Yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, jam’iyyun siyasa Nijeriya na dakon jiran ganin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), wanda suka kara jaddada muhimmancin samun sahihin zabe da rashin son zuciya da sadaukarwa ga ka’idojin dimokuradiyya.
A cikin wata tattaunawa ta musamman da manema labarai, APC ta bukaci sabon shugaban INEC da ya tabbatar da cewa kowacce jam’iyyar siyasa ta samu martaba daidai ga dukkan jam’iyyun Nijeriya, yayin da PDP ta jaddada bukatar shugaban hukumar ya kasance mai zaman kansa da kuma cin gashin kansa.
- Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
- Ƴan Bindiga Sun Harbe Wanda Suka Sace Saboda Rashin Isassun Kuɗi A Asusunsa
A gefe guda kuma, ADC ta gargadi cewa rashin gudanar da zabe mai inganci a karkashin sabon shugaban INEC na iya zama barazana ga zaman lafiyar dimokuradiyya a kasar nan.
Shugaban INEC na yanzu, Farfesa Mahmood Yakubu, yana shirin kammala wa’adinsa na biyu kafin watan Nuwamba.
An nada shi a 2015, kuma an sake kara masa wa’adi na biyu a 2020, Yakubu yana da daya daga cikin shugabanin INEC da suka fi dadewa a tarihin hukumar zaben Nijeriya.
Bisa sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ” shugaban kasa ne zai nada shugaban INEC da mambobin hukumar zabe ta kasa, sannan majalisar dattawa ta tabbatar da su.”
Dangane da tanadin da ke cikin tsarin mulki, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya tanadi jerin sunayen ‘yan takara da za su meye gurbin Yakubu.
Da yake jawabi kan tsammanin jam’iyyar APC mai mulki, daraktan yada labarai, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa yayin da jam’iyyar ke nufin lashe duk zabe, tana jaddada bukatar samun yin aldaci ga kowa.
Ibrahim, a cikin wata hira, ya bayyana cewa, “A matsayinmu na jam’iyya, abin da muka sa a gaba shi ne samun nasarar cin zabe mai cike da inganci.”
“Babban burinmu shi ne, yadda za mu karbe iko ta hanyar da za ta ba da riba ga dimokuradiyya ga mutane. burinmu ita ce yadda za mu tsaya takara a zabe kuma a ba mu damar taka ba tare da an dakatar da mu ko an cire mu daga zabe ba.
“Don haka, muna sa ran samun shugaban hukumar zabe wanda zai ba da dama ga kowa, wanda zai ba da damar gudanar da zabe cikin ‘yanci da adalci. Muna bukatar shugaban INEC da zai yi aiki ka doka.”
Sakataren yada labarai jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya jaddada cewa dole ne shugaban INEC da zai zo ya zama mutum mai nagarta.
Ologunagba ya kuma kira ga shugaban kasa da masu ruwa da tsaki masu alkakkin zaben shugaban INEC su yi la’akari da halayen ‘yan takarar sosai kuma su tabbatar an nada mutumin da ke da kwarewa.
Ya bayyana cewa, “Shugaban INEC na gaba ya zama wani mutum mai nagarta, ya zama wanda ba zai kasance mai mummunan hali ba, ya zama mai adalci, wanda zai zama mai ‘yanci kuma ya gudanar da hukumar ta wannan hanyar, kamar yadda doka ta tanada. Don haka wannan shi ne abin da muke tsammani.”
Ita kuwa jam’iyyar hadaka, ta bakin sakataren yada labarai na kasa, Bolaji Abdulahi, ta bayyana damuwa kan rikicin bai wa INEC ‘yancin kanta.
Abdullahi ya bayyana cewa sabon shugaban INEC da za a zaba dole ne ya yi aiki don dawo da amincewa ta hanyar tabbatar da gudanar da zabe mai inganci a 2027.
Ya ce, “Abu mafi muhimmanci shi ne, ina tunanin INEC ta sha fama da rikice-rikice na samun amincewa a idon masu kada kuri’a a Nijeriya a cikin shekaru da dama.”
“Sabon shugaban INEC ya kamata ya tabbatar da cewa hukumar ta ci gaba da kasancewa a matakin amincewa. Ka san cewa, tabbatar da tsarin zabe yana karfafa gwiwar kowa, kuma shi ne kawai hanyar da za a tabbatar da kwanciyar hankali a cikin kasar nan.
“Dole ne su tabbatar da nada mtumin da zai kasance tsayayye da kuma jajircewa. Idan aka kasa yin hakan, hakan na iya haifar da shakku a cikin zukatan ‘yan kasa game da ingancin zaben 2027, ko za su kasance masu ‘yanci da adalci kan zaben.
“Don haka, ina tsammanin shekara ta 2027 za ta zama mai muhimmanci ga kowa. A matsayin jam’iyya, muna fatan cewa nadin zai ba da damar ga wanda ya fahimci muhimmancin tarihi na aikin.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp