Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta ƙara ƙaimi wajen ɗaukar matakai na daƙile ambaliyar ruwa a cikin birane, bayan ruwan sama mai ƙarfi da ya shafe sama da sa’o’i uku da akayi, wanda ya mamaye wasu sassan birnin Kano ranar Alhamis.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dahiru Hashim, ya ce ruwan ya nuna irin raunin da birnin ke fuskanta sakamakon sauyin yanayi da hauhawar zafin duniya. Ya ƙara da cewa gwamnati ta riga ta share manyan magudanan ruwa tun farkon damina tare da tallafa wa ƙungiyoyin al’umma wajen share ƙananan hanyoyin ruwa da tashoshi.
A cewarsa, an kuma ƙaddamar da ayyukan sarrafa shara da shuka bishiyoyi domin rage illolin da ambaliya ke jawo wa. Haka kuma ana gina babban magudanan ruwa a shataletalen Babangwari wanda zai riƙa ɗaukar ruwan sama daga fiye da rabin birnin.
Gwamnatin jihar ta ce za ta gabatar da sabon shirin babbar hanyar magudanan ruwa a cikin kasafin kuɗin 2026. Hashim ya kuma yi kira ga jama’a da su guji zubar da shara a inda bai dace ba da kuma gina gidaje a kan hanyoyin ruwa domin hakan na ƙara tsananta ambaliya.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da jajircewa wajen samar da hanyoyin da za su ƙarfafa lafiya birnin a yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen sauyin yanayi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp