Shugaban karamar hukumar Warri ta kudu kwamarde Agbateyiniro Isaac, ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu, bisa umartar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA na ta mayar da ofishin gudanar da ayyukan na hukumar zuwa yankin na Warri.
Agbateyiniro ya bayyana wannan matakin a matsayin abin kara karfafa kwarin guwai musamman ga yankin.
- Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Farfesa Ibrahim Tsafe A Matsayin Sabon Shugaban Jami’ar ZAMSUT
- Bunkasar Masana’antun Kasar Sin Ya Kai Kaso 6.0% a Watanni 11 Na Farkon Shekarar Bana
Kazalika, shugaban ya kuma godewa Gwamnan jihar Delta Sheriff Oborebwori, kan namijin kokari da ya yi, domin gknin an mayar da ofishin gudanar da ayyukan na hukumar zuwa yankin na Warri.
Shugaba Agbateyiniro, wanda ya bayyana jin dadinsa kan mayar da ofishin gudanar da ayyukan na hukumar zuwa yankin na Warri ya sanar da cewa, wannan ci gaban da aka samu bisa kokarin da ake ci gaba da yi, a tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma jihar ta Delta musamman domin a kara habaka tattalin arziki a tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma ta jihar Delta.
Agbateyiniro, wanda ya yi wannan yabon a cikin sanarwar da ya fitar a garin Warri, ya kuma bayar da tabbacin cewaa karkashin shugabancin sa, a shirye ya ke, ya samar da kyakyawan yanayi ga mahukuntan hukumar ta NPA, domin ganin a cika wannan umarnin na shugaban kasa, ba tare da bata wani lokaci ba.
Shugaban ya kuma yi kira ga nasu hada-hadar sufurin manyan motoci da ke gudanar da ayyukan su a yankin da sauran masu ruwa da tsaki da su yi amfani da wannan dsmar ta umarnin shugaban kasa.
“Wannan umarnin na shugaban kasa. tamkar bude wata kofa ce, da za ta kara taimaka wa, wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin karamar hukumar ta Warri, da kuma sauran sassan jihar ta Delta, Inji Agbateyiniro.
Kazalika, ya bayyana cewa, wannan damar, za ta kuma taimaka wajen samar da ayyukan yi ga alummar da ke a karamar hukumar ta Warri ta kudu wadda kuma za ta sanya, alummar jihar ta Delta, su kara amfana da tsare-tsaren da Gwamnan jihar Oborebwori ya kirkiro da su wanda hakan zai bai wa, ‘yan jihar, shiga cikin harkokin kasuwanci tare da kuma fitar da kayan da ake sarrawa a cikin jihar zuwa ketare.
Shugaban ya bayyana cewa, wannan umarnin, ya kuma kasance, tamkar samar da romon dimakariciyya ne, a karkashin shugabancin gwamnatin jami’iyyar APC.
“Ya zamar min dole in godewa gwamnan jihar Delta wanda kuma ya kasance Ubangi da na, a bangaren siyasamusamman saboda kammala ayyukan Gadojin Warri zuwa Ode da kuma ta zuwa Itsekiri da kuma aikin gyran hanya, da kudinsu ya kai na biliyoyin Naira, kammala wadannan ayyukan tabbas hakan ya nuna cewa, gwamnan mutum ne, mai cika alkarinsa,” A cewar shugaban.














