Kungiyar Malaman makrantun fasaha ta kasa ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwana 21 saboda ta samu damar daukar mataki akan wadansu matsalolin da suke damuwar lamarin ilimin daya shafi fasaha.
Kungiyar ta kan cewa idan kuma aka ki daukar matakin da ya kamata hakan zai sa su, su daukji matakin da zai kawo tsayawar harkokin koyar da dalibai na makarantun da ke, a kasa baki daya.
- Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama
- JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa
Shugaban kungiyar na kasa ASUP, Komrade Shammah Kpanja shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja ranar Jumma’a inda ya yi kira da ma’aikatar ilimi ta kasa da ba tare da bata lokaci ba, ta aika ita dokar ta bukatunsu zuwa majalisa kasa.
Kpanja hakanan ma dangane da wadanda ake tuntuba kan wasu harkoki da suke waje dangane da amincewa da abubuwan na makarantun fasahar,inda ya tambayi wane oirin ilimi suke da shi, da kuma irin gogewar da su ‘yan kwangilar suke da ita.
Daga ciukin bukatun nasu akwai wadanda suka hada da kafa hukumar da zataika lura da lamurran makarantun fasaha wadanda suka yi kama dana Jami’oi da kuma Kwalejojin horon Malamaina ilimi.
ASUP ta nuna rashin jin dadinta akan abinda ta kira bata lokaci na samar da doka da ‘yn majalisa za su yi, domin asamu kafuwar ita hukumar.
Bugu da kari kuma kungiyar ta kara yin magana kan abinda ya dade yana ci mata Tuwo a kwarya wato yadda ake nuna fifiko tsakanin wadanda suka kammala Jami’oi da kuma makarantun fasaha, ko kuma masu Digiri da Babbar difiloma ta kasa.
ASUP ta ce ci gaba da ake yi na nuna bambancin da ake tsakanin masu shaidar kammala karatu na Digiri da Babbar Difiloma ta kasa, lamarin ba kawo ci gaba yake ba ta bangaren na fasaha.
Bugu da kari kuma ya bayyana irin wahalar da Malaman makarantun ke fuskanta idan aka yi la’akari da matsalar tattalin arziki da su Malman suke fuskanta, inda ya dora alhakin lamarin kan gwamnatin tarayya wajen tafiyar Hawainiyar da take yi kan wajen aiwatar da lamurran da suka hannun a yarjejeniyar shekarar 2010 tsakanin gwmnatin tarayya da kungiuyar ta ASUP.
Kamar yadda ya ce abubuwan sun hada da biyan wani alawus da Malamai, da kuma aiwatarwa gaba daya kashi 25 zuwa35 na tsarin albashi, lamarin da ASUP ta ce har yanzu ba a kaiga aiwatar da hakan ba, kamar yadda abin yake a kasafin kudin Nijeriya.
Kungiyar ta bada bayanin lamarin daya shafi cire alawus- alawaus daga kasafin kudin gwamnatin tarayya da kuma abinda ta kira rashin bin diddikin lamarin na wasu hukumomin da suke da fada aji kan abin, da suka hada da hukumar kula da lamurran da suka shafi albashi ta kasa da kuma ma’aikatar ilimi ta tarayya.
Kungiyar ta ASUP,ta ce abin ma yafi muni, a makarantun fasaha da suke karkashin gwamnatocin Jihohi,inda har yanzu akwai Jihohi da yawa da har yanzu basu amince da far amfani da biyan mafi karancin albashi na Naira 70,000 wanda har zuwa yanzu abin ya zama karfen kafa ga wasu Jihohi fara amincewa su biyan irin Malaman kungiyar tasu.
Bugu da kari kungiyar ta nuna rashin jin dadinta kan abinda ta kira irin bata lokacin da ke yi wajen yadda za a saki kasha na biyu na abinda aka amince da shi na NEEDS wasu kudaden tallafi ,ta kuma kara da cewar han yanzu ma ba ayi a sake duba yadda lamarin yake ban a zango na farko.
ASUP, har ila yau ta bayyana yadda take jin abin a zuciyarta, wato yadda gwamnatin tarayya take nuna halin ko in kula na yadda nagarta irin makarantun da ke son su yi koyi da su, duk da hakan ya yi kira da a rika yin abin cikin adalci, da kuma duk wani abinda da ana yi lamurran cikin gaskiya wajen yin abubuwan da su da nuna fasahar tsantsarta, da take wata hanya ce da take tabbatar da,ana tafiyar ilimi mai nagarta.
Kungiyar ta nuna amfanin sake tattauna magana kan yarjejeniyar ASUP da gwamnatin tarayya ta shekarar, ba ma kamar maganganun biyan kudaden ariyas, watanni 15 na CONTISS da kuma ariyas na karin girma daga shekarar 2014 zuwa 2019.
Kungiyar tana yi ma lamarin kallon rashin wani ci gaban da aka samu dangane da matsalolin da suka dame ta, don haka ne su Shugabannin kungiyar kasa na suka yanke shawarar ba gwamnatin tarayy wa’adin kwana 21.
“Idan kuma har kwanaki 21 suka kare babu wani kwakkwaran matakin da aka dauka mai gamsarwa daga gwamnatin tarayyar, babu wani abinda kungiyar za ta yi illa ta daina koyarwa daga makarantun fasaha na gwamnati a fadin kasa baki daya, idan har hakan ta kasance kamar yadda suka kara jan kunne”.
Matsalolin Samun Guraben Karatu A Jami’oi Ke Sa Dalibai Karanta Kwas Din Da Basu So
Ko wace shekara dubban dalibai daga Nijeriya wadanda suke sa ran tafiya karatu zauwa Jami’oi sun nemi bukatar hakan tare fatan kwasa- kwasan da suke son karantawa, saboda irin ayyukan da suke son yi a gaba su samu cimma burinsu. Sai dai kuma kash! Yawancinsu idan takardun amincewar sun same su, sai, a basu wasu kwasa- kwsan da basu nema ba, ba kuma su bukatarsu.
Akwai karancin guraben karatu a irin kwasa- kwasan da su daliban suke son yi hakan ya biyo bayan kowane sashe ko bangare da akwai kason da ake ware ma shi, inda daga karshe su daliban ana basu kwasa- kwasan da ba zabinsu ba, abinda basu da zabi sai dai su amince da hakan.
Maganar gaskiya ita ce akwai wasu dalibai masu sha’war su samu cika burinsu na karanta kwas din da ya fi kwanta masu a zuciya, cikin dan kankanen lokaci an basu kwas din da su suke bukata ba, sai lamarin ya kasance babu yadda ya iya sai dai hakuri har zuwa karshen rayuwasu.
Lokacin da Mercy Orji ta amshi takardar samun gurbin karatu zuwa Jami’a , ta kalli kanta ne sanye da wata farar Kaftan irin ta dakin gwaje- gwaje, tana kokarin ceto rayuwar marasa lafiya a dakin Tiyata. Amma maimakon su bata Medicine wato abinda ya shafi Likita,sai Jami’ar ta bata dama ta karanta ko kwas din Botany.
Ta ce “Na yi kuka wannan rana. Saboda lokacin da nake makarantar Sakandare ni ce a gaba a darussan, Biology da Chemistry. Duk da yake abin ina yi ma shi kallon kaddara babu yadda zan yi. Sai dai shi samun damar gurbin karatun nan a bangaren Likita tamakar kamar mutum ya ciu cacar lottery ce anan, sai kawai suka kai ni wani sashe. Ga shi ni kuma ban ma san, abinda wanda ya karanta Botany yake yi ba, bayan ya kammala karatun, maganar gaskiya.
Labarin nata bai bambanata da na saura ba.A Nijeriya dubban dalibai suna neman a basu damar karanta wani kwas ne ko darasi,amma daga karshe sai a basu wani abin da ya sha bamban da wanda suke bukata irin hakan ne ke sa su sauya irin yadda suka so tafiyar da rayuwarsu a lamarin daya shafi karatu , da kuma aikin da suke son yi bayan sun kammala. Saboda samun damar gurbin karatu yana da wuya,yawanci suna amincewa da irin kwas din da aka basu.
Peter Omohashi yana sha’awar karanta lamarin daya shafi Lauya ne amma maimakon hkan sai aka bashi Philosophy. Sai ya ce lokacin“Lokacin da na ga ‘Philosophy’,a takardar bani damar gurbin karatu, na yi tunanin ko an yi kuskure ne.Amma sai Iyaye har sun baya kudin amincewa da zan yi karatun tun ma kafin in fara wata maganar abinda nake so ba shi aka bani ba. Sun ce mani na tafi makaranta ka wai, za’a san abinda za ayi a gaba.’ya ce ’ga shi yanzu abin har ya kai shekara uku yanzu.”
Gare shi babbar matsala ita ce, ya bayyanawa mutane dalilin da yasa bai samu damar karanta abinda yake bukatar yi ba. “Kowa yana fada mani, ‘Me yasa ba zaka iya canza kwas din ba?’Sai dai kuma maganar canzawa wata babbar matsala ce gare shi, sanin shi sai idan mutum yana da wata hanya ko kuma yana da kudi. Sai kawai karanta Plato da Aristotle nake yi, duk kuwa da yake zuciyata har yanzu tana cikin Kotu ne.”
Ita kuma Winifred Onema abinda ya tada mata hankali an bata kwas din, abinda da ya shafi aikin gona maimakon lamarin daya shafi karatun koyon aikin Jarida.“Ita babbar sha’warta ita ce ta kasance gaban Talabijin tana karanta labaru ko kuma jagorantar wani shiri,”sai ta ce maimakon hakan. ”,Gani nan ina koyon yadda zan yi magana da manoma dangane da Takin zamani”.
“Abin ya zame mani kamar wani ya yaga mani yadda nake son rayuwar karatu ne zuwa aiki ta kasance ya mika mani wata.” Ta ce da farko ta yi tunanin ko zata bar karatun ne.Amma da yake ‘yar karamar sana’ar da mahaifinta yake yi tana neman salwancewa , don haka sai ta ga babban abinda ya fi shi ne yin hakuri ta yi karatun.“ A Nijeriya da zarar ka rasa damar zuwa Jami’a, za’a dauki shekaru kafin ka kai ga samun wata damar.Shi yasa na yi hakuri amma kullun ina ganin ni tamkar ai ina yin kwas din daya kasance abinda wani ne yake so.”
Sharon Itodo ta san irin bacin ran da ta shiga sosai.Ta so ta karanta lamarin da ya shafi Komfuta ne amma sai aka bata kwas din da ya shafi sha’anin dabbobi. “Da farko na ki amincewa,” kamar yadda ta ce. “Amma bayan shekara tana zaune a gida gas hi kuma mahaifinta ya biya mata kudi ta sake rubuta JAMB har karo na biyu,kawai sai ta yi hakuri ta rungumi kaddara. Ta ce sun kasha kudade masu yawa domin ta samu kwas din da take so.” Yanzu tana shekararta ta karshe, abubuwa sun dame ta.“Har yanzu tana son tana sha’awar lamarin fasaha, tana kuma koyon wasu tsare tsare ne na ta kafar sadarwar zamani daga farko, za ta fara daga yadda abin yake tun farko.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp