• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Masu Shirin Yin Kawance Na Duba Yiwuwar Zakulo Dan Takarar Da Zai Yi Wa’adi Daya

byYusuf Shuaibu
6 months ago
Kawance

A yayin da tattaunawar kawancen ‘yan adawa ke ci gaba da gudana domin kalubalantar Shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027, masu ruwa da tsaki a yankin arewa na kara matsa kaimi wajen duba yiwuwar yarjejeniyar zakulo dan takarar shugaban kasa da zai yi wa’adi daya a yankin kudu.

Wata majiya mai ruwa da tsaki a tattaunawar gamayyar jam’iyyun adawa wadda ta bukaci a sakaya sunanta saboda rashin ba da izinin yin magana a kan lamarin, ta shaida wa manema labarai cewa masu ruwa da tsaki a yankin arewa na neman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ka da ya tsaya takara.

  • Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
  • Sin Ta Bayyana Wani Shiri Na Bunkasa Kiwon Lafiya

Majiyar ta kara da cewa mafi yawan masu ruwa da tsaki na ganin cewa idan dukkanin shugabannin kawancen suka hada kai tare da mara wa dan takara a yankin kudu baya, za su iya kayar da Shugaba Tinubu.

A ranar 20 ga Maris, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku da Peter Obi na jam’iyyar LP da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun sanar da kafa kawancen da ke da nufin kwace mulki a wurin Shugaba Tinubu a shekarar 2027.

Ana ci gaba da tafka muhawara kan ko ya kamata jam’iyyun adawa su hada kai don kalubalantar gwamnatin Shugaba Tinubu’, inda ‘yan siyasa daban-daban ke musayar ra’ayoyi daban-daban.

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu

Dage Zaben Shugabannin PDP Na Jihohi Ya Kara Ruruta Wutar Rikici A Jam’iyyar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kasance mai fafutukar tabbatar da hadin kan ‘yan adawa, yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen kayar da Tinubu a zaben 2027.

A ranar 8 ga watan Maris ne ya bayyana kokarinsa na hada kan ‘yan adawa da kafa kawancen korar jam’iyyar APC.

Bayan sauya shekar El-Rufa’i daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PSP a ranar 10 ga watan Maris, tattaunawar da aka yi tsakanin shugabannin ‘yan adawa ta samu gagarumar nasara.

Atiku da sauran ‘yan adawa sun bayyana cewa taron na ranar 20 ga watan Maris ya nuna kaddamar da kawancen a hukumance.

A baya dai an ruwaito a ranar 23 ga watan Maris cewa ana jinkirin tattaunawa kawance tsakanin shugabannin siyasa saboda burin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku na tsayawa takara da kuma rikicin shiyya.

Majiya ta bayyana cewa masu ruwa da tsaki suna da zabi da yawa don magance duk abubuwan da lamarin ya kunsa.

Majiyar ta ce, “Akwai batutuwa da dama a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki a tattaunawar kawancen, inda batun arewa da kudu shi ne babban abin da ya fi daukar hankali.

“Yawancinmu mun fahimci cewa idan muka tsayar da dan takarar kudu wanda ya cancanta kuma mai gaskiya, kayar da Shugaba Tinubu zai fi sauki. Don haka da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki, musamman na arewa, suna kira ga Atiku a kan kar ya tsaya takara, ya bai wa kawancen damar mara wa dan takarar kudancin kasar nan baya da zai yi wa’adi daya idan aka zabe shi.

“A hakika, wasu daga cikin wadannan masu ruwa da tsaki sun dagewa cewa duk wani dan takara daga kudu da za su mara masa baya dole ne ya amince da alkawarin wa’adi daya.

“Wadannan al’amura sun kunno kai, amma mun himmatu wajen magance su a lokacin da suka taso da kuma daukar nauyin ‘yan Nijeriya da dama da suke fuskantar rashin iya shugabancin APC. Manufarmu ita ce tabbatar da ingantaccen tsari wanda ke wakiltar muradun jama’a da karfafa hadin kan kawancen.”

A lokacin da aka yi yunkurin jin ta bakinsa, sakataren kungiyar hadin kan jam’iyyun siyasa ta kasa, Peter Ahmeh, ya tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki na yin la’akari da shawarar fitar da dan takara daga kudancin kasar nan tare rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta wa’adi guda.

Ahmeh ya bayyana cewa, kawancen ‘yan adawar da ke adawa da Shugaba Tinubu sun fi wadanda tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya fuskanta a shekarar 2014.

Ya ce, “Rattaba hannu kan yarjejeniyar wa’adi guda da dan takara daga kudu na daga cikin abin da ke kan teburin tattauwar, amma har yanzu ba a kammala hakan ba. Bai kai ga karshe ba.

“Peter Obi da wasu masu neman takar shugaban kasa a kudu suka cikin wannan tattaunawa. Na yi imanin cewa za a cimma matsaya nan da ‘yan makonni masu zuwa.

“Akwai zabi masu yawa a kan tebur. Mutane suna kawo sauye-sauye daban-daban, amma gaskiya har yanzu ba a cimma matsaya ba. Da zaran an cimma matsaya kan wannan yarjejeniyar, za mu sanar da al’umma.

“A bayyane yake cewa ‘yan Nijeriya da yawa sun fahimci cewa wannan gwamnati tana cutar da mu fiye da alherinta. Don haka, ‘yan Nijeriya da dama ne ke shiga kawancen. Akwai ‘yan adawa da ke adawa da wannan gwamnati fiye da yadda ake yi wa tsohon shugaban kasar Jonathan a shekarar 2014.

“Don haka, ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki na kkwancen da sauran shugabannin ‘yan adawa da su ci gaba da wannan alkawari domin mu hada kai don ceto kasar nan daga gazawar APC.”

Lokacin da aka tuntubi tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku kai ji ta bakinsa kan wannan kawance, ya yi gargadi game da rade-radin da ka iya kawo cikas ga tattaunawar kawancen.

Atiku, ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya jaddada cewa duk wata yarjejeniya da aka kulla za ta kasance wajibi ga dukkan bangarorin da abin ya shafa.

Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tuntubar juna a fadin kasar nan kan wannan kawancen ‘yan adawa.

Sai dai kuma shugaban matasan jam’iyyar PDP, Timothy Osadolor, ya soki yunkurin da ake yi na dan kudu ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta wa’adi daya, yana mai cewa lamarin ba mai yiwuwa ba ne.

Da yake mayar da martani kan kawancen ‘yan adawa, Daraktan Yada Labarai na APC, Bala Ibrahim, ya yi watsi da yunkurin kawancen, inda ya bayyana cewa farin jinin jam’iyya mai mulki a tsakanin ‘yan Nijeriya na karuwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi
Tambarin Dimokuradiyya

ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu

October 3, 2025
Dage Zaben Shugabannin PDP Na Jihohi Ya Kara Ruruta Wutar Rikici A Jam’iyyar
Tambarin Dimokuradiyya

Dage Zaben Shugabannin PDP Na Jihohi Ya Kara Ruruta Wutar Rikici A Jam’iyyar

October 3, 2025
Yadda Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Daya – Jonathan
Tambarin Dimokuradiyya

Lalacewar Tsarin Zabe Babbar Barazana Ce Ga Dorewar Dimokuradiyyar Afirka — Jonathan

September 27, 2025
Next Post
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Har Yanzu Shugabanci NNPP Na Hannunmu – Tsagin Kwankwaso

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version