Lauyoyi da Kungiyoyin Fararen Hula sun murza gashin baki a kan cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi watsi da duk wani dan takarar da bai shiga zaben fid da gwani ba da jam’iyyun siyasa suka tura mata sunayensu.
Gamayyar kungiyoyin fararen hula sun zargi jam’iyyun siyasa da tura wa INEC da sunayen wasu ‘yan takara wadanda ba su shiga zaben fid da gwani ba a matsayin ‘yan takararsu tare da cire sunayen ‘yan takarar da suka lashe zaben fitar da gwani.
Binciken LEADERSHIP ya gano cewa jam’iyyar APC ta tura wa INEC sunayen manyen ‘yan siyasa wadanda ba su shiga zaben fid da gwani ba a matsayin ‘yan takararsu.
Gamayyar kungiyoyin sun siffanta lamarin da rashin adalci tare da bayyana cewa dole jam’iyyun siyasan su fuskanci hukunci domin kuwa kotu ta shirya tsaf wajen yakar irin wannan gurbatacciyar dimokuradiyya.
Da yake zantawa da LEADERSHIP, shugaban gamayyar kungiyoyin fararen huda, Awwal Musa Rafsanjani ya bayyana cewa bai kamata a bar ‘yan siyasa suna yin abin da suka ga dama ba. Ya kara da cewa su ne manyan wadanda suka fi amfana da dimokuradiyya kuma ne suke lalata ta.
Ya ce, “Wannan wasu dabi’u ne da gurbatattun ‘yan siyasa ke yi kuma INEC tana kara musu kwarin gwiwa a wajen gudanar da zaben fid da gwani, saboda ta yaya wadanda ba su shiga zaben fid da gwani ba a ba su damar tsayawa takara a babban zabe.
“Ya kamata ‘yan Nijeriya su dauki darasi a kan irin wannan lamari da suka faru a baya. Idan har irin wannan lamari ya taba faruwa a baya kuma kotu ta rushe zaben wadanda ba su shiga zaben fid da gwani ba, lalle kotu tana nan za ta zantar da hukunci a kan wannan mummunan dabi’a.
“Mutanen da suke gudanar da irin wannan lamari suna amfani ne da matsayinsu kuma ya kamata INEC ta yi watsi da irin wannan lamari.
“’Yan takara sun gudanar da zaben fid da gwani kuma har jami’an INEC sun halarci wurin tare da saka ido da amincewa da sunayen wadanda suka samu nasara, sannan bai kamata a sauya sunayen wadanda suka shiga zaben fid da gwani ba da wasu ‘yan takara daban ba,”
Su ma kungiyar lauyoyi sun bayyana cewa lamarin Ahmad Lawan da Godswill Akpabio, a bayana yake na saba wa dokar zabe.
Manyan lauyoyin Nijeriya sun mayar da martani kan sauya sunayen wadanda suka lashe zaben fid da gwani, inda suka suffanta lamarin da take hakkin dokar zabe.
Babban lauya mai suna Kayode Enitan (SAN) ya bayyana cewa INEC ba za ta taba amincewa da sunayen ‘yan takarar da ba su shiga zaben fid da gwani ba, domin ya saba wa sashi na 31 da 33 na dokar zabe.
Ya ce, “Akwai hanyoyin sauya ‘yan takarar da suka lashe zaben fid da gwani kamar yadda sashi na 31 da 33 na dokar zabe ta tanada, ana iya sauya sunayen ne kadai idan dan takara ya mutu.
“Idan dan takarar da ya lashe zaben fid da gwani ya mutu, to dole ne jam’iyya ta sake gudanar da zaben fid da gwani.
“Amma haka kawai, INEC ba ta da hukumin sauya sunayen ‘yan takarar da suka lashe zaben fid da gwani, sai dai dan takara ya janye ko kuma ya mutu.”
Shi ma babban lauya mai suna Matthew Buka (SAN) ya bayyana cewa doka a bayyana take, domin doka ta tanadar da cewa babu wanda zai tsaya takarar babban zabe har sai ya lashe zaben fid da gwani a karkashin jam’iyyun siyasa.