Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya kafa harsashin ginin masana’antar sarrafa Rogo domin samar da isashen garin kwaki da ake kawowa daga kudancin Nijeriya.
Manufar Kafa kamfani shi ne saukakawa al’umma wahalar da suke sha wajen sayen garin kwaki duk da cewa su ke noma rogo amma sarrafa shi ne yake yi masu wahala.
- Masu Kiwon Kaji Da Manoman Rogo 700 Sun Samu Horo A Jihar Edo
- Nijeriya Za Ta Rika Samun Naira Tiriliyan Uku A Aikin Tatsar Rogo Duk Shekara – Kashim
Haka kuma Gwamna Radda ya lura cewa masu noman Rogo a yankin Batsari suna shanya shi ne a kan tituna wanda haka yake da hadarin gaske musamman yara da kuma tsofaffi
Da yake jawabi a wajen kafa harsashin wannan kamfani na sarrafa Rogo a karamar hukumar Batsari Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya ce haka zai tallafa wa masu kananan sana’o’i wajen bunkasa tattalin arzikin su.
A cewar sa, lokacin yakin neman zabe ya lura da cewa karamar hukumar Batsari na daga cikin wuraren da ake noman Rogo so sai wanda al’ummomi ke samar da rogo mai yawan gaske.
Ya kara da cewa mutanen Batsari sun dade da wannan sana’a ta noman Rogo tun Iyaye da kakanni, wanda ya ce haka ta sanya ya baiwa hukumar bunkasa kanana da matsakaitun sana’o’i umarnin kafa masana’anta ta sarrafa Rogo a Batsari
“Abin da muke gani shi ne, samar da wannan masana’anta zai kawo bunkasar tattalin arziki sannan ya rage asarar da manoma ke yi wajen samar da abinci sannan zai samar da ayyukan yi ga matasa tare da karfafa al’umma su kara shiga harkar noman Rogo” inji shi














