A kwanakin baya, dusar kankara ta sauka a birnin Beijing a karon farko tun bayan da aka shiga lokacin hunturu na bana. Dusar kankara ta kara kawata birnin, sai dai ta haifar da matsala ga zirga-zirgar mazauna birnin. A baya, bayan saukar dusar kankara, a kan yi amfani da sinadaran narkar da kankara wajen kawar da kankarar da ta mamaye hanyoyi. Amma a wannan shekara, an fara kayyade yin amfani da sinadaran narkar da kankara a birnin Beijing, kuma a maimakon hakan, mahukuntan birnin sun kara tura ma’aikata da motocin kawar da kankara da sauran na’urori don gudanar da aikin.
Dalilin da ya sa aka kayyade yin amfani da sinadaran narkar da kankara a birnin Beijing shi ne, don neman rage illolin da hakan ka iya haifarwa muhalli. An ce, sinadaran narkar da kankara su kan kunshi potassium chloride, da sodium chloride, wadanda in sun hadu da kankara, suna iya rage sanyin digirin daskararren ruwa har zuwa kasa da sifiri, ta yadda kankara za ta narke nan da nan zuwa ruwa. Amma a sa’i daya, sinadaran na iya haifar da illoli ga hanyoyi da muhalli, har da lafiyar jikin dan Adam. Misali, in ruwan da ke kunshe da sinadaran ya shiga cikin kasa, zai iya gurbata ruwan da ke karkashin kasa, wanda hakan ke haifar da barazana ga ingancin ruwan sha da ma muhallin rayuwar dabbobi da tsirrai.
Yadda aka kayyade yin amfani da sinadaran narkar da kankara, ya shaida yadda manufar kiyaye muhalli ke zame wa al’ummar kasar Sin jini da tsoka. A hakika, in mun lura, karin motoci masu amfani da makamashi mai tsabta na kara fitowa a titunan kasar Sin cikin ‘yan shekarun baya, kuma dazuzzukan da aka dasa sun kara yawaita, ga kuma iska da ruwan koguna na kara tsabta. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta gaggauta raya nau’o’in makamashi masu tsabta, har ma ta kai ga kafa tsarin samar da makamashi masu tsabta mafi girma a duniya, kuma yawan wutar lantarki da ta iya samarwa ta amfani da makamashi masu tsabta ya karu da kimanin kaso 60%. Baya ga haka, yawan ranakun da ake samun iska mai inganci a biranen kasar cikin shekara ya kiyaye matsayin kaso 87%, kuma fadin dazuzzukan kasar ma ya karu da kaso 2%, lamarin da ya sa kasar Sin ta zama kasar da ta fi saurin karuwar dazuzzuka a fadin duniya.
A hakika, tabbatar da ci gaban kasa ba tare da gurbata muhalli ba, manufa ce da kasar Sin ke tsayawa tsayin daka a kai. Idan ba a manta ba, cikakken zama na hudu na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20 da aka gudanar a watan Oktoban bana, ya bukaci a gaggauta sauya salon bunkasuwar tattalin arziki, da zaman al’umma ya zama irin na kiyaye muhalli, tare da gina kyakkyawar kasar Sin. Sai kuma a kwanakin baya, mahukuntan kasar Sin sun kira babban taro na tattauna aikin raya tattalin arzikin kasar, inda aka sanya “burikan kaiwa kololuwar fitar da hayakin carbon da kawar da tasirinsa, da kuma kara azamar ingiza sauya akala zuwa ci gaba ba tare da gurbata yanayi ba” a matsayin wani muhimmin aikin da za a gudanar wajen raya tattalin arziki a shekara mai zuwa.
Burikan da aka gabatar sun shaida niyyar kasar Sin ta tabbatar da bunkasa ba tare da gurbata muhalli ba. A yayin da ake fuskantar matsalar karancin makamashi, da kuma kalubalen sauyin yanayi a fadin duniya, manufar kasar Sin ta tabbatar da bunkasa ba tare da gurbata muhalli ba tana da muhimmiyar ma’ana ga duniya. Sabo da na farko, kasancewar kasar Sin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, tabbatar da bunkasuwarta ba tare da gurbata muhalli ba zai yi matukar taimakawa wajen rage fitar da hayakin Carbon mai dumama yanayi. Na biyu, kasar Sin tana da fifiko wajen masana’antun samar da wutar lantarki ta makamashin rana, da karfin iska, da kuma motoci masu amfani da lantarki, wadanda kuma ke samar da alfanu ga karin kasashe ta hadin gwiwarsu da kasar Sin bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”. Na uku kuma, kirkire-kirkiren da kasar Sin ta yi wajen bunkasa tattalin arziki mai alaka da kiyaye muhalli sun samar da misali ga aikin kiyaye muhalli a duniya.
A cikin ‘yan shekarun baya, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta fannin kiyaye muhalli ya janyo hankalin duniya sosai. Kasar Sin ta aiwatar da daruruwan ayyuka masu alaka da tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a Afirka, kuma ta hanyar musayar fasahohi da shirye-shirye da kuma samar da tallafin kudi, kasar Sin ta yi ta inganta hadin gwiwarta da kasashen Afirka ta fannin samar da makamashi masu tsabta. Kamar yadda Brains Muchemwa, masanin ilmin tattalin arzikin kasar Zimbabwe ya ce, kasashen Afirka sun amfana sosai da masana’antun samar da makamashi masu tsabta da ke saurin bunkasa a kasar Sin.
A yayin da take kokarin zamanantar da kanta, kasar Sin tana son raba fasahohinta masu alaka da samun ci gaban kasa ba tare da gurbata muhalli ba, haka kuma tana son aiwatar da wasu ayyuka bisa hadin gwiwa da kasashen Afirka, a kokarin samun ci gaban tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da tabbatar da zamanantarwa gami da kyakkyawan muhalli a lokaci guda.














