Connect with us

LABARAI

COVID-19: Sarkin Gwandu Ya Bada Shawarar Dawo Da Biyan Jangali

Published

on

Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammad Iliyasu Bashar, ya kawo shawara ga gwamnatin Jihar Kebbi da ta dawo da biyan kudaden haraji wanda daidaikun mutane suke biya da kuma kudaden harajin Jangali, wanda makiyaya ke biya a kan shanayensu, domin samar da bunkasa da tallafa wa kudaden shiga da gwamnatin Jihar Kebbi ke kukansa.

Sarkin ya bayar da wannan shawarar ce a wajen zama na musamman na masu ruwa da tsaki a Jihar wanda gwamnan Jihar ya kira domin duba halin da tattalin arzikin Jihar ke ciki.
Sai dai kuma, Sarkin Argungun a Jihar, Alhaji Samaila Muhammad Mera, a na shi shawarar cewa ya yi tilas ne mutane su yi sadaukarwa ta musamman domin magance matsalar rashin tabbas din da tattalin arzikin Jihar ke ciki.
Yana mai cewa, tilas ne gwamnati ta yi dubi na musamman a cikinta, ko da kuwa za ta kai ne da gwamnatin ta dakatar da biyan albashin ma’aikatan Jihar, domin ta aiwatar da wasu mahimman ayyukan nata da suka shafi kare lafiyar al’ummar Jihar.
Shi kuwa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Samaila Abdulmumin Kamba, ya dage ne a kan cewa Majalisar Jihar tana nan a kan kudurinta na kare jin dadin al’ummar Jihar.
Ya ce a shirye majalisar take domin ta sa hannu a kan duk wata doka da gwamnatin Jihar za ta iya gabatar mata domin neman yin gyara a kan kasafin kudin Jihar.
Da yake bayar da na shi shawarar a wajen zaman, Babban sakatare kuma babban Likitan Asibitin kwararru na, Sir Yahaya Specialist Hospital da ke Birnin Kebbi, Dakta Aminu Haliru Bunza, ya shawarci gwamnatin Jihar ce da ta hanzarta sanar da kulle dukkanin makarantun Islamiyya da na almajirai masu karatun allo da ke cikin Jihar domin magance yaduwar cutar ta Corona birus a cikin Jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: