Kungiyar jagororin kiristoci da musulmai ‘yan siyasa da suka fito daga jihohin arewa 19 da babban birnin tarayya Abuja sun ayyana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 da ke tafe, Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar da suka cimma matsayar mara wa baya.
Kungiyar wacce ta misalta goyon bayan tikitin takarar Atiku/Okowa a matsayin zabin da ya dace ga dukkanin masu neman adalci ga kowani bangare a kasar nan.
- Dogara, Babachir Sun Gana Da Shugabannin Kiristoci Don Daukar Matsaya Kan Zaben 2023
- Rayuwata Na Cikin Hatsari, Ana Kokarin Kashe Ni – Yakubu Dogara
Wannan matsayar na kunshe ne ta cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar jagororin suka yi a Abuja a ranar Juma’a dauke da sanya hannun tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Hon. Mohammed Umara Kumalia da Barista Nunge Mele, (SAN) tare da raba kwafinta ga ‘yan jarida a Bauchi.
Idan za ku iya tunawa dai, gungun kiristocin wadanda suke karkashin tawagar su tsohon Kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara wadanda suka kasance mambobin jam’iyyar APC ne a baya, sun yi ta gwagwarmayar yaki da tikitin Musulmi da Musulmi wanda suka sha alwashin ba za su mara wa dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu baya ba.
Sanarwar kungiyar ya nemi dukkanin al’ummar Nijeriya da su mara wa PDP baya domin bai wa kowani bangare dama a cikin mulki a maimakon nuna wariya ga kiristoci ta hanyar yin tikiri musulmai biyu da APC ta yi.
Sun yi tilawar cewa, kungiyar jagororin kiristoci da musulmai a arewa ta kafa wani kwamiti a ranar 8 ga watan Oktoba domin ya yi nazarin dan takarar da ya dace a mara wa baya cikin manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke tafe.
Kungiyar ta ce, a bisa nazarinta da bincikenta, tikitin takarar Atiku Abubakar na PDP ne kawai ya fi zama a’ala ga dukkanin al’ummar Nijeriya, kuma shine wanda ya fi dacewa a duk cikin manyan ‘yan takarar shugaban kasa guda hudu da suke nema a halin yanzu.
Daga bisani kungiyar sun sha alwashin cewa za su kasa su tsare har sai sun tabbatar APC ba ta samu nasara a zaben 2023 ba, domin a cewarsu an kitsa rashin adalci ga al’ummar kiristoci a yadda aka fitar da tsarin tikitin jam’iyyar.