Wace ce abokiyar gaske ta nahiyar Afirka? Kasar Sin ce.
Taron kolin G20 da ya gudana a kasar Afrika ta Kudu a kwanan nan ya tabbatar da hakan.
To, ta yaya za a bambanta abokai na gaske, da wadanda ba su da gaskiya?
Da farko, duba ko za su mai da hankali kan moriyarka.
A lokacin taron kolin G20 na wannan karo, kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu sun gabatar da shawarar yin hadin gwiwa don zamanantar da nahiyar Afirka.
A cikin shawarar, an lura da bukatar kasashen Afirka ta zamanantarwa, kana an tsara wasu ka’idoji kan hadin gwiwar da ake yi don neman zamanantar da Afirka, wadanda suka hada da tabbatar da adalci, da amfanawa juna, da kula da moriyar jama’a, da kare mabambantan al’adu, da inganta muhallin halittu, gami da samar da tsaro.
Idan an yi hadin gwiwa a duniya, bisa wadannan ka’idoji, to, za a iya tabbatar da babbar moriyar kasashen Afirka.
A zahiri, sai wata abokiyar gaske ce za ta iya gabatar da wannan shawara.
Na biyu kuma, sai a kwatanta matakan da mabambantan bangarori suka dauka.
Daniel Makokera, wani shahararren marubuci dan kasar Afirka ta Kudu, ya rubuta wani bayani a shafin yanar gizo na allAfrica a kwanan nan, inda ya kwatanta matakan kasar Sin da na kasar Amurka, dangane da Afirka.
A cewarsa, kasar Sin tana zuba jari don raya tattalin arzikin Afirka, inda take gina layin dogo, da na’urorin samar da wutar lantarki, da tashoshin jiragen ruwa, da yankunan masana’antu, da samar da ilimin sana’a, da fasahohin zamani, gami da daukar matakan soke harajin kwastam, da kare lafiyar jikin manoma ‘yan Afirka, da dai sauransu.
Yayin da kasar Amurka, a nata bangare, manufarta ta kan zama shiri da magana kawai, inda maganar ta kan sauya tsakanin gargadi game da “tarkon bashi”, da suka kan yadda ake gudanar da mulki a kasashen Afirka.
Lokacin da kasar Afirka ta Kudu ta karbi bakuncin taron kolin G20 na wannan karo, kana daukacin nahiyar Afirka ke alfahari da lamarin, kasar Amurka ta ce wai ana wa fararen fata “kisan kare dangi” a kasar Afirka ta Kudu, don haka ta ki tura manyan jami’anta su halarci taron.
A cewar mista Makokera, Amurka tana yin biris da nahiyar Afirka da gangan, don bata son ganin yaduwar ra’ayin cudanyar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, da tasowar nahiyar Afirka.
Ko da yake kasar Sin tana kallon nahiyar Afirka a matsayin babbar abokiya mai muhimmanci, kasar Amurka na ci gaba da neman hana kasashen Afirka shiga cibiyar dandalin harkokin siyasa na duniya.
Mista Makokera ya kara da cewa, sakon kasar Sin ga kasashen Afirka shi ne, “ Za mu yi kokari tare don tabbatar da makoma mai haske, amma ba zan taba tilasta muku bin wata turbar raya tattalin arziki ba.” Wannan shi ne abin da ya kamata aboki mai gaskiya ya yi.
Abokantaka ta gaske dake tsakanin Afirka da Sin za ta haifar da wani sabon tsarin duniya, in ji Makokera.
A nan gaba, za mu kara fahimtar muhimmancin taron G20 na wannan karo, saboda ta ba da damar bambanta abokin gaske da wanda ba na gaske ba, da kuma nuna yanayin huldar dake tsakanin Afirka da Sin, da zai zama mai karin inganci a nan gaba. (Bello Wang)














