Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sanar da cimma yarjejeniyar sayan dan wasan kungiyar Ajad dan kasar Brazil, Antony, bayan ta amince za ta biya fam miliyan 80.75 da karin tsarabe-tsaraben fam miliyan 4.25.
Dan wasa Antony ya zama dan wasa na biyu da Manchester United ta dauka mai tsada bayan dan wasa Paul Pogba wanda ya kasance mafi tsada da kungiyar Old Trafford ta saya daga Jubentus kan fam miliyan 89 a shekara ta 2016.
- Pogba Ya Ce Barayi Suna Yi Masa Barazana
- Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Keta Ka’idojin Fitar Da Kayayyaki
Antony zai zama dan wasa na biyar da Manchester United ta dauka a bana, bayan dan wasa Lisandro Martinez da Casemiro da Tyrell Malacia da kuma Christian Eriksen wanda kwantiraginsa ya kare a Brentford kuma Antony ya taka rawar gani a Ajad da cin kwallo 47 a dukkan fafatawar da ya yi mata kaka biyu.
Dan wasan ya nuna kwarewarsa karkashin kociyan kungiyar na yanzu, Erik ten Hag a Ajad, kuma shi ne kocin ya dauke shi zuwa Manchester United saboda ya san irin salon buga wasansa a baya.
Dan wasan mai shekara 22 a duniya ya zama dan wasa na hudu da aka saya a Premier League da tsada, bayan Paul Pogba da ya koma Manchester United, sai Chelsea da ta dauki Romelu Lukaku da kuma Jack Grealish da Manchester City’ ta dauka.
A ranar 8 ga watan Agustan shekara ta 2016, Manchester United ta kammala daukar Paul Pogba kan fam miliyan 89 kuma dan kwallon tawagar Faransan ya sanar cewar ”lokaci ne ya yi da ya sake komawa kungiyar da ta dace da shi da salon wasansa.
Dan wasa Pogba ya koma kungiyar yana da shekara 23 a lokacin, bayan shekara hudu da ya bar kungiyar zuwa Jubentus kan fam miliyan 1.2 a 2012.
Sannan kudin da aka sayi Pogba ya haura fam miliyan 85 da Real Madrid ta dauki Gareth Bale a shekarar 2013 a matakin mafi tsada a duniya.
Pogba shi ne dan wasa na hudu da Jose Mourinho ya dauka a lokacin, bayan dan wasan tawagar Ibory Coast, Eric Bailly da dan wasan Sweden, Zlatan Ibrahimobic da dan wasan Armenia, Henrikh Mkhitaryan.
Karon farko bayan shekara 20 da wata kungiya a Ingila ta sayi dan wasa a matakin mafi tsada a duniya tun bayan da Newcastle United ta biya fam miliyan 15 kudin Alan Shearer daga Blackburn Robers.
Pogba ya fara zuwa Manchester United daga Le Habre a shekarar 2009 a matakin mai shekara 16, sai dai wasa bakwai kadai ya yi wa kungiyar, sannan ya tafi zuwa Jubentus a 2012, bayan da kwantiraginsa ya kare.
Dan wasan ya yi wasanni 178 a Jubentus da cin kwallo 34 da lashe Champions League a kungiyar ta Italiya a 2015.
Sai kuma ranar 12 ga watan Agustan shekara ta 2021, dan wasa Romelu Lukaku ya sake komawa Chelsea daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5 kuma dan wasan mai shekara 28 a lokacin da dan kwallon kasar Belgium ya sake komawa Chelsea kan yarjejeniyar kakar wasa biyar, bayan da ya koma Eberton daga kungiyar kan fam miliyan 28 a 2014.
Kadan ya rage kudin da aka sayo Lukaku ya kai iri daya da wanda Manchester City ta dauki Jack Grealish daga Aston Billa kan fam miliyan 100 sannan Lukaku shi ne mafi tsada da wata kungiya a Italiya ta sayar, tun farko ya zama na uku mafi tsada da aka dauka a Italiya a 2019 da Inter Milan ta saya daga Manchester United kan fam miliyan 74.
Tun farko kungiyar Chelsea ta bai wa Eberton aron Lukaku a shekarar 2013, daga baya ta sayar mata da shi a Yulin 2014 kan fam miliyan 24 a matakin dan wasan da ta saya da tsada a tarihin Eberton.
Har ila yau a ranar 5 ga watan Agustan shekara ta 2021, Manchester City ta sanar da daukar dan wasa Jack Grealish kan yarjejeniyar kakar wasa shida da za ta kare zuwa shekarar 2027 sannan Manchester City ta sayi Grealish daga Aston Billa kan fam miliyan 100.
Dan wasan mai shekara 25 ya karbi riga mai lamba 10, wadda Sergio Aguero ya yi amfani da ita a kungiyar, sannan kudin da Manchester City ta sayi dan kwallon ya haura fam miliyan 89 da Manchester United ta dauki Paul Pogba daga Jubentus a 2016.
Bugu da kari kwana bakwai tsakani da Manchester City ta sayi Grealish, Chelsea ta sake daukar Lukaku daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5 wanda hakan ne ya sa Grealish kan gaba a matakin wanda aka dauka mafi tsada a tarihin gasar Premier Legue kuma Lukaku ne na biyu, sai Pogba na uku, sannan Antony na hudu.