A makon da ya gabata ne, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mammod Yakubu ya yi alkawarin cewa duk da kalubalen da hukumarsa kefuskanta, za ta gudanar da sahihin zabe mai cike da adalci a 2023.
Ya ce, ‘kuri’un ‘yan Nijeriya ne kadai zai tabbatar da wanda ya lashe zabe a 2023, wannan shi ne kokarinmu ga kasar nan,” in ji Farfesa Yakubu.
- Shekara 62 Da Samun ‘Yancin Kai: Na Damu Da Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki – Buhari
- Darajar Vinicius Junior Ta Sake daukaka
Ko kalamun Farfesa Yakubu zai iya shugabantar INEC wajen gudanar da sahihin zabe a 2023, musamman ma zaben shugaban kasa?.
Dukkan zaben shugaban kasa a Nijeriya yana da matukar muhimmanci da kuma rudani. Ko shakka babu samun cikakken zaman lafiya da hadin kai a Nijeriya ya ta’allaka ne da sakamakon zaben shugaban kasa a 2023.
Gaskiyar lamari shi ne, mutanen Nijeriya suna bukatar fita daga kangin mummunan shugabanci da suka samu kansu a ciki.
A baya, matasa suna nuna halin-ko-in-kula a kan harkokin zabe, amma a wannan lokaci matsa ne suka fi yawa wajen amsar katin zabe a rajistar INEC na zaben 2023.
A yanzu haka matasan Nijeriya sun farka daga dogon baccin da suke yi wajen shiga a dama da su kan harkokin zabe, inda suka sha alkawashin tsunduma a al’amuran zaben shugaban kasa a 2023.
Lallai shigan matasa cikin harkokin zabe gadan-gadan zai samar da sabon sauyi a cikin siyasar Nijeriya.
Saboda haka, hukumar INEC ba ta da wani zabi illa ta yi kokarin gudanar da sahihin zaben shugaban kasa a watan Fabrairun 2023. Dole INEC ta tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ne suka zabi shugaban kasa da hannunsu.
Dokar zabe ta 2022 ta tanadi cewa dole a yi amfani da na’ura wajen bayyana sakamakon. Ko shakka babu amfani da na’ura wajen bayyana sakamakon zabe zai rage magudin zabe.
Wannan ta sa dole INEC ta sake kokari wajen kara ma’aikata da sauran kayayyakin zabe na zamani saboda a samu abin da ake bukata.
Masu sharhin harkokin siyasa dai suna ganin cewa hukumar zabe ba za ta iya gudanar da sahibhin zabe ba har sai ta samu jajirtaccen wakilai a jihohi.
Indan har hukumar zabe tana son gudanar da sahihin zabe, to dole ta samu jajirtattun kwamishinoni zabe a dukkanin jihohin Nijeriya.
Ayyukan kwamishinonin zabe sun hada da kula da dukkan ayyukan ma’aikata na wajin-gadi na INEC da samar da cikakken sahihin sakamakon zabe.
Tambaya a nan shi ne wadannan kwamishinonin zabe da INEC take da su a yanzu za su iya taimaka mata wajen gudanar da shihin zabe?
Tabbas INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe idan ta samu wakilan da za su taimaka mata.
Ya kamata INEC ta yi kokarin tsaftace ma’aikatanta wajen samun nasarar gudanar da sahihin zabe a 2023.
Babu wata hukumar gwamnati da mutane suke da gwarin gwiwa kamar INEC, musamman ma idan aka samu sahihin zabe a 2023.