ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro

by Ra'ayinmu
1 week ago
Arewa

A kwanan baya ne, Kungiyar Gwamonin Arewacin Kasar nan 19, tare da hadaka da Sarakunan Gargajiya na yankin, ta gudanar da taron gaggawa a jihar Kaduna, bisa nufin magance kalubalen rashin tsaro da ya yiwa yankin katutu, wanda a lokacin taron, suka yanke shawarar kafa wata katafariyar Gidauniya tara kudi, har Naira biliyan 19, domin tunkarar matsalar.

A bisa tsarin, duk wata, kowanne Gwamna, zai bayar da na sa kason na Naira biliyan daya daga cikin Asusun Gwamnatin sa

A Jimlace, Gwamnonin za su tara Naira biliyan 228 ne, a shekara, domin tunkarar matsalar ta matsalar tsaro, da ta mayar da yankin, tamkar fagen daga, musamman duba da yadda, matsalar kutsawa cikin makaratun kwana na dalibai, har ana safe su da ci gaba da sace manoma da ‘yan bindiga ke yi da kuma kara kazancewar ayyukan ‘yan ta’dda.

ADVERTISEMENT
  • Ta’addanci: Ko Matakan Shawo Kan Taɓarɓarewar Tsaro Za Su Yi Tasiri?
  • Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Nemi Tinubu Ya Dakatar Da Haƙar Ma’adinai Na Tsawon Watanni 6

A cikin sanarwar su ta bayan taron, kungiyar ta kuma mika jajenta, ga gwamnatocin jihohi bakwai, da aka sace dalibansu da kuma sauran alumominsu, da ‘yan bindiga, suka yi garkuwa da su

Mu a nan, ba wai muna yin batu, kan yanayin yawan samun akuwar matsslar ba ce, amma muna yin dubi ne, kan gazawar gwamonin, na magance matsalar.

LABARAI MASU NASABA

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

A nan za mu iya cewa, wannan zunzurutun kudaden da za su tara har Naira biliyan 19 a wata daya, ya zama wajibi alummar yankin su sauya, na dakile matsalar domin kuwa, ‘yan Nijeriya, sun gaji batun ana tara dimbin kudade, domin magance wata matsala a kasar, amma daga, a karkatar da su, zuwa wata sabga, ta da ban.

Kazalika, batun ba wai kawai na tara wadannan zunzurutun kudaden ba ne, amma babbar ahaure’yan ambayar a nan ita ce, shin wa zai tafiyar da wadanda kudaden ? kuma shin, takamai-mai, wacce daga cikin matsalar ta tsaron, za a tunkarar? ta yaya za a kashe kudaden tare da fayyace yadda aka kashe su?

Matukar gwamonin, ba su bayar da wata gamsasshiyar amsar wadannan tamaboyin ba, wannan Gidauniyar, za ta kasance a cikin shakku, wadda za ta kasance wata hanya ta arzurta ‘yan Kwangila da kuma wasu da za a dauko, a matsayin mutanen tuntba, inda su kuma alumomin da ya kamata, magance masu kalubalen, za su ci gaba kai Gawarwakin ‘yanuwansu, makabartu, suna bizne su, saboda ci gaba da hare-haren na ‘yan bindiga.

Bugu da kari, Gwamonin sun bukaci da a dakatar da hakar ma’adanai, har na tsawon watanni shida, duba da cewa, hakar na’adanan, ta haramtacciyar hanyar, ta kasance tamkar wata hanya, samun kudaden ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

Alumomin da ke a jihohin Zamfara, Kaduna da Neja, sun ci gaba da fuskantar ‘yan bindiga da kuma’yan ta’adda bakin haure, ke kutsawa cikin alumomin da ke a wadannan jihohin suna hana su, kwanciyar hankali, tare da gindaya masu haraji.

A yanzu, Gwamonin na son ganin an tsaftace fannin na hakar ma’adanai ta hayar bayar da lasisi.

A nan, za a iya cewa, dakatawar ta watanni shida, ba ta wadatar ba, domin har yanzu, wasu na ci gaba da gudanar da ayyukan, ta haramtacciyar hanya.

A saboda haka, ya zama wajibi Gwamonin, su bukaci Ma’aikatar Hakar Ma’adanai ta Tarayya da ta sanar da su, ainahin kamfanonin da suka mallaki lasisin hakar ma’adanai tare da kuma wadanda suke amfana da fannin.

Hakazalika, akwai bukatar jihohin su samu cikakkun bayanan sirri, kan ayyukan da a ke gudanarwa, ba hakar ma’adanai a jihohin su da alumomin da abin ya shafa, inda kuma alummar, na ‘yancin su fada ko har yanzu, ana ci gaba da gudanar da ayyukan a yankunan su.

Kazalika, gungiyay ta kuma goyi bayan kafa ‘yansanda na jihohi, inda shi kasansa, wannan batun ke da bukatar, a yi dogon nazari a kai.

A bisa tunaninsu, kirkiro da ‘yansandan na jihohi, ita ce, hanya daya tilo, za a iya magance kalubalen rashin tsaro

Abu daya da takardar sakamakon taron ba su ta tsalle shi ne, shin a ta yaya ne, yankin ya tsinci kasansa, a cikin wannan matsalar ta rashin tsaro.

Gwamonin su kuma mika ta’aziyyarsu ga shugaba Bola Tinubu da kuma kokarin da yake ci gaba da yi, na tabbatar da tsaro, amma sun gaza yin dubi ga batun cin hanci da rashawa da yin tunani kan yadda ‘yan bindiga da kuma’yan ta’adda, ke ci gaba da aikata ta’asarsu, a cikin alumomi ba.

A nan za mu iya cwa, batun ya fi karfin tara kudade da damar da kayan aiki, amma dole ne, Gwamnonin su fuskanci gaskiya, musamman kan gazawar iya shugabanci wadda ta bayar da damar samun matsalar ta rashin tsaro.

Ya zama wajibi, Gwamnonin su yi dubi kan yadda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ke watayawarsu a cikin alumma tare da kakkafa sansanoninsu su kuma kai hare-harensu, ba tare da a far masu ba.

Batun na tara Naira biliyan 228 a shekara, batu ne da ya wuce maganar fitar da sanarwa ga kafafen yada labarai, amma sakamko na gari, shi ne ake bukata.

Shin dalibai a jihar Zamfara, za su iya zuwa makarantunsu na Boko, ba tare da jin wani tsoro ba? Manoma a jihar Kaduna, za su iya zuwa su iya komawa ci gaba da noma gonaksnu ba tare da wata fargaba ba? Matafiya za su iya bin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ba tare da ‘yan bindiga sun kai masu hari ba?

Gwamnonin sun dauki matakai da dabaru na zuba kudade domin tunkarar kalubalen na rashin tsaro.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Next Post
Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su

Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.