Hukumomin Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio, Aliero, Jihar Kebbi, sun sanar da dakatar da ayyukanta nan take, inda suka umarci dukkan ma’aikata da ɗalibai su bar harabar makarantar ba tare da ɓata lokaci ba.
Umarnin yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Magatakarda Maimaro Alhaji Tilli da Sakataren Majalisar zartarwar jami’ar suka fitar, inda ta bayyana cewa rufe jami’ar zai fara aiki ne nan take kuma ya shafi dukkan nau’ikan ɗalibai da ke karatu a jami’ar.
- G20: Kaduna Ce Jihar Da Tafi Dacewa Da Zuba Jari A Nijeriya – Gwamna Uba Sani
- Wasu Kura-kurai Da Matan Aure Ke Yi Ke Sa ‘Yan Aiki Aure Mazajensu
An umurci ɗalibai su bar harabar makarantar cikin awa ɗaya bayan sanarwar, yayin da aka ba wa Sashen Tsaro na Jami’ar izinin korar duk wanda aka samu a ɗakunan kwanan ɗalibai ko wasu wuraren da aka hana shiga.
Jami’ar ta kuma shawarci ɗaliban da ke da ɗakunan kwana a wajen harabar jami’ar, ciki har da Gidan Rami, da su bar gidajensu don guje wa abin da ta bayyana a matsayin “cin zarafi” daga jami’an tsaro da ke da alhakin tabbatar da bin dokar jami’ar.
Duk da cewa takardar ba ta bayyana dalilin yanke wannan shawara ba, majiyoyi a cikin jami’ar sun danganta ta da sabuwar barazanar tsaro da ke shafar cibiyoyin ilimi a arewacin Nijeriya.
Jami’ar ta bayyana cewa, rufe makarantar zai ci gaba da aiki har sai an samu wata sabuwar sanarwa.














