Shugaban kungiyar al’ummar musulmi na Jihar Kogi (KOSMO), Alhaji Nasirudeen Yusuf Abdallah ya yi kira da al’umma a kan su zabi cancanta da kwarewa ba jam’iyyar ba a zaben 2023.
Nasirudeen Abdallah ya yi wannan kiran ne a wajen lakcar bikin shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1444 AH da kaddamar da kalandar musulunci da kuma karrama wasu mashahuran mutane da suka ba da gudunmawarsu wajen yada addinin musulunci a Jihar Kogi, wadda aka gudanar a ranan Asabar da ta gabata a masallacin Sharif Aboki da ke birnin Lakwaja.
- Bukatar Tabbatar Da Sabon Kamfanin NNPC Ya Ba Mara da Kunya
- Buhari Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Sufeton ‘Yansanda Tafa Balogun
Ya kuma bukaci musulmi da su tabbatar sun yi rajistar katin zabe, sannan ya gargade su da su kauce wa zaben jam’iyya, a maimakon hakan su zabi cancanta da kwarewa ga ‘yan takarar da za su fitar musu da kitse a wuta.
Shugaban kungiyar KOSMO ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda ‘yan Nijeriya suka tsinci kansu cikin kuncin rayuwa da wahalhalu iri-iri da kuma rashin tsaro.
Ya kuma nuna damuwarsa duba da yadda aka samu wagegen gibi tsakanin talaka da masu hannu da shuni, yana mai cewa talaka na kara dulmiya cikin talauci da fatara, a yayin da kuma masu arziki na kara kudancewa.