Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi kira ga majalisar kasa ta gaggauta aiki a kan kudurorin sake fasalin tsarin zaben Nijeriya domin kauce wa kawo tsaiko a shirye-shiryen gudanar da zaben 2027.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wannan kira a a Abuja yayin da yake karbar bakoncin tawagar Kungiyar Tarayya Turai (EU) masu saka ido kan zabe karkashin jagorancin, Mista Barry Andrews.
- Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
- Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi
Yakubu, wanda ke kusantar karewar wa’adinsa na karshe a wa’adi na biyu kan mukamin shugaban INEC, ya ce amincewa da dudurorin sake fasalin tsarin zabe da wuri zai tabbatar da samun sauki wajen gudanar da zaben 2027.
“Muna kira ga majalisar kasa da ta yi la’akari da shirin gyaran tsarin kudurorin zabe cikin gaggawa. Amincewa da dokar cikin lokaci yana da muhimmanci ga shirinmu na gudanar da zabe a 2027.
“Rashin tabbas game da tsarin doka na zabe na iya kawo matsaloli masu yawa ga ayyukan hukumar INEC yayin da lokacin zabe ke karatowa,” in ji shi.
Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumarsa ta aiwatar da shawarwarin da aka mika mata kai tsaye a rahoton EU na zaben 2023.
“An dauki mataki kan wasu bangarori na shawarwarin da ake bukatar hukumar ta aiwatar da su. Haka kuma, ana daukar mataki kan shawarwarin da suka shafi fannoni da dama wadanda ake bukatar hadin gwiwa tsakanin INEC da sauran hukumomi da masu ruwa da tsaki yayin da ake jiran kammala bitar sake fasalin shari’a da majalisar kasa ke yi,” in ji shi.
A nasa kalamun, Mista Barry Andrews ya yaba da muhimmancin Nijeriya a dimokuradiyyar duniya, yana bayyana aikin EU na 2023 a matsayin daya daga cikin manyan aikace-aikace ga dukkan kasashen duniya.
“Aikinmu shi ne taimakawa wajen samun ci gaban na aiwatar da shawarwarin daga zabukan shekarar 2023. Mun lura da manyan ci gaba a wasu fannoni da dama, ko da yake wasu kalubale suna nan yadda suke, musamman wadanda suka shafi shari’a da gudanarwa da tsarin gyara fasalin kundin tsarin mulki,” in ji shi.