ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa

by Leadership Hausa
4 months ago
ADC

Kafin zaɓen shekara ta 2027, jam’iyyar APC da hadakar jam’iyyar ADC na gwagwarmayar neman samun goyon bayan mutanen arewa da kuma wacce ta fi dacewa wajen kare muradunsu.

Shugaban jam’iyyar ADC na wucin gadi kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, daɓid Mark, ya bayyana cewa talauci da rashin tsaro da ƙuncin tattalin arziki su ne matsalolin da suke yi wa a arewa katutu.

Shi ma tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma jago a ADC, Babachir Lawal, ya bayyana cewa arewa ta amince da jam’iyyar ADC ta hanyar gamayyar ƙungiyar tuntuɓa kan harkokin siyasa ta ƙasa, a matsayin jam’iyya daya tilo da ta fi kare muradunta tare da alwashin ƙwace mulki a hannun APC a 2027.

ADVERTISEMENT
  • 2027: Masu Neman Takarar Shugaban Kasa A PDP Sun Kara Matsa Kaimi Bayan Ficewar Atiku
  • Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC

Mark da Lawal sun bayyana wannan a ranar Asabar a lokacin taron gamayyar ƙungiyar tuntuɓa kan harkokin siyasa ta arewa karo na uku da aka gudanar a Abuja.

da yake mayar da martini kan batun, daraktan Yada Labarai na APC, Bala Ibrahim, ya yi iƙirarin cewa jam’iyyar mai mulki tana da goyon baya a duk faɗin ƙasar nan, ciki har da arewacin Nijeriya, inda ya bayyana cewa muradin ƴan Nijeriya na samun kariya ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

LABARAI MASU NASABA

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

A yanzu haka dai ratotannin sun tabbatar da cewa APC da ADC suna gogayya wajen neman samun goyon bayan mutanen arewa kafin babban zaɓen 2027 ya ƙariso.

A ranar 1 ga Yuli, manyan ƴan adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi da dan takarar shugaban ƙasa a APC a 2023, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun gabatar da ADC a matsayin hadakar jam’iyyar adawa domin ƙalubalantar Tinubu a 2027.

Shugabannin ADC sun ci gaba da yin ƙoƙari don samun goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya da sauran yankuna tun bayan buɗe jam’iyyar.

A taron, Mark ya buƙaci shugabannin arewacin Nijeriya da su daina dabi’ar zargi da kuma amincewa na suna da alhakkin ƙalubalen da yankin ke fuskanta.

Ya ce, “Wannan wata dama ce da kuma girmamawa kasancewa a gabanku yau don magana kan batun halin da muke ciki a yanzu da kuma sauya makomarmu. Ina kira a gare ku mu yi gaggawar samun haɗin kai da ƙarfafa dangantaka a matsayin hanyar magance ƙalubalen da yankinmu ke fuskanta. 

“Arewacin da muka sani ya kasance wata ƙasa ce mai ɗimbin tarihi da albarkatun ma’adinai da ƙasa noma da al’adu masu yawa da kuma ƙarfin tasiri.

“ɗuk da wadannan albarkatu, muna fuskantar ƙalubale masu yawa da suka hada da rashin tsaro da talauci da rikice-rikicen ƙabilanci da addinai da rarrabuwar kai a siyasa da matsalolin zamantakewar da na tattalin arziki. Wadannan ƙalubale ba su faru a dare daya ba kuma ba za su kau ba har sai mun hada kai wajen daukar matakin da ya dace.

“ɗole ne mu yarda da cewa mu ne masu gina matsalolinmu, dole ne mu daina zargin kawunanmu idan muna son samun mafita ɗorewar yankinmu.”

Tsohon shugaban majalisar dattawa ya ƙara bayyana cewa rarrabuwar kawuna ta hana wa arewacin ƙasar nan ci gaba, yayin da halin ko-in-kula da rashin daukan mataki ya ƙara zurfafa rarrabuwar da ta riga ta wanzu.

“ƙalubalen da ke fuskantar arewacin Nijeriya suna da alaƙa da juna. Rashin tsaro yana janyo ficewar masu zuba jari, wanda hakan ke ƙara tsananta talauci. Talauci yana jawo aikata muyagun laifuka. ƙabilanci na rage ƙarfin haɗin kanmu wajen neman kyakkyawan shugabanci. Rugujewar harkokin siyasa na tabbatar da cewa ba za a samu ingantaccen ci gaba a yankinmu. Wannan ba arewar da muka gada ba ne,” in ji ADC.

ɗon dawo da martaban yanki, Mark ya jaddada cewa akwai buƙatar matanen arewa su sake tunani da yin Nazari wajen daukan matakan da suka dace.

Ya kira ga dukkan mutanen arewa su dauki wannan a matsayin babban nauyi na haɓaka haɗin kai wajen inganta yankin maimakon zama a rarrabe.

A nasa ɓangaren, Lawal ya bayyana cewa gamayyyar ƙungiyar tuntuɓa kan harkokin siyasa ta arewa ta amince da ADC a matsayin jam’iyyar da ta iya tunkarar APC a zaɓen 2027.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ce wakilai daga dukkanin jihohin arewa 19 sun cimma yarjejeniya cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta wani yuƙuri wajen magance matsalolin yankin. 

Ya ce masu ruwa da tsaki daga arewacin ƙasar nan sun amince su tashi tsaye su yada saƙonsu wajen samn haɗin kan mutane da cimma matsaya kan zaɓe mai zuwa. 

A martaninsa, daraktan yada labarai na APC ya ce jam’iyyar mai mulki ba ta damu da abin da ake kira da suna hadakar jam’iyya ba.

Ibrahim ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na jagorantar gwamnati mai cike da samun goyon bayan dukkan mutanen Nijeriya.

Ya ce, “Jam’iyarmu ta APC, tana samun goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya da kuma dukkan sauyan yankunan Nijeriya gaba daya, sai dai wadanda ba su gamsu ba da suka kafa jam’iyyar ADC a yanzu.”

Ya bayyana cewa APC ta jajirce wajen sabunta fata ga ƴan Nijeriya kuma yana nuna tabbacin cewa jam’iyyar za ta ƙara samun nasara a 2027.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC
Manyan Labarai

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa
Siyasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025
Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP
Siyasa

Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

November 12, 2025
Next Post
Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025
Kwankwaso

NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji

November 16, 2025
Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

November 16, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

November 15, 2025
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025
Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa

Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi

November 15, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

November 15, 2025
Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025
Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.