da Na’urorin Tantance Bayanai (MIDAS) a manyan mashigin kasa da kuma wasu filayen jiragen sama guda hudu na kasar.
Har ila yau, a bangaren kwarya-kwaryar gyarar fuskar da NIS ke yi, ta daga darajar sashen kula da harkokin jami’anta da bincike a kan tsare-tsaren gudanarwa daban-daban na raba wa ma’aikata ayyuka da tura su wuraren da za su yi aiki, sai kuma biyan albashi da sauran hakkokin ma’aikata da aka mayar ta na’ura kai-tsaye duk a cikin tsarin tafiyar da ayyukan NIS.
Bugu da kari,bangaren kula da shige da ficen baki ya kara samun wani sauyi na ci gaba mai kayatarwa a lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin yi wa bakin wajen da ke zaune a Nijeriya rajista, inda aka yi musu afuwa ta wa’adin wata shida su je su yi rajistar domin a samu damar daukar bayanan bakin da suka shigo ta bayan gida da kuma wadanda suke zama a cikin kasa ba bisa ka’ida ba. Wannan yana taimakawa wajen samun bayanan dukkan bakin da suka shigo kasa da kuma aiki da bayanan a tsakanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati.
Tsarin bai wa ‘Yan Afirka masu Fasfon kungiyar Tarayyar Afirka Biza nan take yayin da suka shigo cikin kasa da sauran wadanda suka cancanta a karkashin ayyanawar da Shugaban kasa ya yi game da tsarin bayar da bizar nan take ga ‘Yan Afirka, shi ma wani gagarumin sauyi ne da NIS ta kaddamar domin cimma nasarar saukaka hada-hadar kasuwanci. Domin a karkashin wannan tsarin ne za a samu damar kara dinke Afirka ta zamo tsintsiya madaurinki daya, da ba su walwalar kai-komo a kasashensu na Afirka a matsayinsu na ‘Yan Afirka. An yi kyakkyawan tanadin kula da tsaron kasa a karkashin wannan tsarin na bayar biza nan take.
Wadannan kadan ne daga cikin sauye-sauyen da ko shakka babu suka daga darajar NIS a karkashin shugabancin Muhammad Babandede har ta kai ga samun wannan lambar yabo na Kwamitin Shugaban kasa. Tabbas NIS ta cancanta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: