Burinmu shi ne ya kasance tsarin zabenmu ya tabbatar da dukkan kuri’unmu su zama an kirga su. Muna da marmarin tsarin da zai cika dogon burinmu na zabar shugabannin da za su kyautata rayuwar ’yan kasa da gaske maimakon son kansu.
Tun bayan komawar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, ‘yan Nijeriya na ci gaba da fatan ganin an gudanar da sahihin zabe mai inganci da zai ba su damar yin amfani da kuri’unsu a matsayin muryoyinsu.
- APC Ba Ta Da ‘Yan Takarar Sanata A Mazabun Yobe Ta Arewa Da A’Ibom Ta Arewa —INEC
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 95 Za Su Yi Zabe A 2023 —INEC
A karon farko ‘yan Nijeriya na ganin zamanin magudin zabe ya kare ta hanyar bullo da fasahar zamani a harkar zabe. Mun yi imani da gaske cewa a wannan karon za a kirga kuri’unmu saboda da sabon tsarin zabe ta hanyar na’urar zamani ta aike da sakamakon zabe.
Amfanin da na’urar ya sanya kusan a yanzu ba zai yiwu ba a yi amfani da katunan zabe fiye da adadin wadanda aka amince da su a kowace rumfar zabe.
Duk da haka, shin gudanar da sabon tsarin aikin zabe zai iya tasiri wajen hana magudin zabe? Ko kuma zai iya canza yanayin magudin zabe?
A yayin da aka yi nazari a kan yadda ake gudanar da babban zabe, musamman tsarin gudanar da sakamakon zabe da fasahohin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bullo da su a cikin harkokin zabe, watau Bimodal Voters Accreditation System (BVAS) da INEC Result Viewing Portal (IReV Portal),
Ya zo karshe cewa Dimokuradiyyar Nijeriya na kara bunkasa kuma tsarin zabenmu yana kara fitowa fili.
Duk da haka, a cikin nazarin da muka yi game da waɗannan fasahohin, mun gano cewa akwai sauran abubuwan da za a yi don tsarin gudanar da sakamako gaba ɗaya, har ma da gabatar BVAS da IReV Portal.