Samun mijin da zai kalli iyayenki a matsayin nasa iyayen, wanda zai mutunta ‘yan uwanki kamar nasa ‘yan uwan.
Samun mijin da idan ba ki da lafiya, zai ji tamkar shi ne ba shi da lafiya wurin kulawa da ke da sadaukarwa. Samun namiji mai hakuri wanda zai dauke ki a matsayin da Allah ya yi ki na rauninki da ajizancinki na mace.
- An Bukaci Amurka Da Ta Kauracewa Sanya Wasu Sassa Na Muzgunawa Kasar Sin Cikin Kudurin Dokar Tsaron Kasa
- Hidimar Kwastam Mai Zaman Kanta Da Sin Ta Kafa Ta Samar Da Sabbin Damammaki Ga Masu Zuba Jari Na Waje
Samun namijin da yake jin ke dolensa ne, dole ne a kansa ya rike ki amana, ya kula da ke da dukkan karfinsa da ikonsa. Samun mijin da zai kula miki da mutuncinki a kan harshensa da ayyukansa. Namijin da sauyin jiki ko tsufa ba ya sa ya guje ki ko ya tozarta ki.
Namijin da ba ballagazi ba. Namiji mai sauraron damuwarki da kawar miki da ita iya yinsa. Namiji mai tsafta da gyara, da jawo ki a jiki, hira da ke, da wasa da raha da ke.
Namijin da yake da yafiya da yi miki uziri a lokacin hakan, da yi miki murmushi, da uzuri, da nuna soyayya. Namijin da ya yarda komai ya same ki, shi ya sama, mai dadi ko mara dadi. Namiji mai son ci gaban ki da taya ki cika mafarkanki masu kyau na alkhairi.
Namiji mai tausayi wanda za ki same shi a sanda kike bukatar tausayin sa da taimakon sa. Namijin da yake kaunarki, kike kaunarsa domin Allah da son zama tare da juna.
Samun irin wannan namiji ga mace ya fi auren gidan daular da ba za ta samu wannan ba, sai dai kudi.
Allah ya hada kawunan ma’aurata ameen.














