Rukunonin Kamfanin Dangote ya sanar da cewa, zai shiga Kasuwar Baje Koli ta kasa da kasa da za a gudanar a jihar Kano.
An tsara za a bude kasuwar baje kolin ne, daga ranar 22 na watan Nuwamba zuwa ranar 6 ga watan Disambar shekarar 2025, inda ake sa ran, sama kamfanonin a cikin kasar nan da kuma na waje 1000, za su baje kolin hajarsu.
- Tawagar Atiku Ta Isa Bauchi Don Halartar Jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi
- Buƙatar Daƙile Kutsen ‘Yan Bindiga Na Iyakokin Jihar Kano
Babban Shugaban Sashen Samar da Bayanai na Kamfanin Anthony Chiejina, ne ya sanar da hakan.
Anthony ya sanar da cewa, Kamfanin na Dangote ne, zai dauki nauyin gudanar da baje kolin tare da kuma shiga cikin baje kolin gadan-gadan.
Ya kara da cewa, ana sa ran sama da masu baje kolin daga cikin kasar da kuma ketare, za su baje hajarsu, a kasuwar.
“Jihar Kano, ta kasance tamkar cibiyar hada-hadar kasuwanci, ba wai a kawai a Nijeriya ba, har da ma a nahiyar Afirka,” in ji Anthony.
Ya ci gaba da cewa, kamfanin ya kuma kasance ya na da manyan kamfanonin da ke tsasar Shinka, a jihar ta Kano.
Kazalika, ya sanar da cewa, kamfanin na da kuma wasu kamfanonin tsadar Shinkafa da a jihohin Jigawa, Zamfara, Nijer, Kebbi, da kuma Sokoto, wanada ke da karfin tsasar Shinkfar da ta kai jimlra tan miliyan 1.5 a duk shekara.
Ya bayyana cewa, kamfanin yayi hakan ne, musamman bisa nufin tallafa wa kokarin gawamnati na samar da wadataccen abinci a kasar baki daya.
A cewarsa, kamfanin zai tabbatar da cewa, sauran sassansa sun taimaka wajen ganin an samu cin nasara, na gudanar da baje kolin a cikin nasara, tare da kuma bai wa masu yin kasuwancin kwarin guiwa wajen yin hadaka da kamfanin na Dangote.
Ya sanar da cewa, duba da matukar bukatar da ake da ita a kasuwani na Suga, kamfanin zai yin amfani da damar ta baje kolin wajen yin baje kolin sabon buhun samfarin Suga, mai nauyin daga kilo 100 da kuma kilo 25.
Ya sanar da cewa, taken baje kolin na bana, wanda shi ne, karfafa kwarin guiwar kanana da matsakaitan sana’oi, taken ya zo daidai da manufar kamfanin na Dangote, na tallafa wa kanana da matsakaitan sana’oi a kasar.
Ita kuwa, Babbar Mai Bai Wa Shugaban Rukunonin Kamfanin na Dangote Alhaji Aliko Dangote Shawar ta Musamman a bangaren Gudanar da Ayyuka da Dabaru da kuma Hulda da Jama’a Fatima Wali-Abdurrahman a cikin sanarwar da ta fitar ta ce, bisa daukar nauyin gudanar da baje kolin na bana, Kamfanin zai tabbatar da ya karfafa kwarin guiwar kanana da matsakaitan sana’oi, wanda hakan, zai basu damar baje hajar su, a lokacin baje kolin.
Shi kuwa Shugaban Cibiyar Kasuwar Baje Kolin Masana’antu da Ma’adanai da Aikin Noma KACCIMA Jakada Hassan Usman Darma, ya sanar da cewa, “ Muna sa ran kamfanonin kimanin 100 da kuma wasu masu baje kolin sama da 1,000, daga ciki da wajen kasar, za su baje hajaarsu, a kasuwar.”














