Rahotanni daga Pretoria sun tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun afka cikin wani ɗaki da ake amfani da shi a ɓoye a matsayin mashaya ba bisa ƙa’ida ba, inda suka kashe mutum 11 ciki har da yaro mai shekara uku.
Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar a unguwar Saulsville, wadda take yammacin Pretoria, kuma ya sake tayar ƙorafe-ƙorafe kan ƙara yawaitar harbe-harbe a Afrika ta Kudu, ƙasar da ke fama da yawan laifuka da kisan gilla. Ƴansanda sun ce mutum 25 aka harba gaba ɗaya, inda 14 daga cikinsu aka garzaya da su asibiti.
- Hakimi, Osimhen Da Salah Ƴan Wasan Da Ke Takara A Ƙyautar Gwarzon Afrika
- Sin Ta Yi Alkawarin Zurfafa Dangantaka Da Afrika Ta Kudu
Mai magana da yawun ƴansanda, Athlenda Mathe, ta bayyana cewa maharan su uku suka shiga cikin ginin da ƙarfe 4:30 na safe suka buɗe wuta kan mutanen da ke cikin mashayar giyar. Ta ce ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu ya rasu ne a asibiti, yayin da sauran goma suka mutu a wurin. Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai yara masu shekaru 12 da 16, abin da ya ƙara girgiza jama’a da hukumomi.
Mathe ta ce har yanzu ba a san musabbabin harin ba kuma babu wanda aka kama. Ta kara da cewa irin wannan harin yawanci na faruwa ne a wuraren shan barasa ba bisa ƙa’ida ba, inda ake taruwa ba tare da tsaro ba. Ta jaddada cewa irin waɗannan wurare suna janyo hatsaniya, har ma da faɗa . Ƴansanda sun ƙaddamar da bincike tare da farautar maharan da ake zargin suna da alaƙa da harkokin ɓata gari.














