Ba kamar dai yadda abin ya kamata ya kasance ba wato dattin da ake ta cin karo da shi da kuma gani a kan tituna ne, shi yasa lamarin yake da matukar tada hankali ne domin kuwa haka abin yake kasancewa,a kan tituna, da cikin Kasuwanni, da kuma hanyoyi, saboda wasu abubuwan da suka hada da rashin wuraren da ya dace a rika sa shara da kuma rashin kwashewar.Irin wannan matsalar da take gurbatawa da lalata muhalli ko shakka babu abin gaskiya ne domin kuwa sun ce yana matukar taimakawa ga abubwan da sune suke kawo cikas ga lafiyar al’umma da kuma yiyuwar kamuwa ko barkewar cututtuka,wanda daga karshe yana dakushe karkashi da ganin kimar shi Babban Birnin tarayyar.
Mazauna shii Birnin da masu kawo ziyara sun a ci gaba da nuna damuwarsu kan yadda ake zubar da shara da yaduwar Bololi masu yawa kan manyan hanyoy wanda lamarin na rashin kulawa, da maida hankali na wadanda alhakin yin hakan ya rataya a wuyansu domin rashin nuna damuwa ta kawar da ko kwashe su.
Idan mutu ya biyo da ganin yadda manyan garuruwan na Babban Birnin tarayyar suke kamar Wuse, Utako, Garki, Gwarinpa, Jabi, Life Camp da kuma Nyanya, yanzu yawan shara nan da can, ana iya cewa suna gasa ne da irin yadda tsarin mafi dacewa na yadda shi BabbanBirnin ya kamata ya kasance.
Ya yin da wari na rubabbun abubuwan da suka lalace iska na dauka warin zuwa sama, yayin da su kuma masu harka da Bola da wasu Dabbobi suke ta harkokinsu a irin wuraren da aka tara Dalar Bola daban- daban inda ya kamata ake zubawa amma kwashewar tana neman gagara kamar yadda ya dace.
Birnin Tarayya da ya zama abin burgewa da sha’awa a lokutan baya, da tunfarko an tsara shi ne, sai dai kuam yanzu abin ya zama Muhallin ne da ya dace ya rika kasance kowane lokaci abin ban sha’awa, yanzu sai dai wadanda abin ya zama masu dole suke harkokinsu da mazaunan shi ,har ma suke nuna abin tamkar kamar bai damesu ba.
“Ko ta in aka duba, za ka lura d akwai yawan shara da aka zuba wurun da aka saba sawa azo a kwashe amma makonni da yawa yin hakan bai samu ba,” kamar dai yadda Oritoke Olalekan, mazaunin Wuse ya nuna rashin jin dadinsa.
“Da alama hukumar kula da kiyaye yadda muhallin Babban Birnin tarayya da kamata ya kasance (AEPB) ta yi dogon Bacci ne da yasa har yanzu bata farka ba.Domin kuwa ai wannan shi ne babban aikinsu layuyyuka su kasance cikin tsafta, sai dai kuma yanzu yin hakan na neman gagararta har ta kai faduwar Tasa.”
Masu motoci da ‘yankasuwa suma sun nuna rashin jin dadinsu
Rafiu Jimoh-Adebukola, wani direban tashi da yake yin aiki a Utako, ya ce ba karamar barazana bane ga abinda ya shafi lafiya da hadarin dake tattare da yi ma abin rikon sakinar Kashi.
“Idan sharer ta taru da yawa, mutane su kan kunna mata wuta domin su rage irin warin da take yi. Hayakin yana rage mana yadda muke kallon abubuwa sosai da kuma sa numfashinmu ya zama mai wahala. Wani lokaci ma ‘Bata- Gari’ su kan boye irin wuraren da ake tara sharer da yawa su rika kwayyce wayoyin mutane bama kamar idan, an samu cinkoson motoci kamar yadda ya jaddada,”.
A kwanar zuwa Life Camp kuma mahadar Nyanya, mazauna wurin sun ce yawan wuraren da ke tara shara ya zama tamkar wani wuri ne na dindindin domin tara sharar. Wuraren su kan j ara’ayi masu mu’amala da kome yawan sharer da aka tara,wadanda aka fi sani da suna “Baban bola,” wadanda suke daukar wasu kayan da za a iya sake yin amfani da su idan aka yi wata dabara ko amfani da fasaha,amma sau da yawa su kan yawancin abubuwan da basu kamata su barai ba a wurin.
Irin hakan kamar yadda su mazauna wuraren / garuruwan suka bayyana yana taimakawa masu aikata laifuka wajen jindadinsu yadda za su aikata abubuwan da suke yi.
“Suk ace sun wuraren da irin su masu mu;amalar da sharar ake samun matsala da su ta yin sata ko aikata abubuwan da babu dadin ji. Bayan an kama su ‘yansanda na sakinsu bayan sun amshi cin- hanci,” kamar yadda Taye Ayedero yayi zargin hakan na faruwa, wani direba shi ma, cewa ya yi sun gaji da kai wa gwamnati kuka,“;kamata ya yi ita gwamnatin ta daukai mataki.
Lamarin hakanan yake a Wuye, Garki da kuma wasu wurare d a kuma gundumar Maitama.
Wata mazauniyar Wuye, Esther Ishaya cewa ta yi abin yana kara kasancewa wata babbar matsala, inda tace sharar da aka tara wurin ta dade har wata uku ko fiye da haka.
Lamarin ya fi baci a Gwarinpa
Masu harkokin kasuwanci da masu hada- hadar motoci a kusa da gundumar Gwarinpa suma suna nuna rashiin jin dadinsu kan yadda wuraren da ake tara ko zuba shara ya zama wani abin damuwa kan wasu manyan hanyoyi a gundumar.
Wuraren da abin ya fi muni sun hada da wadand a suke kan hanyar 3rd Abenue Road, ta shiga wuraren kwana na ayyuka da gidaje, har ma da kusa da kasuwar Kado-Bimko market.
Yayin da masu harkokin kasuwanci suke nuna rashin jin dadinsu na abubuwan da ke sa wuraren nasu wurin ba wanda za a zauna bane har ayi tunanin yin wata harka musamman ma abokan huldarsu na kasuwanci,masu harkar tuki suma abin yana ci masu Tuwo a kwarya, domin kuwa shara ta rufe hanya, abinda ke kawo cunkoson abubuwan hawa musamman ma lokacin da aka taso daga aiki.
Daya daga cikin masu shaguna da aka tattauna da shi, Fidelis Oketa, ya ce akwai wani “abu mai tada zuciya da yake fitowa daga cikin tarin sharar wanda ba karamar guba bace tana kuma samar da illa ga lafiyar dan Adam’’.
“Mun kai kukanmu ga hukumar gidaje ta gwamnatin tarayya ba sau daya ko biyu ba, domin sune suke bada fili ga duk wanda aka gani nan,amma duk abin ba wani matakin da suka dauka .A matsayi na mai wanda ke harkokin kasuwanci na zuba milyoyin Nairori, ya kuma kasance ina fuskantar irin hakan ai abin wani ci baya ne. Duk yawancin abokan hulda ta sun guje mani ba su zuwa wuri na yanzu saboda irin halin da muke fuskanta yanzu.”
Shi ma da yake magana wata mai gidan abinci kusa da cibiyar, Blessing Daniel,ta ce ta rasa fiye da kashi 70 na masu zuwa su sayi abinci wurinta amma yanzu basu zuwa saboda halin da wurin yake ciki.
“Sabbin fuskokin da su kan zo nan, sai ta kasance ta kyar suke iya tsayawa su kare cin abincinsu, suna barin wurin ne ba tare bata lokaci ba, sauri- sauri suke yi, maimakon su ce a kara sa masu wani abincin lokacin da suke cikin ci.”
Mai harkar abincin sayarwa ta ce wadanda suke lura da kwashe sharar saboda yana da matukar wuya ba duka bane suke kwashe shara koda kuwa sun zo din.
“Za su zo wurin kwashe sharar sau biyu daganan sai su bar wurin zuwa wani wuri kamar yadda ta ce,”.
Ta bada shawarar a maida wurin da ake zubar da sharar zuwa wani wuri da yafi dacewa da a rika kai sharar.
Wani direban Tasi da yake harkar tuki, Jamilu Sulaiman, ya ce masu motoci suna fuskantar matsala ta yin zirga- zurga a wuraren kamar yadda suke son yi, domin kuwa wasu hanyoyin yawan tarin sharar da aka zuba ya rufe su.
Wani shugaban al’umma, Malam Abubakar Ali, ya yi kira da hukumar kare muhalli ta Babban Birnin tarayya wato AEPB ta shigo cikin lamarin , domin kuwa duk irin kokarin da mazauna wurin suka yi bai yi wani tasiri ba.
Shugaban al’ummar Kado-Bimko, Malam Ibrahim Isiaku, wanda shi ma wurin na shi an lalata shi wuraren da aka zuba ko tara shara, ya ce bayanin da suka samu daga wurin hukumar shi ne kwangilar da aka bada ta kwashe shara a wurin ta kare ta dade da karewa.
Ya ce saboda haka ne, wasu mazauna wurin ne suka yanke shawarar sune za su rika biyan kudaden da za’a kwashe masu shara, ta hanayar masu shaguna da kuma sauran masu harkokin kasuwanci a wurin.
Za a iya samun matsalar barkewar annobar da za ta shafi lafiyar al’umma
Kwararre bangaren lafiyar al’umma ya ja kunne wadanda ke da ruwa da tsaki cewa matsalolin da za ‘a iya fuskanta dnaganta da rashin kwashe rana abin duk yafi wani tunanin da mutum zai yi.Kamar yadda suka yi bayani , sharar da ta fara yin wari tana samar da wasu sinadarai masu cutarwa kamar su methane da ammonia, wadada za su iya sanadiyar samar da cututtukan da suke da alaka da lamarin daya shafi numfashi da sauran wasu cututtuka.
Daga Daily Trust muka samo wannan mukalar














