Wasu manoman Masara a jihar Oyo, sun shelanta cewa, za a fusknaci karancin Masara a Nijeriya a 2021, inda suka yi nuni da cewa, manomanta a kakar noma ta shekarar 2020,sun yi asarar miliyoyin naira saboda gazawar da Gwamnatin Tarayya ta yi, na taimakawa fannin aikin noma a kasar nan.
Manoman wadanda ke a yankin Oke cikin sun bayyana hakan ne a karkashin inuwar kungiyar manoman mazauan jihar Oyo, inda suka danganta karancin da za a fuskanta na Masarar kan rashin yin dubi a kan yadda yanayin ambaliyar ruwan sama zai kasance a kasar nan da kuma rashin samar da dauki a fannin da gwamnatin bayar da dauki ta gaza, inda hakan zai janyo karancinta a 2021.
A cewar manoman, ‘ya’yanta, sun yi asarar miliyoyin naira a kakar nama ta 2020 saboda gazawar da gwamnatin ta yi na samar wa da fannin noma taimakon da yakamata.
Yakin na Oke Ogun da ke a jihar Oyo, babu wata tantama ya yi fice wajen noma a duk fadin Kudu maso Yamma da ke a kasar nan.
Sun bayyana cewa, manomanta da dama, sun yanke shawarar kin gaba da nomanta saboda kalubaken rashin kayan aikin noma na zamani.
Takardar bayan taron da shugabansu Mista Alabi Kazeem ya raba wa manema labarai a garin Ibadan sun yi ikirarin cewa, ‘ya’yan kungiyar sun ranci kudade daga daga bankuna da kuma daga gun dai-dai mutane domin noma Masara biyo bayan hasashen yanayi da aka yi kan yawan ruwan sama da za a yi daga watan Okutoba.
A cewarsa, “Akasarin ‘ya’yan kungiyarmu, sun yanke shawarar kin noma Masara saboda karancin ruwan sama, inda ya kara da cewa, amma idan ‘ya’yan kungiyar sunji bayanai daga gun gwamnatin kan yanayi, ta hanyar sashen hasashen yanayi tare da gudanar da gangani da ma’aikatar muhalli da albarkatun kasa ta jihar Oyo cewa, za a samu ruwan sama da ya wa a karahen watannin Okutoba da Nuwamba, manoman za su nemo kudade, domin noma Masara a jihar.”
Sun yi amfani da damar wajen yin kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya samar da wasu sabbin shirye -shirye domin a taimaka wa manoman Masara na gaskiya da ke a kasar nan, inda ya yi kira ga Gwamnan jihar ta Oyo Mista Seyi Makinde, da ya cika alkawarinsa na fadada taimakon gwamnatin na bayar da daukin kudade ga kungiyoyin manoma mazauna jihar da ke a kananan hukumomi 10 a yankin Oke Ogun.
Ya ci gaba da cewa, abin takaici, hasashen yanayin ya janyo ‘ya’yan kungiyar sun yi asarar miliyoyin naira da suka karbo rance daga gun bankuna, dai-daikun mutane da kuma abokan arziki somin su noma Masarar.
Ya ci gaba da cewa, nuna son mu yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar su kawo ma su dauki, inda ya ci gaba da cewa ‘ya’yan kungiyar a yanzu an kai su makura wajen nemo kudaden da za su noma Masara a kakar nama ta 2021.
Sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da babban bankin Nijeriya CBN da su fito da wasu sabbin shirye-shirye masu domin magance kalubalen karancin abinci a kasar, musamman Masara a 2021 ganin cewa, manoman Masara da dama a kasar, sun yan yi asara saboda fa ri.
A cewarsa, a cikin sauki za a iya yin hasashen za a yik arancin Masarar a kasar nan a kakar shekarar 2021, in har, gwamnatin ba ta dauki matakan da suka da ce ba a cikin gaggawa, domin taimaka wa manoman Masarar.
Ya ci gaba da cewa, gwamnan mu na jihar Oyo, ya nuna a zahari gwamnatinsa a shirye ta ke ta bunkasa aikin noma a jihar, musamman noman Masara da kuma habaka, tattalin arzikin jihar, inda ya kara da cewa, muna kira a gare shi ya kara fadada zuba kudade ga guraren noma da kuma bayar da rance ga manoman Masara da ke a yankin Oke Ogun.