Shugabannin Kungiyar Miyetti Allah na Kasa (MCBAN) reshen kudu maso gabas, sun roki gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, kar ya tsaurara hana shanu yawo yin kiwo a jihar, inda ya sanar da cewa yin hakan zai shafi kudaden shiga da makiyaya masu kiwon da ke samu don ci gaba da rayuwarsu.
A wata ganawa a gidan gwamnatin jihar da ke a Akwa da gwamna jihar ya gudanar da kwamtin da ke magance yin kiwon dabbobi a kan hanya a jihar, Soludo ya sanar da soke hana bartin yin kiwon shanu a kan hanya a jihar ta Anambra.
- Kotu Ta Bai Wa Kwamishinan Gona Wa’adin Kwana 2 Ya Dawo Da Tirakta 58 Da Ya Sayar A Zamfara
- Mutane 8 Sun Mutu A Ruwa A Jihar Jigawa
Soludo ya bayyana cewa, soke yin kiwon a kan titunan jihar, na da daga cikin dokar jihar ta hana kiwo ta 2021, inda ya kara da cewa gwamnatinsa za ta tsaurara dokar a watan Satumbar 2022.
A cewarsa, duk da cewa an kafa dokar kusan shekara daya, amma har yanzu makiyaya a jihar na ci gaba da yin kiwo a wasu kan hanyoyin jihar, inda ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da tsaurara dokar ta hana yin kiwon a kan tituna a watan Satumba.
Ya yaba wa kwamtin bisa mayar da hankali kan yin ayyukan da aka dora musu na hana yin kiwon a kan titunnan jihar, inda ya kara da cewa, al’ummar jihar ta Anambra, sun kasance suna zaman lafiya da Fulani makiyaya da ke a jihar, amma dole ne makiyayan su dinga gudanar da kasuwancinsu kan yadda doka ta tanada.
A nasa jawabin jagoran kungiyar ta Miyetti Allah na shiyyar Gidado Siddiki, ya roki gwamnan da ya janye kudurinsa na wanzar da dokar a yanzu domin kungiyar ta samu damar ilimantar da ‘ya’yanta, kan yadda za su yi kiwonsu a jihar.
Ya ce “muna kira ga masu ruwa da tsaki da kafafen yada labarai da su roki gwamnan don ya janye kudurinsa na wanzar da dokar ta soke yin kiwo a jihar.”