Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu, domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a Taron Shugabannin G20.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai halarci taron, amma ya yanke shawarar zama a gida domin mayar da hankali kan sha’anin tsaro, bayan hare-haren jihohin Kebbi da Kwara.
- Nijeriya, Ghana Da Cote d’Ivoire Za Su Iya Karɓar Baƙincin Gasar Kofin Duniya – Ministan Wasanni Na Ghana
- Nijeriya, Ghana Da Cote d’Ivoire Za Su Iya Karɓar Baƙincin Gasar Kofin Duniya – Ministan Wasanni Na Ghana
A cewar mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, Shugaban Afirka Ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda zai jagoranci taron G20 na wannan shekara, shi ne ya gayyaci Shugaba Tinubu zuwa taron.
Za a yi taron daga ranar Asabar, 22 ga watan Nuwamba, zuwa Lahadi, 23 ga watan Nuwamba, a cibiyar baje kolin Johannesburg (Johannesburg Expo Centre).
Taron zai haɗa shugabanni daga manyan ƙasashe 20 na tattalin arziƙi a duniya, Tarayyar Turai (EU), Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), da manyan hukumomin kuɗi.
Sanarwar ta ƙara da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa zai dawo Nijeriya bayan kammala taron.














