Connect with us

LABARAI

Ku Tsaya A gida Gobe Juma’a: Idris Tune Ga Ma’aikatan Jihar Katsina

Published

on

Shugaban Ma’aikatan gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Idris Usman Tune ya bada umarni ga dukkanin ma’aikatan jihar da su tsaya a gida gobe juma’a sakamakon matakan kariya da gwamnati ke dauka akan cutar mashako

Shugaban ya yi wannan kira ne domin cika umarnin da gwamnatin jihar Katsina ta bada na cewa a kauracewa haduwa waje guda, sannan a nisanta da juma tare da yin amfani da sabulun wanke hannu da na’urar auna zafin jiki.

Alhaji Idris Tune wanda ya ce ma’aikata suna da rawar da za su taka wajan fadakar da jama’a su guji duk wani abu zai jawo kamuwa da wannan cuta ta mashako ko Cobid 19 kamar yadda ake kiranta.

“Kirana ga ‘yan uwana ma’aikata shine, a bi duk wasu ka’idoji da masana kiwon lafiya suka shinfida, mu kiyaye yawan gaishe-gaishe da muka saba da shi, abi ka’ida na yin amfani da sabulun wanke hannu sannan idan za a’ yi atishawa a rika rufe hanci saboda kadda a yada wannan cuta cikin al’umma” inji shi

Haka kuma ya yi kira ga ma’aikatan jihar Kasina da su zauna a gida gobe juma’a, inda ya kara da cewa za su duba su ga yadda ma’aikatan su amshi wannan umarni tun daga gobe juma’a har zuwa ranar lahida, duk abinda suka gani shi zai ba su damar dawowa da ma’aikatan a bakin aiki ranar litinin ko kuma su cigaba da zaman gida sai abinda Allah Ya yi

A cewarsa dukkanin ma’aikatan jihar Katsina za su zauna a gida ba kamar yadda wasu jahohi suka yi ba, inda suka umarci wani bangare na ma’aikata da su zauna gida kamar da matakin 1 zuwa 12, Tune ya ce sai nan gaba za su duba yiwuwar yin haka, amma dai yanzu suna umarta dukkanin ma’iakata da su zauna a gida.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: