A ranar Lahadi, Arsenal ta yi nasara kan Manchester United da ci 1-0 a wasan makon farko na sabon kakar gasar Firimiya da aka buga a filin Old Trafford.
Ɗan wasan bayan Arsenal, Riccardo Calafiori, ne ya zura ƙwallon a minti na 13, yayin da United ta fara wasan da sabbin ‘yan wasanta Bryan Mbeumo da Matheus Cunha.
- Gwamna Bala Ya Yi Alhinin Rasuwar Tsohon Gwamnan Bauchi A Zamanin Mulkin Soja
- Daje Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Neja
Sakamakon wasan ya saukar da Manchester United zuwa matsayi na 15, yayin da Arsenal ta hau kan teburin gasar zuwa matsayi na 6.
Kocin United, Ruben Amorim, ya bayyana wasan da cewa ya kasance mai wahala ga ƴan wasansa, amma ya jaddada cewa wasan gaba zai bambanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp