• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna

by Yusuf Shuaibu
7 months ago
Siyasa

Yayin da har yanzu ya rage shekaru biyu a gudanar da zaben shugaban kasa a 2027, ‘yan siyasa na ci gaba da gudanar da dubarun siyasa ciki har da tarurruka da kuma ziyarar gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda yanzu ake gani a matsayin sabuwar amarya a fagen siyasar Nijeriya.

Duk da yake gudanar da tarurrukan sun dade suna cikin dubarun siyasar Nijeriya, yanayin da ‘yan siyasa daga jam’iyyar APC mai mulki da ‘yan adawa ke yin safa da marwa zuwa gidan tsohon shugaban kasa a Kaduna don tattaunawar sirri da daukar hotuna tare da shi. Wannan ya faru ne saboda yadda Buhari ya yi watsi da siyasa da kuma karkatar da ‘yan siyasa daga inda suka saba.

  • Manchester Ta Kai Zagayen Semi Final A Europa Bayan Doke Lyon
  • Bai Wa Shanu Guba: Sojoji Sun Shiga Tsakani Domin Dakile Yunkurin Ramuwar Gayya A Filato

Wadannan ziyarar ta kwanan nan ga Buhari, duk da cewa galibi ana alakan ta shi ga neman mulki, wanda ‘yan siyasa suka rike a matsayin wani dubarun neman iko.

Har zuwa yanzu ana ganin Buhari ya rabu da siyasar bayan ya bar ofis, Buhari a hankali ya zama mutum mai tallata ‘yan siyasa, inda bangarori daban-daban suna neman goyon bayansa da albarkarsa. Sauya sheka tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa jam’iyyar SDP ya kara tsananta jita-jita game da ra’ayin siyasar tsohon shugaban a yanzu.

Don haka, lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda kwanan nan ya sanar da kwancen hadin gwiwar jam’iyyun adawa don hambarar da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya jagoranci gungun manyan ‘yan siyasa ciki har da El-Rufai da tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal zuwa gidan Buhari a Kaduna, masu sharhi da yawa sun fassara hakan a matsayin wata magana a fili ga tsohon shugaban kasar. An bayyana cewa makusantarsa ‘yan asalin jam’iyyar CPC suna shirin ficewa daga APC.

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

Duk da cewa Atiku ya dage yayin tattaunawar da ya yi da manema labarai bayan ziyarar cewa ganawar ba ta batun siyasa ba ne, amma jawabin El-Rufai ya nuna karara akwai siyasa a cikin ganawar.

Bayan ziyarar ‘yan adawa kwanaki kadan da na gwamnonin APC, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya isa gidan Buhari sa’o’i kadan bayan tawagar Atiku, wanda ya kara tsananta siyasa. Ya kuma ba da tabbaci ga ra’ayin cewa shugabannin jam’iyyar APC sun damu da siyasar tsohon shugaban kasar.

Masu lura da al’amura siyasa sun bayyana cewa kalaman da Ganduje ya yi bayan ganawar, ya tabbatar da cewa APC na yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa Buhari ya kasance tare da jam’iyya mai mulki. Wannan matakin na zuwa ne yayin da kawancen ‘yan adawa ke samun karfi, musamman a yayin da ake zaman doya da manja tsakanin gwamnatin Tinubu da ‘yan arewa.

Idan za a iya tunawa a lokacin watan Ramadan, dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya kai ziyarar girmamawa ga Buhari da sauran shugabannin siyasar arewa a lokacin rangadin da ya kai yankin.

Mai sharhi kan harkokin siyasa, Shamsudeen Ibrahim ya bayyana ziyarar da kwamitin gudanarwa na APC da Ganduje ke jagoranta suka kai ga Buhari a matsayin tsoron rasa riko, tsoron rasa arewa, da tsoron rarrabuwar kawuna. Ba ziyarar ‘yan’uwantaka ba ne. Ziyarar neman tsira ne.

Mai sharhi kan harkokin jama’a, Dakta Saidu Dukawa, ya kara da cewa ziyarar ta zama wata manuniya ga jama’a cewa shirye-shiryen zaben 2027.

Dukawa, ya kasance babban malami a jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ya ce, “A bayana, ana yin irin wannan ziyarar ga tsoffin shugabannin kasa da suka hada da Obasanjo da Jonathan don cimma manufofin siyasa, amma yanzu lamarin ya zama tarihi. “

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Tambarin Dimokuradiyya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Next Post
An Gudanar Da Bikin Musanyar Al’Adun Al’ummun Sin Da Cambodia A Phnom Penh

An Gudanar Da Bikin Musanyar Al’Adun Al’ummun Sin Da Cambodia A Phnom Penh

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

November 1, 2025
Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

November 1, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.