Gwamnatin Tarayya ta ce Amurka ta amince za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarta wajen tsaron Nijeriya.
Wannan ya haɗa da ba da ƙarin bayanan leƙen asiri da kayan tsaro don taimaka wa yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin da ke haddasa rikici.
- Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Goyon Baya Ga Sake Bincikar Laifukan Da Japan Ta Tafka
- Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Wasanni 8 Da Ta Buga
Wannan mataki ya biyo bayan taruka da aka yi a Washington, DC, tsakanin manyan jami’an Nijeriya da hukumomin gwamnatin Amurka.
Tawagar Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu, ta haɗa da Babban Lauyan Ƙasa, hafsoshin tsaro, da Sufeto Janar na ’Yansanda.
A yayin tattaunawar, tawagar Nijeriya ta ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Sun ce rikicin da ke faruwa yana shafar al’ummomi daban-daban ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba, kuma kiran shi da kisan ƙare dangi ba daidai ba ne.
Ƙasashen biyu sun amince su fara aiwatar da sabuwar yarjejeniyar haɗin gwiwa nan take, tare da kafa kwamitin haɗin gwiwa domin tsara aikin tsaro tare.
Amurka kuma ta yi alƙawarin bayar da agajin jin-ƙai da taimako wajen inganta tsarin gano barazana tun wuri.
Gwamnatin Nijeriya ta ƙara tabbatar da ƙudirinta na kare fararen hula da kuma tabbatar da ’yancin addini.
Wannan tattaunawar na zuwa ne biyo bayan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya yi iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a Nijeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya musanta wannan zargi, yana mai cewa Nijeriya ƙasa ce da ake zaman lafiya da yarda da juna a tsakanin addinai.














