Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, sun sasanta rikicin da ke tsakaninsu, tare da kudurin yin aiki tare domin samun nasarar zabe a babban zaben badi.
A baya LEADERSHIP ta rawaito cewa Gwamna Mohammed, ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ficewa daga kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP na shugaban kasa idan har dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya gaza fitowa fili ya karyata wadanda ke yi masa aiki tare da bayyana goyon bayansa na sake tsayawa takara a karo na biyu a Jihar Bauchi.
- 2023: Gwamnan Akwa Ibom Ya Karyata Ajiye Mukaminsa Na Shugaban Yakin Zaben Atiku Da Okowa
- Yin Amfani Da Yanar Gizo Wajen Raya Duniya
Mohammed, wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar a Arewa, ya bayyana haka a wata wasika mai shafi takwas da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Dr. Iyiocha Ayu.
Ayu da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun yi gaggawar kai wa gwamnan Jihar Bauchi ziyara a kwanakin baya.
Duk da cewa taron a sirri aka yi, shugabannin jam’iyyar sun yi watsi da duk wani ra’ayi na sabon rikici a tsakaninsu.
A ci gaba da taron na Bauchi Atiku ya kuma yi wata ganawa da Gwamna Mohammed da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Abuja a daren ranar Talata.
Da yake bayyana sakamakon taron Abuja da aka yi a safiyar ranar Laraba ta shafinsa na Facebook da aka tabbatar, Atiku ya rubuta cewa: “A daren jiya na karbi bakuncin wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyarmu ta PDP a Abuja, mun tattauna halin da jam’iyyarmu da al’ummar kasar nan ke ciki, kuma muka sake komawa kan lamarin don aikin kishin kasa don murmurewa da dawo da Nijeriya don dawo kasa turbar daidai. – AA.”
Idan dai ba a manta ba PDP ta yi ta fafatawa da kungiyar gwamnoni biyar (PDP G5) wato gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike da takwarorinsa na Abia, Oyo, Enugu da Jihar Benue, Okezie Ikpeazu, Seyi Makinde, Ifeanyi Ugwuanyi. da Samuel Ortom.
A baya-bayan nan dai sun kara zafafa adawa da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.