Bisa wani rahoton da kula da rage cunkoso na TTP ya bayyana cewa, an samu karin yawan manyan motocin da ke bin hanyoyin shiga cikin Tashar Jiragen Ruwa da ke a jihar Legas zuwa sama da 2,000 a kullum.
Wannan ya nuna irin mahimmanci da hanyoyin suke da shi, musamman wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar.
- Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
- Saliba Ya Sabunta Kwantiraginsa Da Arsenal Har Tsawon Shekaru 5
Kazalika hanyoyin sun kasance tamkar wani tsani ne, na hada-hadar fitar da kaya waje da kuma kayan da ake shigowa da su, cikin kasar, musamman duba da irin yawan Kwantainonin da a killum, ake shiga da su a hanyoyin.
A saboda yunkurin da Hukumar Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar ke yi na magance matsalolin da cunkoson musamman na mayan motocin a cikin harabar Tashoshin Jiragen Ruwan ne, ya sanya ta kirkiro da sabon tsari a 2021 tare da kuma wanzar da shi wanda ake yin amfani da na’urar zamani da ke kira a trance, electronic call-up system.
Wannan tsarin na tabbatar da ganin cewa, manyan motocin da ke shiga Tashoshin sun mallaki Tikiti kafin a ba su damar shiga cikin Tashoshin Jiragen Ruwan musamman domin a dakele barin shigar su ba tare da samun izini ba.
Tashar ta jihar Legas na da natukar mahimmanci a tsarin jigilar shofar da kaya a kasar nan wadda kuma ta kasance a kan gaba wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan.
A hirar da da manema labarai Manajin Darakta na TTP Jama Onwubuariri ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da aka samu a bangaren na TTP tun lokacin da aka faro sun hada da, sanya ido kan sama da manyan motocin miliyan uku da ke shiga cikin Tashoshin musamman bisa nufin rage cunkoson da kuma sake fitarsu, daga cikin Tashoshin a kan lokaci
Ya sanar da cewa, kirkiro da tsarin biyan kudade kan lokaci na shigar motocin cikin Tashoshin hakan ya taimaka matuka, wanda kuma bisa hadakar da aka yi da hukumar NPS a yanzu da sauran kungiyoyin da aiki a Tashoshin da hukomin tsaro, hakan ya taimaka matuka wajen rage cunkoson a Tashoshin.
Ya kara da cewa ana kuma kan kara wani shirin fadada aikin na TTP, zuwa wasu yankuna na nahiyar Afirka wanda ya bayyana cewa, hakan zai kuma kara bayar da wata damar ta gudanar da zirga-zirgar fitar da kaya a cikin sauri zuwa kasashen da ke a karkashin kungiyar ECOWAS.
” Burin mu shi ne, ci gaba da mayar da hankali wajen inganta amfani da fasahar zamani da kuma kara daga darajar kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar nan, ” A cewarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp