• English
  • Business News
Saturday, October 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

by Rabi'u Ali Indabawa
4 hours ago
in Rahotonni
0
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yayin da Nijeriya ke murnar cika shekara 65 da samun ‘Yancin Kai, manyan hukumomin jihohi, ‘yan siyasa, da manyan lauyoyi sun bayyana ra’ayoyi daban-daban kan makomar kasar.

Duk da cewa sun yarda cewa kasar na nesa da matsayin da ya kamata ta kasance daga bangaren ci gaba, ra’ayoyinsu sun bambanta kan ko tafarkin da ake bi a yanzu zai kai ta ga samun makoma mai kyau.

  • Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
  • ADC Ta Umarci Dukkan Mambobinta Su Yi Murabus Daga Tsoffin Jam’iyyunsu

Wasu sun yi jayayya cewa Nijeriya ta daina samun ci gaba tun bayan Jamhuriyar Farko da ta Biyu, suna dora laifin ga shiga mulki na sojoji da kuma rashin kyakkyawan shugabancin farar hula wajen koma-baya da kasar ta yi.

A ranar Laraba, 1 ga Oktoba, Nijeriya za ta yi bikin samun ‘Yancin kai daga mulkin Birtaniya a shekarar 1960. Kamar yadda aka saba a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, bikin wannan shekarar na zuwa ne a daidai lokacin da rashin tsaro ke karuwa tare da matsin tattalin arziki kan al’umma.

 

Labarai Masu Nasaba

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

Yadda Sanata Barau Ke Samar da Masana Don Ci Gaban Kano

Nijeriya za ta zama kasa mai girma duk da kalubale — Afenifere

Kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta nuna kwarin gwiwa cewa kasar za ta kasance mai girma.

Sakon wannan kwarin gwiwa ya fito ne daga kakakin kungiyar Afenifere, Kwamared Jare Ajayi, a ranar Asabar yayin da LEADERSHIP Sunday ta tuntube shi a Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Kungiyar siyasa da al’umma mafi girma ta Yoruba ta ce ta dogara da wannan kwarin gwiwa “A kan alherin Allah, albarkatun da kasar ke da su, jajircewar da gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu ke nunawa wajen tabbatar da ci gaban Nijeriya, juriya da karfin hali na mutanen kasar, da kuma jimillar kwarewar da muka samu, kuma har yanzu muna samun sa.”

Afenifere ta kara da cewa ba koyaushe ne ‘yan Nijeriya suke zama cikin jin dadi ba saboda an shafe lokuta da dama ana cikin rashin gamsuwa da shugabannin da suka taba mulkin kasar.

“Wannan lokuta na rashin gamsuwa sun haifar da rashin amincewa tsakanin shugabanni, kuma sun sa wasu mutane yin abubuwan da a al’ada ba za su yiwu ba.

“Amma yana da muhimmanci a amfana da darussan da ke cikin wannan kwarewar domin su zama masu amfani a gare mu,” in ji shi.

Ajayi ya kara da cewa wannan kwarewar ta kara wa mutane karfin hali da juriya.

A cewarsa, abubuwa da dama sun faru a Nijeriya wadanda da sun yi muni da gaske kuma za su iya raba kasar, ba tare da alherin Allah da sadaukarwar ‘yan kasa masu kishin kasa ba.

“Gaskiya ce wadannan abubuwan na ci gaba da kasancewa, duk da cewa kasar na da manyan albarkatu, dalili ne da zai sa a ce Nijeriya za ta kasance kasa mai girma, duk da kalubalen da take fuskanta.”

Ya lura cewa talakawan ‘yan Nijeriya koyaushe suna da sha’awa kuma suna kokari don samun kasa mafi kyau.

“Abin bakin ciki shi ne, da yawa daga cikin wadanda suka rike manyan mukaman gwamnati sun rushe tsammanin ‘yan Nijeriya. Ya dace gwamnati ta roki kowa da kowa ya yi aiki tare wajen sanya Nijeriya ta kasance kasa mai girma ta hanyar daukar taken ‘All Hands on Deck for a Greater Nation’ a matsayin taken bikin ‘Yancin kai na wannan shekarar.”

“Duk da haka, muna ganin cewa wadanda ke rike da mukaman gwamnati, musamman ‘yan siyasa, ya kamata su nuna karin kishin kasa a aikinsu, yayin da da yawa daga talakawan ‘yan Nijeriya suka riga suka fara aiki tukuru.”

Kakakin Afenifere ya bayyana fatan cewa tasirin alherin da matakan manufofi daban-daban da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dauka zai fara bayyana zuwa karshen wannan shekarar.

Kungiyar ta ce ana sa ran tattalin arzikin kasar zai kara inganta a sabuwar shekara, bisa ga alamu da suka riga suka fara bayyana kuma daidai da Manufar “Renewed Hope Agenda” ta Shugaba.

Bugu da kari, ana sa ran samun manyan ci gaba a bangaren tsaro, musamman tare da kaddamar da ‘yansanda na jihohi, wani bangare ne da gwamnati ke nuna matukar himma a kai.

Yayin da kasar ke cikar shekararta ta 66 da samun ‘yancin kai, gwamnatocin jihohi ya kamata su ba wa kananan hukumomi karin ‘yanci “domin mutane a matakin kasa su iya jin tasirin gwamnati cikin inganci.”

Sai dai, Ajayi ya yi kira ga gwamnati da ta aiwatar da sake fasalin kasar a sabuwar shekara.

 

Bala’in da muke ciki laifin sojoji ne da kundin tsarin mulki na 1999 — PANDEF

A nata bangaren, Kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF) ta dora laifi kan sojoji da Kundin Tsarin Mulki na 1999 saboda rashin ci gaban kasar cikin shekaru 65 da suka gabata.

Sakataren yada labarai na kasa na PANDEF, Dr Obiuwebbi Ominimini, shi ya bayyana haka a cikin hira da LEADERSHIP Sunday a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribers.

Ominimini ya ce: “Ya kamata mu dora laifi kan gwamnatin soja wadda ta kafa tsarin tarayya. Mulkin Aguiyi Ironsi ne ya lalata abin da shugabanninmu suka yi gwagwarmaya a kai.

A lokacin samun ‘yancin kai, mun yi gwagwarmaya domin sahihin tsarin tarayya; ikon mallakar albarkatu da kuma biyan haraji ga cibiyar gwamnati.”

“Wannan ne ya ba wasu yankuna damar samun saurin ci gaba. Misali, yankin Gabas ya iya gina jami’a daga abin da ake samu daga auduga da man gyada, yankin Arewa ya iya gina Jami’ar Ahmadu Bello daga ginshikan gyada, Awolowo a yammacin kasa ya iya gina jami’a tare da kafa tashoshin rediyo/talabijin na farko. Ya yi abubuwa da dama a Ibadan da kuma yankin Yamma.

“Amma sai Aguiyi Ironsi ya zo ya kaddamar da tsarin tarayya, ya kuma tattara dukkan ikon a cibiyar gwamnati. Yayin da wasu ba su iya taba albarkatunsu na halitta ba, irin su mai da gas a yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da wasu sassan Kudu maso Yamma, wasu kuma suna karbar kashi 100 cikin 100 na albarkatunsu.

Misali, zinariya da kuke da ita a yankin Arewa, Zamfara, Neja, Babban Birnin Tarayya, Nasarawa da wasu sassan Arewa, ana tattarawa ne ta hannun iyalai da manyan mutane.”

“Saboda haka, kana da attajirai masu biliyoyin kudi a wasu sassan Arewacin Nijeriya, yayin da kake da talakawa daga yankin Neja Delta. Yau, ana mulkin Nijeriya ne da ma’aunai guda biyu. Wannan sakamakon abin da Aguiyi Ironsi ya aikata ne. Lokacin da Gowon ya zo, ya gina tsarin a kan haka.

“Yanzu muna da kundin tsarin mulki da ake kira Kundin Tsarin Mulki na 1999 wanda samfurin karya ne, domin an ce, ‘mu mutanen Nijeriya’, alhali kuwa mutanen Nijeriya ba su taba haduwa don rubuta wannan kundin tsarin mulki ba.”

 

Ci Gaban Kasarmu Yana Tafiyar Kunkuru — Tsohon Sakataren ACF

Tsohon sakataren Arewa Consultatibe Forum (ACF) kuma dattijo, Anthony Sani, ya ce bikin cikar Nijeriya shekara 65 yana tattare da farin ciki da bakin ciki.

A cikin martaninsa kan batun Nijeriya a shekara 65, Sani ya nuna takaici cewa duk da shekaru 65 da samun ’yancin kai, kasar na ci gaba kamar tafiyar kunkuru.

Sani ya ce, “Matsayina kan Nijeriya a shekara 65 yana dauke da farin ciki da bakin ciki, farin ciki saboda muna da ’yanci mu yi mulkin kanmu yadda muke so; bakin ciki kuma saboda ci gaban namu yana tafiyar kunkuru.

“Bikin ya kamata ya kasance na lissafin abin da muka cimma da kuma inda muka yi rauni, sannan mu tsara hanyar gaba cikin sauri fiye da haka,” in ji shi.

 

Yawancin ’yan Nijeriya sun rasa fata, in ji Okorie

Ga wanda ya kafa (APGA), Cif Chekwas Okorie, a batun shekara 65, yawancin ’yan Nijeriya ba su da wani fata.

Ya koka kan abin da ya bayyana a matsayin rashin adalci, gaskiya da daidaito a kasar, musamman a yankin Kudu maso Gabas tun bayan samun ’yancin kai.

Okorie ya lura da cewa tun bayan kammala yakin basasa na Nijeriya a shekarar 1970, yankin Kudu maso Gabas ya ci gaba da fuskantar wariya.

Ya tabbatar da cewa ’yan Igbo sun ci gaba da kasancewa a matsayin masu shan wahala, inda ya kara da cewa waccan wariya ta dauki mummunan salo a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari, kuma gwamnatin yanzu ta Bola Ahmed Tinubu ba wai kawai ta dauka ba, har ma ta kai ta wani sabon matsayi.

Ya ce abin takaici ne shugaban kasa ya bai wa dukan yankin Kudu maso Gabas ministoci biyar kawai, alhali Jihar Ogun kadai tana da manyan ministoci goma.

Yayin da yake waiwayen tarihi, Okorie ya bayyana cewa sojoji sun kirkiri kananan hukumomi 188 a Arewa maso Gabas, amma suka bai wa dukan Kudu maso Gabas kananan hukumomi 188 kawai.

Ya koka kan rushe kadarorin da ’yan Igbo ke da su a Jihar Legas duk da cewa an bayar da izini.

Okorie ya kuma lura da cewa lokacin da Arewacin kasar ya ki yarda da samun ’yancin kai, Herbert Macaulay da Nnamdi Azikiwe sun yi zagaye a sassan kasar, musamman a Arewa, suna wayar da kan jama’a kan muhimmancin samun ’yancin kai.

Ya ce, sakamakon rashin adalci da ake yi wa ’yan Igbo da sauran sassan kasar, ya kafa wata kungiya mai suna Igbo Agenda domin tunkarar ’yan Igbo zuwa babban zaben 2027.

Ya bayyana cewa fitattun ’yan Igbo da dama suna shiga cikin wannan shiri, inda ya kara da cewa za su shirya taron siyasa na farko na ’yan Igbo a watan Janairu na shekara mai zuwa.

Okorie ya kara da cewa ’yan Igbo za su yanke wanda zai zama shugaban kasa a 2027, yana mai cewa ’yan Igbo suna da kashi 25 cikin 100 na kuri’u a dukkan jihohin kasar.

“Mun yanke shawarar tayar da gwarzon da ke barci; za a kayar da Tinubu a Jihar Legas a 2027. Duk wanda yake son zama shugaban kasa a 2027 dole ne ya yi yarjejeniya da ’yan Igbo,” in ji shi.

 

Nijeriya Na Ja Da Baya, In Ji Tsohon Dan Majalisa

A nasa jawabi, tsohon dan majalisar dokoki na Jihar Enugu, Alek Ogbonnia, ya ce Nijeriya na ja da baya a daidai lokacin da ta cika shekara 65.

Ogbonnia, wanda kuma shi ne shugaban tsofaffin ‘yan majalisa na jihar, ya ce ilimi wanda ake tsammanin shi ne ya kamata ya tsara ci gaban kasar, ya rushe.

Ya zargi wasu sojojin kasa da ‘yansanda na kasa da zama ‘yan fashi da makami domin yanzu suna karbar kudi daga hannun jama’a da bindiga.

Ogbonnia ya bayyana cewa Nijeriya ba ta ci gaba, yana mai jaddada cewa abubuwa da dama a Nijeriya suna rushewa.

Ya kara da cewa yawancin kaliban Nijeriya da suka kammala karatu ba sa samun aiki, yayin da rashin aikin yi ya ci gaba da yaduwa a cikin kasar.

 

Nijeriya Kullum Baya Take Komawa, In Ji Shugaban PDP Olafeso

A cewar tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Kudu maso Yamma, Dakta Eddy Olafeso, kasar nan ba ta da abin murnar cika shekara 65 da samun ’yancin kai.

Sai dai, Olafeso ya ce akwai abubuwa da dama da za a iya fata a nan gaba kadan.

“Kasarmu ba ta samu ci gaba na gaskiya ba tun bayan samun ’yancin kai,” in ji shi.

Yayin da yake magana da jaridar LEADERSHIP Sunday a Akure, babban birnin Jihar Ondo, a ranar Asabar, mamban kwamitin amintattu na PDP ya nuna cewa ci gaban kasar a tsawon shekaru ya tsaya cik sakamakon rashin ingantaccen shugabanci.

“Kasarmu ba ta taba samun ci gaba mai kyau ba tun daga zamanin Jamhuriyya ta Farko a karkashin Obafemi Awolowo a Yammacin Nijeriya, Sardauna da Tafawa Balewa a Arewa, da kuma Michael Okpara da Nnamdi Azikiwe a Gabas.

“Duk da haka, ina ganin zamani da fasaha sun riga mu gaba kwarai, lamarin da ya sanya babu wani zabi face mu ci gaba da amfana daga wadannan ci gaban kasa-da-kasa.

“Amma idan aka yi nazari kan ci gaban dan’Adam, ingancin rayuwa, samar da lafiya da ilimi, da kuma ci gaban ababen more rayuwa, muna kama da ’ya’ya marasa wayo da aka bar su a baya.”

 

“Ina ganin cewa duk da alamu na tafiyar da al’amura ga wasu, kusan rabin jama’armu na rayuwa ne karkashin talauci. Ba za mu iya kira wannan ci gaba ba, dan’uwana. Kuma yawan jama’armu na karuwa cikin sauri.”

Olafeso ya bayyana cewa kasar tana kara zama “gidan talauci mai tsanani.”

“Babu yadda za a yi wadannan matsaloli su wuce ba tare da tasiri a kan ingancin rayuwa ba. A ganina, babu abin da za a yi murna da shi a shekara 65, amma akwai abubuwa da yawa da za mu iya sa ran samu nan gaba.”

“Tambaya a nan ita ce, shin mutanen da ke rike da madafun iko sun dace da wannan aiki? Shin suna yin mafi iyawarsu? Shin sun iya ilmantar da kansu? Gwamnati ba za ta iya cewa ‘ku matse bel dinku’ ba alhali cikin wadanda ke fadin haka na kara girma kullum.”

Olafeso ya koka kan rashin tsoron Allah da rashin jin tsoron doka a tsakanin ‘yan Nijeriya, musamman wadanda aka dora wa nauyin mulki.

“Babu ladabi a cikin gwamnati. Kowa a karshe cin hanci da rashawa yake yi. Ya zama salon rayuwa. Rashawa salon rayuwa ne a Nijeriya. Talakawa an bar su gaba daya ga kaddararsu. Babu tsaro a kasar. Wadannan shugabanni ba su yi mana wani abu mai amfani ba. Ba na cewa laifin APC kadai ne, amma tun bayan samun ‘yancin kai, ‘yan kadan daga cikin shugabanni ne suka tsarkake kansu wajen kula da talakawa a titi.”

“Mutumin da kake magana da shi yana bin bashin rayuwarsa da rayuwar ’yan’uwansa ga Obafemi Awolowo, wanda ya bai wa mahaifina da surukina damar tura kowa makaranta. Uwaye masu aure da yawa ba su da kudi sosai, amma duk ’ya’yansu sun samu ilimi.

Amma a yau, yanayin yana kara muni. ’Yan gudun hijira, wadanda suka rasa matsuguni a cikin kasa suna cikin mawuyacin hali fiye da wadanda ke cikin filayen yaki,” in ji shi.

 

Nijeriya Ta Tsaya Cik – Nsirimobu

Shima a nasa bangaren, mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Courage Nsirimobu, ya ce a shekara 65, Nijeriya ba ta ci gaba ba, illa dai ta tsaya cik.

“A shekara 65, Nijeriya ta fuskanci koma-baya ko kuma abin da muke kira jinkirin ci gaba. Ban yi imani cewa muna ci gaba ba. Har yanzu ana kiran ta kasar duniya ta uku da kasa marar ci gaba.

“Tambayar wa za a dorawa laifi abu ne a bayyane; mun yi ta samun jerin shugabanni marasa nagarta da ba su taba magance tushen matsalolin Nijeriya ba,” in ji Nsirimobu.

 

An Gina Nijeriya Kan Tushen Da Bai Dace Ba – Robinson

A nasa bangaren, wani mai fafutukar kare ’yan yankin Neja Delta, Dr Ken Robinson, ya danganta matsalar Nijeriya da tushen ta da bai dace ba.

Robinson ya ce: “Idan ka gina gida kuma gidan bai kasance yadda kake tsammani ba, ya kuma yi lahani, to shirinka ne ya lalace. Don haka, tushen wannan kasa bai yi daidai ba. Ba muna zaune tare don mu yarda da halin da muke ciki ba. An tilasta mana ne.

“Saboda haka, tun daga farko, komai ya tafi ba daidai ba, kuma muna ta gini a kan tushe marar kyau, tare da injiniyoyi marasa kyau, masu zanen tsari marasa kyau da kuma mazaunan gini marasa kyau.”

“Wannan shi ne abin da ya haifar da abin da muke gani; rashin tsaro, talauci, wahala, rashin iya gudanarwa, cin hanci da rashawa, rashin gaskiya, rashin kishin kasa daga wasu ’yan kasa da kuma rashin hadin kai da ci gaba.

Duk wani abu da ake gani yanzu ya samo asali ne daga tushen da bai dace ba,” in ji shi.

Wasu lauyoyi da suka yi magana da LEADERSHIP Sunday sun ce kasar ba za ta iya cimma sahihin ’yanci ba idan shugabanni ba su nuna karin jajircewa ba. A cewarsu, juyin mulki da aka yi ta samu a kasar a baya sun ja kasar baya; duk da haka, hakan ba zai zama uzuri ba wajen rashin samar da ingantaccen mulki.

Abdul Balogun, babban lauyan Nijeriya (SAN), ya ce shugabanni suna bukatar su yi karin aiki idan ana so a ji tasirinsu ga mutanen da suka zabe su. Ya bayyana tsarin zaben kasar a matsayin abin kunya, inda ya ce, “Abin kunya ne cewa bayan shekara 65, har yanzu ba mu daidaita tsarin zabenmu ba.

Abin da kasa za ta iya yi shi ne ta sanya tsarin zabe ya zama mai gaskiya da bayyanawa. Tsarin zabenmu, a halin da ake ciki, ba na gaskiya bane. Akwai shinge daga farko har zuwa karshe.”

A cewarsa, har yanzu bangaren shari’a shi ne kawai reshen gwamnati da ke rike kasar waje guda. Ya ce, “Duk yadda mutane za su iya ganin bangaren shari’a da rashin kyau, har yanzu shi ne kadai cibiyar da ke tsaye ba tare da aibantawa ba. Tabbas, akwai munanan mutane a ciki, amma hakan bai isa ya soke gagarumin aikin da shari’a ke yi a kasar ba.”

Ya ci gaba da cewa, “A lokacin da muka sami ’yancin kai a shekarar 1960, mun gaji tsarin mulki da ke tafiya a kan rassa uku: bangaren zartarwa, bangaren majalisa, da bangaren shari’a. Ina bukatar in bayyana cewa a shekarar 1960, ana tura korafe-korafe daga Nijeriya zuwa Birtaniya domin samun hukunci na karshe.

Abin da muka gani daga baya shi ne mun yar da kundin tsarin mulkin ’yanci a shekarar 1963 domin mu dauki matsayin Jamhuriyya, kuma Sarauniya ta daina kasancewa Shugabar Kasarmu.”

“An kafa Kotun Koli a matsayin kotu ta karshe, saboda haka mutum zai yi tsammani cewa da zarar muna da Kotun Koli tamu, doka ta Nijeriya za ta zama mafi rinjaye. Idan ka kalli haka, za ka ga cewa ina jan kafa wajen cewa bangaren shari’a a Nijeriya ya cancanci ‘A’ saboda yanayin da muke ciki a matsayin kasa.

Wadannan yanayi sun sanya ba zai yiwu ba gare ni a zauna a matsayin dattijo in ba wa bangaren shari’a ‘A’, amma duk da haka, zan ba shi babban alamar nasara saboda ya kasance abin da ke daidaita al’amura. Ko mutane sun amince da hukuncin kotu ko ba su amince ba, ba shi da wani tasiri.”

“Ba shi da wani tasiri a ma’anar cewa muna gaskata da mulkin doka, amma ba ma son bin tafarkin doka.”

“Eh, zan iya fadin hakan a sarari. Yawancin ’yan Nijeriya ba sa son su amince da jan hankali; duk abin da ya tashi dole ya sauka,” in ji shi.

Lauyan tsarin mulki, Yusuf Baleh, ya gargadi shugabannin kasar da su daina raina jama’a. Ya ce, “Shekara 65 kenan, amma har yanzu ’yan Nijeriya ba su ji tasirin mulki ba.”

A cewarsa, shugabanni na iya kin karbar gaskiyar cewa ’yan Nijeriya na fama da mawuyacin hali, inda ya ce, “Shugabanni na iya kin gaskiyar cewa mafi yawan ’yan Nijeriya ba sa iya samun abinci sau uku a rana.”

Ya kara da cewa, “Daya daga cikin matsalolin da kasar ke fuskanta su ne, munanan tsarin zabe. Sai mun daidaita zabukanmu. Wannan saboda dan siyasa yana ganin bai bukaci kuri’ar jama’a ba don ya shiga ofis, kuma hakan zai sa ya yi rashin kyautata hali saboda yana ganin kuri’ar jama’a ba ita ta kai shi ofis ba.”

“Ba za mu iya samun ci gaba mai ma’ana ba idan tsarin zabenmu ya ci gaba kamar yadda aka saba,” in ji shi a karshe.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Nijeriya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

Next Post

Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

Related

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin
Rahotonni

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

20 hours ago
Yadda Sanata Barau Ke Samar da Masana Don Ci Gaban Kano
Rahotonni

Yadda Sanata Barau Ke Samar da Masana Don Ci Gaban Kano

1 day ago
Masana Sun Dora Alhakin Rashin Cika Alkawuran ‘Yan Siyasa Kan Jam’iyyu
Rahotonni

Masana Sun Dora Alhakin Rashin Cika Alkawuran ‘Yan Siyasa Kan Jam’iyyu

7 days ago
Rashin Aikin Yi: A Halin Yanzu Masu Digiri Na Sayar Da Fiya Wata Da Aikin Achaba
Rahotonni

Rashin Aikin Yi: A Halin Yanzu Masu Digiri Na Sayar Da Fiya Wata Da Aikin Achaba

7 days ago
2027: Abubuwan Da Jam’iyyun Siyasar Nijeriya Ke Tsammanin Samu Daga Sabon Shugaban INEC
Rahotonni

2027: Abubuwan Da Jam’iyyun Siyasar Nijeriya Ke Tsammanin Samu Daga Sabon Shugaban INEC

1 week ago
Maulud 1,500: Yadda Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Ta Yi Maulidin Takutaha A Kaduna 
Rahotonni

Maulud 1,500: Yadda Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Ta Yi Maulidin Takutaha A Kaduna 

2 weeks ago
Next Post
Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Gwamnatin Jigawa Ta Bai Wa  Mahaddata Ƙur’ani 200 Tallafin Karatu

Gwamnatin Jigawa Ta Bai Wa  Mahaddata Ƙur’ani 200 Tallafin Karatu

October 4, 2025
Ruwan Sama Ya Lalata Gadoji Da Hanyoyi A Taraba, Kebbi Da Filato

Ruwan Sama Ya Lalata Gadoji Da Hanyoyi A Taraba, Kebbi Da Filato

October 4, 2025
Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

Jami’ar Ibadan Ta Bude Sashen Karatu A Gida Ta Intanet

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi

October 4, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum Hudu Da Ake Zargi Da Aikata Muggan Laifuka A Yobe

October 4, 2025
Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Tinubu Zai Ziyarci Jos Domin Halartar Jana’izar Mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa

October 3, 2025
MDD Ta Yi Alƙawarin Tallafa Wa Gidauniyar Malala Mai Rajin Inganta Ilimin ‘Ya’ya Mata

MDD Ta Yi Alƙawarin Tallafa Wa Gidauniyar Malala Mai Rajin Inganta Ilimin ‘Ya’ya Mata

October 3, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.