• English
  • Business News
Wednesday, July 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu

by Sani Anwar
3 weeks ago
in Siyasa
0
2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wasu jiga-jigan ‘yan adawa a Nijeriya, karkashin kungiyar hadaka ta ‘Nigeria National Coalition Group’ (NNCG), na ci gba da kokarin tabbatar da wata hadaka mai karfin gaske da nufin kawar da gwamnatin APC, karkashin jagorncin Bola Ahmed Tinubu.

Wadannan ‘yan hamayya, sun samar da wata kungiyar hadaka da aka yi wa lakabi da ‘All Democratic Alliance (ADA)’, wadda suka aike wa hukumar zabe ta kasa da zummar yi mata rajista, domin zama jam’iyyar siyasa.

  • Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 
  • 2027: An Samu Ruɗani Kan Buƙatar Yi Wa ADA Rajista Don Ta Zama Jam’iyya

Kazalika, tun a farkon wannan shekara ne ‘yan mahayyar suka fara tunanin kafa wata hadaka, domin cimma wannan kudiri nasu da suka sanya a gaba.

Bugu da kari, wasikar wadda suka aika zuwa ga shugaban Hukumar Zabe ta Kasar (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar 19 ga watan Yuni, shugaban jam’iyyar hadakar ADA na kasa, Cif Akin Ricketts da Sakataren riko, Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan kuma Hukumar Zaben ta Kasa (INEC), ta karba a ranar 20 ga watan Yunin da muke ciki.

Har ila yau, kawancen hadakar na kunshe ne da jiga-jigan ‘yan hamayya a fagen siyasar wannan kasa da suka fito daga bangarorin kasar nan daban-daban, daga kuma mabambantan addinai.

Labarai Masu Nasaba

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100

Majalisar Dattawa Za Ta Yi Zama Na Musamman Don Karrama Buhari 

Wannan ne ma dalilin da yasa wasu ke ganin hadakar za ta iya yin karfi kwarai da gaske, kasancewar ta samu wakilci a sassa daban-daban na wannan kasa.

Dalili kuwa shi ne, ‘yansiyasa ne da a baya suka samu damar rike manya-mnyan mukamai, sannan kuma har zuwa yanzu yana da tasiri a fagen siyasar kasar yadda ya kamata.

Manya-manyan jiga-jigan da ake gani a cikin wannan sabuwar tafiya ta hadakar jam’iyyar sun hada da:

Jagoran adawa a kasar, wanda a baya ya sha yin takarar shugabancin kasa, sannan kuma ko a shekarar 2023 shi ne ya zo na biyu bayan da ya samu kuri’a kusan miliyan bakwai.

Alhaji Atiku Abubakar, wanda a yanzu dan jam’iyyar PDP ne; ya kasance guda kuma jigo a siyasar Nijeriya, tun lokacin da ya zama mataimakin shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a shekarar 1999 zuwa 2007.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda ya fito daga Jihar Adamawa da ke Arewa maso gabashin Nijeriya, Bafulatani ne da ake yi wa kallon daya daga cikin masu matukar tasiri a fagen siyasar Nijeriya.

Atiku, na daga cikin fitattun mutanen da suka kulla wannan hadaka da ta haifar da jam’iyyar APC a shekarar 2014, da ta yi nasarar kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP a 2015.

A halin da ake ciki yanzu dai, jam’iyyar PDP na da gwamnoni kimanin 10 a fadin wannan kasa, koda-yake dai kuma, har yanzu babu gwamnan da ya bayyana amincewa da bin Atikun zuwa sabuwar jam’iyyar hadakar, duk da dai ana ganin watakila ficewar tasa za ta sa wasu daga cikin gwamnonin ficewa su su bi shi.

Haka zalika, tsohon dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar LP, na daya daga cikin mutane na gaba-gaba a kafa wannan sabuwar tafiyar ta jam’iyyar ADA.

Peter Obi , wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambra ne, ya kasance na uku a zaben shugaban kasar da ta gabata a 2023, inda ya samu kuri’a fiye da miliyan shida.

Obi, dan asalin kabilar Igbo ne daga Kudu maso gabashin wannan kasa, wanda da ya samu farin jini yadda ya kamata, musamman a tsakanin ‘yan kabilarsa.

Wannan dalili ne ma yasa ake ganin jam’iyyar tasa ta LP ta samu nasara a jihohin kasar nan 12, ciki har da Jihar Legas da Abuja a zaben shugaban kasar na 2023.

Kazalika, jam’iyyarsa ta LP na da gwamnan guda daya a Jihar Abia, sannan kuma ana ganin watakila ya bi shi cikin wannan sabuwar hadaka da ake shirin yi.

Har wa yau, a watan Maris da ya gabata ne Malam Nasiru el-Rufai ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC tare da kuma da komawa jam’iyyar SDP.

Tsohon gwamnan, ya kasance Ministan Abuja a tsakanin shekara ta 2003 zuwa 2007, kafin ya zama gwamnan Jihar Kaduna da ke Arewa maso yammacin kasar, na tsawon wa’adi biyu, wato tsakanin 2015 zuwa 2023.

Fitaccen ɗan siyasar, a kakar zaben 2023; wanda Bahaushe ne dan asalin garin Zaria, ya kasance na gaba-gaba wajen goyon bayan Bola Ahmed Tinubu na APC.

Sai dai kuma, bayan lashe zaben na Tinubu; sai kuma baraka ta kunno kai a tsakaninsa da Nasiru, bayan da majalisar dattawa ta ki amincewa da tantance shi, domin ba shi mukamin minista a gwamnatin ta Tinubu.

Rotimi Amaechi, shi ma guda ne cikin tsofaffin hannu a bangaren siyasar wannan kasa, domin kuwa ya kasance tsohon Gwamnan Jihar Ribas mai arzikin mai fetur da ke yankin Kudu maso kudancin wannan kasa daga 2007 zuwa 2015.

Haka nan, bayan kammala wa’adinsa a matsayin Gwamnan Jihar Ribas din, tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya nada shi ministan sufuri na tsawon shekara takwas daga 2015 zuwa 2023.

Har ila yau, A shekarar 2022 ya bayyana anisarya ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, to amma kuma sai ya sha kaye a hannun Tinubu a zaben fitar da gwani.

A wata hira da ya yi da BBC a baya-bayan nan, tsohon ministan ya ce; a shirye yake domin shiga duk wata hadakar da za ta kawar da gwamnatin Tinubu a halin yanzu.

A gefe guda kuma, Rauf Aregbesola ya taba rike mukamin Gwamnan Jihar Osun da ke Kudu maso yammacin Nijeriya, har na tsawon wa’adi biyu daga 2010 zuwa 2018.

A shekarar 2019, tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya nada shi, mukamin ministan harkokin cikin gida, mukamin da ya rike har 2023.

Aregbesola Bayerabe ne da ya fito daga yankin Kudu maso yammacin Nijeriya.

A farkon shekarar nan ne, Rauf Aregbesola ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar ta APC.

Tsohon jami’in soji, wanda ya taba zama Gwamnan Mulkin Soji na Jihar Neja daga 1984 zuwa 1986, Dabid Mark; dan asalin Jihar Benuwai ne.

Kazalika, ya rike mukamin ministan sadarwa; kafin ya zama dan majalisar dattawa mai wakiltar Benuwai ta Kudu a cikin jihar ta Benuwai.

Har ila yau, shi ne Shugaban Majalisar Dattawa mafi jimawa a mukamin, bayan jagorantar majalisar na tsawon wa’adi biyu, wato shekara takwas daga 2007 zuwa 2015.

Sannan, ya kasance dan asalin kabilar Idoma daga yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya, shi ma yana cikin wannan hadakar jam’iyyar adawa, dumu-dumu.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 2027Tinubu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Yaƙin Iran Da Isra’ila Zai Iya Shafar Zamantakewa Da Tattalin Arziƙin Nijeriya

Next Post

Sin Na Adawa Da Duk Wata Yarjejeniyar Haraji Da Ka Iya Illata Moriyarta

Related

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100
Manyan Labarai

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100

13 hours ago
Majalisar Dattawa Za Ta Yi Zama Na Musamman Don Karrama Buhari 
Siyasa

Majalisar Dattawa Za Ta Yi Zama Na Musamman Don Karrama Buhari 

17 hours ago
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Manyan Labarai

Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

1 day ago
Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Manyan Labarai

Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

1 day ago
Mutumin El-Rufai, Baloni, Ya Fice Daga APC A Kaduna
Siyasa

Mutumin El-Rufai, Baloni, Ya Fice Daga APC A Kaduna

2 days ago
‘Yansanda Sun Hana Gudanar Da Taron Tunawa Da Ranar Haihuwar Obi A Kaduna
Labarai

‘Yansanda Sun Hana Gudanar Da Taron Tunawa Da Ranar Haihuwar Obi A Kaduna

4 days ago
Next Post
Sin Na Adawa Da Duk Wata Yarjejeniyar Haraji Da Ka Iya Illata Moriyarta

Sin Na Adawa Da Duk Wata Yarjejeniyar Haraji Da Ka Iya Illata Moriyarta

LABARAI MASU NASABA

Allah Ya Yi Wa Wakilin Sadarwan Bauchi,  Jafaru Ilelah, Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Wakilin Sadarwan Bauchi,  Jafaru Ilelah, Rasuwa

July 23, 2025
Yadda Muka Zama Bayin ‘Yan Bindiga -Mazaunin Wani Kauye

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyen Katsina, Sun Jikkata Mutane 2, Sun Sace Wasu

July 23, 2025
Ɗan Shekaru 15 Ya Kashe Wani Matashi Kan Rikicin Gona A Jigawa

Ɗan Shekaru 15 Ya Kashe Wani Matashi Kan Rikicin Gona A Jigawa

July 23, 2025
Kwankwaso  Ne Kaɗai Ɗan Siyasar Da Zai Iya Maye Gurbin Buhari — Jigo A NNPP

Kwankwaso  Ne Kaɗai Ɗan Siyasar Da Zai Iya Maye Gurbin Buhari — Jigo A NNPP

July 22, 2025
Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar

Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar

July 22, 2025
Hana Natasha Zaman Majalisa Barazana Ne Ga Dimokuraɗiyya — CLO

Hana Natasha Zaman Majalisa Barazana Ne Ga Dimokuraɗiyya — CLO

July 22, 2025
Taron Kolin Sin Da EU Zai Bayar Da Damar Zurfafa Hadin Gwiwar Sassan Biyu

Taron Kolin Sin Da EU Zai Bayar Da Damar Zurfafa Hadin Gwiwar Sassan Biyu

July 22, 2025
Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100

July 22, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Inganta Fahimtar Juna Ta Hanyar Shawarwari Da Tattaunawa

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Inganta Fahimtar Juna Ta Hanyar Shawarwari Da Tattaunawa

July 22, 2025
Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Kwaskwarimar Majalisar Dokoki Kan Naira Biliyan 7

Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Kwaskwarimar Majalisar Dokoki Kan Naira Biliyan 7

July 22, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.