’Yan Majalisar Ɗokoki ta Ƙasa sun roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba umarninsa na janye ’yansandan da ke kare manyan jami’ai, ciki har da ’yan majalisa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya bayyana hakan a zaman haɗin gwiwa na majalisar da aka yi domin karɓar kasafin kuɗin shekarar 2026.
- Shekara Biyar Da Rasuwar Sam Nda-Isaiah
- Marigayi Shugaba Buhari Ya Yi Zargin Na Yi Shirin Kashe Shi —Aisha Buhari
Ya ce ’yan majalisa na fargabar tsaronsu, musamman lokacin da za su koma mazaɓunsu ba tare da rakiyar ’yansanda ba.
ADVERTISEMENT
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin janye ’yansandan ne domin ƙara yawan jami’an tsaro da za a tura wuraren da ke fama da matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.














