Shafin TASKIRA shafi ne, da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi magana ne, game da abin da ya shafi auren jari madadin auren mutunci da wasu mazan ke yi a yanzu.
Wanda dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko me za a ce game da hakan?, fadi amfani ko rashin amfanin yin hakan, Ko akwai wasu matsaloli da hakan zai iya haifar wa?”.
- 2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe
- Za A Yi Ruwan Sama Na Kwanaki 3 A Jere A Wasu Jihohin Nijeriya – NiMet
Ga dai bayanan nasu kamar haka;
Sunana Princess Fatima Mazadu, daga Gomben Nijeriya:
Kwadayi da zubda mutunci, wanda kuma ba zai taba debuwa ba. Dan ba daraja sam wallahi, ,ga raini baka isa ka sata abu ba, sai ta ga dama. Tunda cikin hutu ka sameta, ka zamo mijin Hajiya ba dai abika ba, sai dai ka bi. Ni kam a wurina bai da fa’ida bare tsari, ban da zubda daraja da kima na da namiji da aka san shi da taka gida da daraja a fannin aure. Rashin amfani kam ai ya fi amfaninsa, kawai amfaninsa za ka ci mai kyau ne wanda ba zai bi jikinka ba. Saboda ba cikin natsuwa za ka ci shi ba da kwanciyar hankali, saboda gori da raini. Matsala ta farko raini, na biyu zubda mutunci da darajawa, na uku kuma iyayenka kansu ba za a girmamasu ba. Kowa ya auri daidai abun da ya san zai masa biyayya, kuma ya kare masa mutuncinsa, sannan ya daga darajar da kimasa, ba wai ka auri mace tana maka kallon kaskanci ba. Allah ya tsare mu da sharrin son zuciya.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano LGA Jihar Kano:
Wasu yanayin halin da ake ciki ne a wannan kasar tamu, wasu kuma mutuwar zuciya ne. Sabida sun san cewa mafiya yawan matan, ko iyayen matan ne za su na daukar nauyinsu. Gaskiya rashin amfanin irin wannan auren ya fi yawa, duba da za ki ga a mafiya lokuta da zarar mazan sun cimma wani buri nasu sai auren ya mutu. Ko kuma ki ga wasu matan su zo suna wulakanta mazajen, sabida sun san dama don dukiyar su da kudinsu mazan suka aure su. To, su ma matan da zarar bukatarsu ta biya, sai wulakanci ya biyo baya a karshema auren ya mutu. Ana samun matsalar raina darajar auren kansa, da raina juna idan tafiya tayi tafiya. Shawarata a nan ita ce komai za mu yi mu yi shi domin Allah, da zuciya daya ba don cikar wani buri ba. Duk da addininmu ya yarda ka auri mace don dukiyarta to ammafa ba ta irin wannan sigar ba, ayi aure da niyya aikata sunnar annabi abin kuma da ya biyo baya ya zamana ribar kafa ne Allah ya sa mu dace amin.
Sunana Hadiza Ibrahim Ɗ. Auta Kaura-Namoda Jihar Zamfara:
Auren Jari: Maza da yawa a wannan lokacin sun zama ci-ma-kwance. Matan da ke cikin gidansu ma ganin suke yi hidimarsu ta zamo musu wata babbar lalura. Hakan ya sa suke bar wa mata jan ragamar gidan yadda suke so, suna yin watsi da darajar auren saboda ganin girman ciyarwa ko hidimar gidan ta yau da kullum. Ko da akwai amfani a auren jari rashin yin sa ya fi yin sa amfani matukar namiji yana son ya zamo mijin matar ya zamo matar gida. Don wani lokaci shi yake zama mata mace kuma ta koma mijin idan aka yi rashin dacen haduwa da wadda ta waye da zaman duniya kuma ta fi shi sanin ‘yancin kanta. Akwai tarin matsalolin da ke wanzuwa a cikin irin wannan auren. Musamman idan aka biyo bangaren ‘yan’uwansa da shi kansa. Saboda idan har gidan na matar ne; to shi danginsa ba su isa su yi wa matar tutiya da gidan ba, ko kuma nuna isa ko sakewa a gidan ko da sun samu tarba mai kyau daga matar gidan. Saboda suna dar-dar a kan kada su yi mata ba daidai ba ta kora su ko ta fada musu wata magana mara dadi, watakila ma gori ya biyo bayan hakan. Babba shawarar da zan bayar a kan haka ita ce; ko da namiji zai yi auren jarin, ya tabbatar shi ma yana da abin hannunsa bai zamo malalaci ba. Ko babu komai macen ba ta isa ta juya shi ba, sannan kuma ba ta isa ta yi masa gorin arzikinta ya zo ci ba.
