Ba sabon abu bane a ji cewa ‘yar aiki ta aure maigida ko kuma ta kori uwargidan ma gaba daya.
Wannan matsalar tana faruwa ba tun yanzu ba, wanda kuma har wannan lokacin wasu matan sun kasa ganewa su ne ke jawo hakan da kansu har abin ya zo ya dame su.
Mafi yawan mazaje sun fi son ‘yar aiki mace ta kula da ayyukan cikin gida maimakon namiji saboda da dalilai na tsaro. Wasu matan kuma sun gwammace namiji ya yi musu ayyukan gidan domin gudun kada su kawo wacce za ta iya musu illa.
Amma da yake maza sun fi karfin su a daukar matsayi hakan ya sa wasu matan suke saduda amma ba domin suna so ba. Sai dai kuma matan ke jawo matsalar da suke fuskanta da ‘yan aikinsu da kansu, domin su ne suke zabar wacce za ta yi musu aikin ba mazajensu ba.
Ga kura kuren da mata suke yi har ‘yan aikin su ke zama kishiyoin su kamar haka:
1. Dauko wacce ta fita wayo: Mata da dama idan sun tashi dauko ‘yar aiki a rashin sani sai su dauko macen da ta fi su wayo a badini amma a zahiri ta yi kama da doluwa.
Irin wadannan matan ba sa yadda su fito da fuskar kyawunsu na asali idan za su je neman aiki, sai su yi biji-biji yadda mace idan ta ganta tamkar wata abar tausayi. Amma da zarar ta saki jiki sai ta fara fito da halittunta yadda duk wanda ya ganta ta yi.
2. Saka su ayyuka na musamman: Akwai wasu ayyukan da duk rashin son aikin mace ita ya kamata ta yi wa mijinta shi amma ba ta saka wata ta yi masa ba muddin dai ba ‘yar cikinsa bace.
Ayyuka irin na gyaran dakin miji. Yi wa miji girki fita da miji sayayya duk bai dace mace ta bari ‘yar aikinta ta ke mata ba.
3. Barin ‘yar aiki ta fahimci matsalarki da mijinki: Muddin za ku bari ‘yar aiki tana fahimtar abin da yake hada ki da mijinki sabani to tabbas za ta iya amfani da wannan damar ita kuma ta rika dadada masa da abin, yadda har zai fara sha’awar ina ma ita ce matarsa. Don haka ki kiyaye hira da ‘yar aiki akan matsalolinki da mijinki.
Za Mu Ci Ci Gaba Mako Mai Zuwa Idan Allah Ya Kai Mu













