Jami’ai uku da aka dakatar na jam’iyyar APC a karamar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara sun shigar da jam’iyyar kara a gaban kotu suna kalubalantar dakatarwa da aka yi musu a matsayin rashin bin dokar jam’iyyar.
Babangida Aliyu Shinkafi da Kabiru Ibrahim da kuma Ibrahim D. Kurya sun shigar da kara a gaban babban kotun Jihar Zamfara da ke Gusau, a ranar 14 ga Nuwamba, 2025, suna nemi kotu ta soke dakatarwar da aka yi musu da kuma hana ci gaba da kamfe na tsoratarwa da cin zarafi da nuna wariya daga shugabancin jam’iyyar a jihar. Cikin wadanda ake karar sun hada da jam’iyyar APC, Alhaji Tukur DanFulani Maikatako da Alhaji Ibrahim Bama Shinkafi.
Mambobin jam’iyyar uku, wadanda suke aiki a matsayin shugaban gunduma, sakataren walwala da wakilin masu Nnakasa bi da bi, sun bayyana a cikin bayanin da suka bayar cewa suna ci gaba da zama sahihan mambobin gudanarwa na APC, bayan an zabe su bisa ka’ida a lokacin taron jam’iyya na 2022. Sun bayyana cewa dakatarwar an yi ta ne saboda siyasa kuma tana da alaka da biyayyarsu ga jigon APC, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi wanda ake cewa yana da matsala a dangantakarsa da wasu mutane masu rinjaye a cikin reshen jam’iyyar na jihar saboda tsayuwarsa kan ka’idojin dimokuradiyya wajen bin tsarin doka da sauran su. Mambobin suna neman sanarwa cewa “duk wani yunkuri na dakatarwa, korewa, tsoratarwa, cin zarafi ko kawar da membobinsu (Shinkafi, Ibrahim da Kurya) daga APC ta hannun wadanda ake kara (APC, Maikatako da Shinkafi) ko wani mutum kuma da ake kiransa da wani suna, ya saba wa doka, saba ka’ida, karya dokoki da kuma yin karfa-karfa.” Sai dai kuma kotu ba ta saka ranar fara sauraron wannan shari’a ba.