Sunana Abubakar Usman Malam Madori A Jihar Jigawa:
Auren jari maimakon auren mutunci na soyyayyar tsakani da Allah, yana nuna fifikon dukiya fiye da kyawawan dabi’u, wanda hakan na iya rushe ginshikin aure da aka gina shi, akan abun duniya da kwadayi. Amfani amfanin yin hakan. Akwai amfani, domin zai iya kawo saukin rayuwa ta hanyar arziki idan an yi dace. Rashin amfaninsa, rashin samun soyayya, ta kwarai da rashin girmama juna, domin tun fari an dora auren a wani mizani na soyayyar bogi, sannan akwai rashin girmamawa da fahimta, wanda ka iya janyo rabuwar aure da rashin kwanciyar hankali. Matsalolin da hakan zai iya haifarwa; Rashin zaman lafiya wulakanci da kuma raini daga iyayen gida, yiwuwar cin zarafi ko karancin kulawa a cikin aure. Shawara ga masu aikata hakan, a duba nagarta da tarbiyya fiye da dukiya. Aure na bukatar soyayya da jituwa, dan samun zuri’a nagari wacce za a yi alfahari da ita nan gaba. Ba kallon abun ta fuskar kudi ko wata biyan bukatar kai kadai ba.
Sunana Hafsat Sa’eed daga Neja:
Abin da ya sa maza suka zabi yin auren jari, ba komai bane face halin da ake ciki na a yanzu. Babu ne ya sa suka zabi su yi auren da suke ganin, za su samu hutu da salama a ciki. Yana da amfani yin hakan, musamman ma ga mutanen da suke cikin wani yanayi ba su da kudin da za su iya yin auren. Ba wani matsaloli da zai haifar face kai namiji ba kada katabus a gidan face yadda aka yi da kai.
Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:
Tabbas wasu mazan sukan zabi auren jari akan auren mutunci, amma hakan ba abin da ya dace bane. Domin auren mutunci, ya fi auren jari. Daga rashin amfanin auren jari shi ne kudin ai ba su da tabbas za su iya karewa, idan suka kare ka ga auren ma na iya karewa. Haka nan mutun na iya fuskantar wulakanci da kaskanci daga gurin matar da dai sauransu. Matsaloli da yawa daga cikin abin da na fada a baya. Sannan zai zama ba shi da iko da gidansa bai isa ya sa ko ya hana ba, haka kuma idan sun sami zuri’a za su fi ganin darajar uwar su fiye da tasa. Shawara dai ita ce mutane mu rage kwadayin duniya, mu duba abin da zai zamar mafi kyau mu da zuri’armu bakidaya.
Sunana Asiya Adamu Jihar Kano:
A gaskiya dai wasu mazan na yin auren jarin ne, ba dan komai ba sai dan su ci kudin ita matar, su kuma samu ninkin riba a kan fukiyar da su ke dashi. Kwata-kwata hakan ba shi da wani alfanu, saboda mutumci ya fi komai a rayuwa akan dukiya. Tabbas a nawa ganin akwai matsaloli, kamar idan auren jari ne, kowa a cikin ma’auratan zaman kanshi yake, babu mai sawa da hanawa. Gaskiya masu yin hakan, su sani cewa hakan ba abun da ya dace bane, kuma su sani hakan ba zai haifar musu da da mai ido ba.
Sunana Ibrahim Garba Bizi Jihar Yobe:
Auren kudi kawai, ba tare da la’akari da halayya da mutunci ba, yana nuna son zuciya da rashin hangen nesa. Rashin amfani; zai iya haifar da rayuwa mara farinciki, rashin girmamawa da daukaka. Matsaloli; Rashin kwanciyar hankali, Izzar miji ta rushe, matar na iya raina miji, zai iya zama aure mai cike da yaji da cin mutunci. Shawara; A duba mutunci, tarbiyya da fahimta, kafin jari, kudi na iya karewa, amma nagarta ita ce ginshiki. A guji auren son zuciya, da na duniya kawai.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor graphics) daga Jihar Kano:
Hmm ai wasu mazan yanzu! Sun fi son auren jari yadda za su ci a sama, su sami wajen kwana da abubuwan bukatar rayuwa. Su indai mace na da kudi sun zama shazumama. Hakan bai dace ba sam, duba da cewar aure ne ba na domin Allah ba sai kwadayin abin duniya. Ai amfaninsa wajen su za su samu abin duniya, suna kwance ba tare da sun yi motsi ba. Rashin amfaninsa su kansu basu da wata daraja wajen matan. Su dage dai su nemi na kansu dan wannan ba hanya ce mai bulewa ba. Matsaloli barkaita za su iya biyo bayan hakan.
Sunana Aminu Bello Mohammed daga Jihar Gombe:
A hakikanin gaskia yin hakan kuskure ne, a wani kaulin kuma a kira yin hakan jahilci. Ba shi da wani kmfani, domin kuwa babu amfanin auren da babu soyayya, kuma ai arzikii nufi ne na Allah, indai za a yi irin wannan auren babu abin da ke biyo baya sai wulakanci. Matsalolin ba za su kirgu ba, sabida yawan su, kadan daga ciki shi ne auren ba zai yi karko ba, domin an yishi ne bisa son zuciya da kwadayin abin duniya. Shawara ga masu wannan hali shi ne suke tsoron Allah, su nemi yardan Allah akan dukkan lamura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp